26/07/2020
BACK TO SENDER !!!
INA AL'UMMAR KOKO/BESSE DA MAIYAMA📢
To ku sheko ku shigo ga jirgin Alkhairi✈wato Alh Shehu muhammad koko (WAMBAN KOKO)👍Bari harma kuji kadan daga cikin ayukan Alkhairin dayakeyi.
1.TALLAFAWA HARKAR ILIMI:A kokari da yakeyi don ganin yaranmu sun samu ilimi ingan tacce, sun hada da Gina ajujuwan karatu, da bayarda littaffan karatu da rubutu kyauta, hadi da dunkawa yara tufafin makaranta da bayarda kyaututtuka ga yara masu hazaka, da kuma daukar nauyin yara matasa zuwa makarantun gaba da firamari harma sakandari.
2.WUTAR LANTARKI:A kokari da yake yi don inganta rayuwar Al'umma, da taimakawa yan kasuwa masu amfani da wutar lantarki kamar:Teloli, masu Walda, Masu Aski, Masu kayan sanyi dadai sauran Al'umma baki daya.Maigirma koko yayi kokari wajan samo muna taransafomomi guda hudu 4 masu karfin wuta 5000 a garin koko.
3.NOMA.Mai girma koko ya tanadi Takin zamani hadi da magungunnan feshi don rabawa ga manoma kyauta domin inganta harkar noma da kawar da yunwa da fatara.
4.A kokarin da yakeyi na tallafawa Manya da kananan yan kasuwa, mai girma koko nanan yana chigaba da tallafawa yankasuwa da kudade hadi da jingina su ga manya-manya yan kasuwa domi farfado da tattalin arziki da kawarda talauchi da bu kasa yankin koko/besse da maiyama.
5.SAMARWA MATASA AIKIN YI DA MORE RAYUWA:Mai girma koko yayi alkawali gina gidan na tashar F.M kuma mai dogo zango, tare da gina kamfanin fenti, da Alli (chalk) da kuma gina makarantu Nursery, primary da secondry a yankin koko/besse da maiyama domin rage zaman kashe wando da hana matasa shiga bangar siyasa.
6.TAIMAKAWA ADDINI:A kokarin sa da yakeyi kuma ya saba na tallafawa addin, mai girma koko ya tallafawa marayu sama da Dari 100 da kudade da abinchi da kuma daukar nauyi karatunsu.
Mai girma wamban koko bai tsaya nan ba yana kokari wajan gina makarantu allo da islamiyyoyi da taimakawa Almajirai, gyaran masallatai da bayarda Injimukka(Generators)ga masallatai da makaran tu.
7.KULA DA HARK