Bala Wunti Support Organisation - Katagum LGA

Bala Wunti Support Organisation - Katagum LGA The time for delay is over, and the people are ready to rise.

Through trust, respect, integrity, inclusivity, and collaboration; Bauchi will become a state where every person can rise, grow, and thrive.

BWSO Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa da Ƙungiyar Makera Tukwane a KatagumBala Wunti Support Organisation (BWSO) ta kai ziyara ga ...
27/06/2026

BWSO Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa da Ƙungiyar Makera Tukwane a Katagum

Bala Wunti Support Organisation (BWSO) ta kai ziyara ga Ƙungiyar Makera Tukwane a Ƙaramar Hukumar Katagum domin ƙarfafa alaƙa da masu sana’o’in gargajiya da kuma tattauna hanyoyin bunƙasa sana’ar tukwane. Haka kuma, ziyarar ta mayar da hankali kan samar da ayyukan yi da ƙarin damar tattalin arziki ga matasa.

Kodinetan BWSO na Katagum, Ahmad Musa, ya yaba da ƙoƙarin masu sana’ar tukwane wajen raya sana’ar gargajiya da gudummawar da suke bayarwa ga tattalin arzikin al’umma. Ya jaddada cewa BWSO za ta ci gaba da haɗa kai da ƙungiyoyi daban-daban domin tallafa wa sana’o’i da ƙarfafa dogaro da kai.

Shugaban Ƙungiyar Makera Tukwane ta Katagum, Salihu Abubakar, ya gode wa BWSO bisa ziyarar tare da bayyana cewa hakan zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin biyu. Ya ce suna shirye su yi aiki tare domin bunƙasa sana’ar tukwane da samar da ƙarin damammakin tattalin arziki ga matasa da mata, a wani ɓangare na ƙoƙarin kawo ci gaba mai ɗorewa a Katagum.

Ahmad Musa
BWSO Coordinator
Katagum local govt chapter.

Yi Rajista da BWSO Katagum domin ka kasance cikinmu👇BWSO Katagum na gayyatar ɗaukacin matasa, mata da maza masu kishin c...
25/06/2026

Yi Rajista da BWSO Katagum domin ka kasance cikinmu👇

BWSO Katagum na gayyatar ɗaukacin matasa, mata da maza masu kishin ci gaban Ƙaramar Hukumar Katagum da su shiga wannan tafiya ta alheri da cigaba.

✅ Yi rajista
✅ Kasance cikin masu kawo ci gaba
✅ Ka ba da gudummawa wajen gina makomar Katagum
✅ Kasance cikin masu amfana da shirye-shiryen wannan gidauniya

Yi rajista yanzu ta wannan shafi:
🌐 https://www.thebwsoportal.org

Domin ƙarin bayani:
📞 08061577578
📞 08067677751

Ahmad Musa
BWSO Coordinator,
Ƙaramar Hukumar Katagum.

BWSO Katagum Ta Gana da Bull & Truck Construction CompanyBala Wunti Support Organisation (BWSO) reshen Karamar Hukumar K...
23/06/2026

BWSO Katagum Ta Gana da Bull & Truck Construction Company

Bala Wunti Support Organisation (BWSO) reshen Karamar Hukumar Katagum ta ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma ziyartar masu aikin hannu da sauran al’umma, inda ta kai ziyara ta musamman ga Bull & Truck Construction Company da ke Kafin Kuka, Gadau Road, Azare.

A yayin ganawar, Ahmad Musa, Coordinator na BWSO a Karamar Hukumar Katagum, ya gabatar da manufofi da ayyukan BWSO, tare da bayyana kudurinta na karfafawa matasa, bunkasa shugabanci, inganta ilimi, hidimtawa al’umma da kuma samar da ci gaba mai dorewa. Ya bayyana cewa ziyarar na daga cikin kokarin BWSO na gina kyakkyawar alaka da cibiyoyi da kungiyoyin da ke bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma.

Coordinator ya kuma gabatar da bayanai kan taron Ranar Kwarewar Matasa ta Duniya 2026 (World Youth Skills Day 2026 Conference) mai taken “Skills for the Shared Future”, inda ya jaddada muhimmancin koyon sana’o’i da kwarewa, kirkire-kirkire, kasuwanci da dogaro da kai ga matasa. Ya tabbatar wa kamfanin cewa za a ba su guraben halartar taron tare da karfafa hadin gwiwa a shirye-shiryen da ke tallafawa bunkasar matasa da ci gaban al’umma.

Bugu da kari, ya yi bayani kan shirin rajistar kungiyoyin kawance 'affiliate group' na BWSO, yana mai bayyana cewa shirin zai taimaka wajen kara dankon hadin gwiwa tsakanin BWSO da kungiyoyin al’umma, kungiyoyin kwararru da sauran cibiyoyi.

