Tarihin Magabata

Call Directions Website Contact the organization

Tarihin Magabata An ƙirkiri wannan shafi na Arewa Tarihi domin kawo maku tarihin magabata na ciki da wajen Nijeriya, domin ilmantarwa, nishaɗantarwa, dakuma faɗakarwa.

A cikin wani hoto da aka ɗauka a shekarar 1968 lokacin Yaƙin Basasar Najeriya, ana ganin Laftanar-Kolonel Ayo Ariyo da K...
23/04/2026

A cikin wani hoto da aka ɗauka a shekarar 1968 lokacin Yaƙin Basasar Najeriya, ana ganin Laftanar-Kolonel Ayo Ariyo da Kolonel Olusegun Obasanjo suna cin abinci tare a filin daga (frontline).

A lokacin, Obasanjo ya karɓi jagorancin rundunar 3rd Marine Commando daga shahararren Kolonel Benjamin Adekunle wanda ake wa laƙabi da “Black Scorpion”, kuma yana zagayawa sassan rundunar da ke ƙarƙashin sabon shugabancinsa.

15/04/2026

Tuna baya...

Yayin da Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa ke jawabi kan bayar da magani kyauta ga mata masu goyo da yaran da basu wuce shekara 18 ba.

Allahu ya kyautata makwancinsa. Ameen ya Hayyu ya Qayyum.

12/04/2026

Tuna baya:

Lokacin da tsohon shugaban kasar Pakistan Zulfikar, ya yaga takardar dake dauke da kudirin cewar Pakistan bazata mallaki makamin nuclear ba, a zauren majalisar dinkin duniya.

Yau saidai tarihi Pakistan ta mallaki nuclear ta huta da barazanar is'ra'ela da kawayen ta.

Zaman sulhun da akeyi a Pakistan alamu suna nuna cewa sabuwar yaudara ce Amurka ta sake shiryawa, domin dakarun juyin ju...
11/04/2026

Zaman sulhun da akeyi a Pakistan alamu suna nuna cewa sabuwar yaudara ce Amurka ta sake shiryawa, domin dakarun juyin juya hali na Iran sun hango jiragen ruwan yaki na Amurka sun taso daga tashar ruwan Fujairah dake Daular Larabawa sun nufi mashigar ruwan Hormuz.

Nan take dakarun Iran s**a sanar da wakilan Iran dake tattaunawa akan su sanar da Pakistan domin zasu tarwatsa su idan s**a matso kusa da mashigar ruwan.

Yadda Babangida Su Kayi Da Dimka Sunan Janar Ibrahim Babangida ya fara fitowa a duniya, tun a ranar 13 Ga Fabrairu, 1976...
13/02/2026

Yadda Babangida Su Kayi Da Dimka

Sunan Janar Ibrahim Babangida ya fara fitowa a duniya, tun a ranar 13 Ga Fabrairu, 1976, ranar da abokin sa Kanar Bukar S**a Dimka ya kashe Shugaban Kasa na mulkin soja a lokacin, Janar Murtala Ramat Muhammad wajen karfe 8:30 na safiyar ranar.

Bayan da Dimka ya kashe Murtala, sai ya zarce gidan rediyon tarayya da ke Lagos, in da ya fara yin sanarwa. Sai dai kuma ya na cikin yi wa ‘yan Najeriya jawabin ne, sai Janar dan Danjuma ya umarci Babangida yaje gidan Radiyo ya kamo Dimka ko ta halin ka'ka. Babangida ya darkaki gidan radiyon ya na mai jagorantar rundunar sojoji da motocin sulke da aka tura don ta murkushe Dimka.

IBB ya shiga gidan Rediyon ne domin ya shawo kan Dimka da ya yi watsi da yunkurinsa na kwace mulki. Maimakon IBB ya yi amfani da Karfi sojoji k**ar yadda aka bashi umarni sai ya zabi hanyar lallashi.

Juyin mulkin ya ci tura," k**ar yadda ya shaida wa Dimka. "Dole ka mika wuya." Sai Dimka ya yi barazanar zai harbe shi, sai IBB yayi murmushi ya shaida wa Dimka kashe ni, in ka kashe ni nasan matata da ‘ya’yana ba za su sha wahala a karkashin kulawar ka ba. Sai Dimka zuciyarsa ta karaya kuma ya nemi a yi masa afuwa idan an kafa sabuwar gwamnati, in da yake cewa Babangida, zai taka muhimmiyar rawa.

IBB ya fita da nufin zuwa neman izinin tattauna batun neman Sulhu daga Dimka. IBB ya koma wurin Danjuma wanda ya fusata da wannan bukata da ya kawo. Danjuma Ya dakawa IBB tsawa da cewa, “Ban nemi kaje don sulhu ba! a lokacin da IBB ya dawo gidan rediyon Najeriya cikin Sauri Kafin ya Karasa Dimka ya tsere.

Daga baya an k**a Dimka da Taimakon wata karuwa a gabashin Najeriya a lokacin da yake kokarin tserewa zuwa Kamaru. A ranar 15 ga watan Mayu 1976, aka Harbe shi a bainar jama'a saboda laifin cin amanar kasa.

✍️ Muhammad Cisse

20/01/2026
20/01/2026

Wannan bidiyon yana tona asirin yadda Patrice Emery Lumumba, Firayim Ministan Congo na farko, ya zama barazana ga ƙasashen waje, da kuma yadda ƙasarsa kanta ta juya masa baya.
Ballewar yankuna, juyin mulki, cin amana, tsoma bakin ƙasashen waje duk sun haɗu s**a mayar da filin samun yanci ya koma filin yaƙi da Mubarak da jini.

Yau shekaru 60 da rasuwar Tafawa Ɓalewa da Ahmadu Bello SardaunaA rana irin ta yau a 1966 ne aka kashe Firaiministan Naj...
15/01/2026

Yau shekaru 60 da rasuwar Tafawa Ɓalewa da Ahmadu Bello Sardauna

A rana irin ta yau a 1966 ne aka kashe Firaiministan Najeriya na farko, Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello da wasu jiga-jigan ƴansiyasa da sojoji a yunƙurin sojoji na juyin mulki.

Tarihin Magabata

Inyamuri Chukwuma Nzeugwu shine wanda ya halaka Ahmadu Sardauna a rana irin ta yau 15 ga watan Janairu 1966...Sardauna y...
15/01/2026

Inyamuri Chukwuma Nzeugwu shine wanda ya halaka Ahmadu Sardauna a rana irin ta yau 15 ga watan Janairu 1966...

Sardauna ya amince da Chukwuma ya bashi amana, amma hakan bai hanashi cin amana ya halaka Sardauna ba...

Tarihin Magabata

04/01/2026

Yau Shekaru 42 Da Kashe Birgediya Muhammad Bako. An Aikeshi Ya Kamo Shugaban Kasa Shehu Aliyu Usman Shagari A Yunkurin Ya Rasa Ransa.

Brigadier Ibrahim Bako Ya Mutu A Juyin Mulki Na Disamba 1983.

Soja Daya Tak Daya Rasa Ransa A Rana Mai Kamar Ta Yau 31 Disamba 1983 A Lokacin Juyin Mulkin Soja A Najeriya.

Birgediya Ibrahim Bako ya kasance babban jami'i a cikin sojojin Najeriya da s**a taka babbar rawa a juyin Mulkin sojoji guda 2 da akayi a Najeriya, da juyin mulkin da akayi a ranar 29 ga watan Yuli 1966 (counter), da kuma juyin mulkin ranar 31 ga watan Disamba 1983, juyin mulkin 1983 ya hambarar da gwamnatin dimokaradiyya ta Shehu Shagari.

An kashe Bako ne a lokacin da yake yunkurin k**a shugaban kasa Shehu Shagari a juyin mulkin.

Birgediya Ibrahim Bako (A lokacin daraktan tsangayar soji a kwamanda na rundunar soji da kwalejin ma’aikata, Jaji) kuma mukaddashin GOC 1 Mechanized Division, Kaduna.

Sojojin da s**a shirya juyin mulkin sun tura Birgediya Ibrahim yaje ya kamo shugaban kasa Shehu Shagari salin-alin ba tare da zubar da jini ba, domin kasancewar mahaifin Ibrahim Bako amini ne ga Shugaban Kasa Alhaji Shehu Aliyu Usman Shagari, ana fatan wannan alaƙar za ta tabbatar da mika mulki cikin lumana.

Bako dai bai san cewa an fallasa shirin juyin mulkin ga shugaba Shagari ba! wanda yasa masu gadin sa na cikin shirin kota kwana.

Bayan ya isa gidan shugaban kasa (a cikin kayan da ba na soja ba), kuma ba tare da tawagarsa na dauke da wasu isassun mak**ai domin k**a shugaban ba. An harbe Bako ne a lokacin da yake zaune a gefen fasinja na wata babbar mota kirar Unimog a wata arangama da aka yi tsakanin sojojin da ke tare da Bako da kuma sojojin Brigade of Guards a karkashin jagorancin Captain Augustine Anyogo.

Motar Unimog da aka kashe Bako a ciki ta na gidan baje kolin kayan tarihi na sojojin Najeriya da ke Zariya Najeriya.

Bako ne kawai wanda ya mutu a juyin mulkin 1983. Majalisar Koli ta Soja (SMC) ta yi shiru na minti ɗaya a lokacin taronta na farko a ranar 3 ga Janairu, 1984.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tarihin Magabata posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Tarihin Magabata:

Shortcuts

Share

Category