Da suke mayar da martani a madadin kamfanin, mahukuntan Bull & Truck Construction Company sun yi maraba da tawagar BWSO tare da nuna godiyarsu bisa wannan ziyara. Sun gode wa kungiyar bisa wannan karamci na tuntuba da hadin gwiwa, tare da yaba wa kokarinta wajen karfafawa matasa, bunkasa al’umma da kuma hada masu ruwa da tsaki cikin harkokin ci gaba.

Ahmad Musa
BWSO Coordinator
Katagum local govt chapter

19/06/2026

BWSO Katagum Ta Gana da Kungiyar Masu Gyaran Motoci ta Kasa (NATA) Reshen Karamar Hukumar Katagum.

BWSO Katagum Ta Gana da Kungiyar Masu Gyaran Motoci ta Kasa (NATA) Reshen Karamar Hukumar KatagumA ci gaba da ziyarce-zi...
19/06/2026

BWSO Katagum Ta Gana da Kungiyar Masu Gyaran Motoci ta Kasa (NATA) Reshen Karamar Hukumar Katagum

A ci gaba da ziyarce-ziyarcen al’umma da masu ruwa da tsaki, Bala Wunti Support Organisation (BWSO) reshen Karamar Hukumar Katagum ta kai ziyarar girmamawa ga Kungiyar Masu Gyaran Motoci ta Kasa (NATA - Nigerian Automobile Technicians Association) da ke Babban Garejin Azare.

Ziyarar ta ba tawagar BWSO damar ganawa da shugaban kungiyar domin tattauna hanyoyin hadin gwiwa da kuma karfafa kokarin bunkasa matasa da ci gaban al’umma.

A yayin ganawar, Coordinator na BWSO a Karamar Hukumar Katagum, Ahmad Musa, ya gabatar da manufofi da ayyukan kungiyar BWSO, inda ya jaddada manufofin kungiyar na bunkasa shugabanci, karfafawa matasa, inganta ilimi, koyon sana’o’i domin dogaro dakai da kuma yi wa al’umma hidima.

Bugu da kari, ya karfafa wa kungiyar NATA gwiwa da ta yi rajista a matsayin 'Affiliate Group' ta BWSO, domin kasancewa cikin kungiyoyin hadin gwiwa karshin BWSO.

Shugaban NATA, Alhaji Abdullahi Dadata, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar na Jihar Bauchi, kuma Mukaddashin Shugaba na Shiyyar Katagum, ya yi maraba da tawagar BWSO tare da nuna godiyarsa bisa wannan ziyara da karamci.

Ya jaddada muhimmancin tallafawa matasa, yana mai cewa mafi yawan matsalolin da al’umma ke fuskanta na da alaka da rashin samun taimako da damammakin ci gaba ga matasa. Ya kuma bayyana cewa tun shekaru da dama yana taka rawa wajen shirye-shiryen bunkasa matasa da karfafarsu.

Shugaban ya yaba da yadda Dr. Bala Wunti ke ci gaba janwo matasa a jiki da kuma jajircewarsa wajen tallafawa shirye-shiryen da ke kawo ci gaba da tasiri mai kyau ga al’umma.

Ya kuma bayyana cewa kungiyar NATA tana da mambobi sama da 528 da s**a yi rajista a cikin garejin Azare kadai, yayin da adadin mambobinta a daukacin al’ummar Katagum ya zarce 2,000, lamarin da ya sanya ta cikin manyan kungiyoyin sana’o’i mafi girma a yankin.

An kammala taron cikin yanayi na fahimtar juna da hadin kai, inda bangarorin biyu s**a tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da hada hannu wajen karfafawa matasa, bunkasa sana’o’i da kuma inganta shirye-shiryen ci gaban al’umma a fadin Katagum.

Ahmad Musa
BWSO Coordinator
Katagum local govt

18/06/2026
18/06/2026

BWSO Katagum takai ziyara ofishin N.U.R.T.W domin tattauna muhimman abubuwa.

BWSO Katagum Ta  Ziyarci Ƙungiyar Ma'aikatan Sufurin Hanya ta Ƙasa (NURTW), reshen karamar Hukumar KatagumƘungiyar Bala ...
18/06/2026

BWSO Katagum Ta Ziyarci Ƙungiyar Ma'aikatan Sufurin Hanya ta Ƙasa (NURTW), reshen karamar Hukumar Katagum

Ƙungiyar Bala Wunti Support Organisation (BWSO), reshen Ƙaramar Hukumar Katagum, ta ci gaba da kai ziyara ta musamman domin haɗin gwiwa da yada manufofinta acikin al-umma, ayayin da takai ziyarar girmamawa ga Ƙungiyar Ma'aikatan Sufurin Hanya ta Ƙasa (NURTW), reshen Ƙaramar Hukumar Katagum, a ofishinsu dake babbar tasha, Azare.

A jawabinsa, BWSO Coordinator na Ƙaramar Hukumar Katagum, Ahmad Musa, ya gabatar da BWSO a matsayin ƙungiya mai jagorancin matasa kuma mai mayar da hankali kan ci gaban al’umma. Ya bayyana cewa ƙungiyar tana da burin ƙarfafawa matasa gwiwa wajan dogaro dakai, shugabanci nagar, jagoranci mai bullewa, , inganta ilimi da kuma samar da tasiri mai kyau ga al’umma.

BWSO Coordinator ya kuma yi wa ƙungiyar bayani kan Babban Taron Ranar Ƙwarewar Matasa ta Duniya (World Youth Skills Day – WYSD) na shekarar 2026, wanda za a gudanar a Azare ranar 15 ga Yuli, 2026, Wanda akayi masa take daS "kills for the shared future".

A nasa jawabin, Shugaban NURTW na Ƙaramar Hukumar Katagum, Alhaji Ismail Abubakar, ya yi maraba da tawagar cikin girmamawa tare da yin bayani kan ƙungiyar da rassanta da ke faɗin ƙaramar hukumar. Sannan ya nuna farincikinsa ganin yadda aka girmamasu da mutuntasu.

Shugaban ya yaba da ziyarar tare da yi wa BWSO, shugabanninta da duk masu ƙoƙarin inganta rayuwar matasa da al’umma addu’ar samun nasara. Haka kuma ya yi addu’ar Allah Ya kiyaye tawagar a hanyarsu ta komawa gida.

AMANA SICKLE CELL FOUNDATION VISITS BWSO KATAGUM LGA OFFICEYesterday, Monday, June 1st, 2026, our office officially re-o...
02/06/2026

AMANA SICKLE CELL FOUNDATION VISITS BWSO KATAGUM LGA OFFICE

Yesterday, Monday, June 1st, 2026, our office officially re-opened after the Sallah break with a very special and important visit from the leadership of the Amana Sickle Cell Foundation.

The Coordinator, Ahmad Musa, hosted the delegation to deliberate on critical areas of humanitarian service and health advocacy for our communities. The session provided an excellent opportunity to explore how we can channel our shared values into sustainable, grassroots-driven healthcare interventions that protect and support vulnerable individuals across Katagum Local Government Area.

During the engagement, the foundation shared their extensive network of domestic and international partnerships. They highlighted their active alignments with globally recognized health bodies and organizations, including:
• Global Alliance for Sickle Cell Disease Organizations
• Global Action for Sickle Cell Disease and Other Inherited Blood Disorders
• Global Alliance for Non-Communicable Diseases
• Nigerian Non-Communicable Diseases (NCDs) Alliance
• World Health Organization (WHO)
• Federal Ministry of Health and Social Welfare
• Nigerian Heart Foundation

We are deeply encouraged by this visit and look forward to leveraging these institutional standards to roll out impactful health sensitization and relief programs. Together, we remain fully committed to our core mission of selfless community service and uplifting those who need it most.

TRULY TALENTED LIMITED (TTL) COLLABORATES WITH BALA WUNTI SUPPORT ORGANIZATION (BWSO) TO TRAIN 30 STUDENTS LEADERS IN KA...
25/05/2026

TRULY TALENTED LIMITED (TTL) COLLABORATES WITH BALA WUNTI SUPPORT ORGANIZATION (BWSO) TO TRAIN 30 STUDENTS LEADERS IN KATAGUM

TTL, in collaboration with BWSO, is Organising a Capacity Building Workshop on Leadership, Personal Branding, Scholarship, Communication and Leveraging Technology for Success.

The one-day training is set to hold on Saturday, 30th May 2026 in Azare with 6 sessions to be facilitated by equally passionate emerging leaders.

The target participants are predominantly Katagum students in tertiary institutions who have exhibited some zeal towards leadership and service.

If you are passionate about honing your leadership skills, please apply via the Google Form link below:
https://forms.gle/S5Z5qrHxs6rnRRa79

There are limited slots. The training is completely free of charge. Other details are as contained in the attached flyer.

Address

General Hospital Road
Azare
751101

Opening Hours

Monday 08:00 - 16:00
Tuesday 08:00 - 16:00
Wednesday 08:00 - 16:00
Thursday 08:00 - 16:00
Friday 08:00 - 13:00

Telephone

+36703600585

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bala Wunti Support Organisation - Katagum LGA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Bala Wunti Support Organisation - Katagum LGA:

Shortcuts

Share