Bauchi State Fire Service

Bauchi State Fire Service Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bauchi State Fire Service, Government Organization, ADAMU JUMBA Road, G. R. A. BAUCHI, Bauchi.

ZIYARAR TAYA MURNA.Ƙungiyar masu sauraron gidan rediyon Globe FM Bauchi, ƙungiya ce da take da kyakkyawar alaƙa da kuma ...
20/08/2026

ZIYARAR TAYA MURNA.

Ƙungiyar masu sauraron gidan rediyon Globe FM Bauchi, ƙungiya ce da take da kyakkyawar alaƙa da kuma zumunci da hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi. Kasancewar haka ne yasa shugaban ƙungiyar, Mallam Sadisu Rabin Dami, ya jagoranci tawagar wasu daga cikin 'yan ƙungiyar inda s**a kawo ziyara hedkwatar hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, a yau Alhamis.

Mal. Sadisu, ya ce sun kawo ziyarar ne domin su taya Bldr Dauda B. Pali MNIOB, murnar tabbatar mishi da muƙamin shugaba mai cikakken iko na hukumar da akayi a kwanannan. Daga nan kuma ya yi addu'ar Allah Ya ci gaba da yiwa shugaban jagoranci, Ya kuma kare shi.

Shugaban hukumar, yayi godiya wa 'yan ƙungiyar akan ziyara da kuma addu'ar da s**a yi.

GENERAL FALL-IN.The Bi-monthly General fall-in of The Officers and Men of The BSFS, took place today Wednesday, the 19th...
19/08/2026

GENERAL FALL-IN.

The Bi-monthly General fall-in of The Officers and Men of The BSFS, took place today Wednesday, the 19th at The headquarters of The Service.

***********

Yau Laraba, sha tara ga wata, aka gudanar da taron Manya da kuma ƙananan jami'an hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi.

CONGRATULATORY VISIT.In continuation of the congratulatory visit by family members, friends and well-wishers of Bldr Dau...
13/08/2026

CONGRATULATORY VISIT.

In continuation of the congratulatory visit by family members, friends and well-wishers of Bldr Dauda B. Pali MNIOB, to felicitate with him on his recent confirmation as The Substantive Director of The BSFS. This evening his relatives paid him a congratulatory visit.

***************

ZIYARAR TAYA MURNA.

Da yammacin yau ne 'yan uwan Bldr Dauda B. Pali s**a kawo ziyarar taya murna wa ɗan su, dangane da tabbatar da naɗin shi a matsayin shugaba mai cikakken iko hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi.

A CONGRATULATORY VISIT.A group of The old boys of The defunct Government Science Secondary School Kafin Madaki, visited ...
13/08/2026

A CONGRATULATORY VISIT.

A group of The old boys of The defunct Government Science Secondary School Kafin Madaki, visited the headquarters of The BSFS, today Thursday the 13th, where they congratulated Bldr Dauda B. Pali MNIOB (a former student of the school) on his recent confirmation
as The Substantive Director of The Bauchi State Fire Service.

***********

ZIYARAR TAYA MURNA.

Ƙungiyar tsofaffin daliban tsohuwar makarantar sakandaren Kimiyya ta Kafin Madaki, a yau Alhamis, s**a ziyarci hedkwatar hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, in da s**a taya Bldr Dauda B. Pali MNIOB (tsohon ɗalibin makarantar) murna tabbatar da naɗin shi da akayi a matsayin shugaba mai cikakken iko na hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi.

Address: ADAMU JUMƁA ROAD, GRA BAUCHI.

EMERGENCY NUMBERS 09038352982 and 07086463943.

STAND BY DUTY.A crew of five (5) firefighters of The Bauchi State Fire Service, were on a stand by duty at the venue of ...
10/08/2026

STAND BY DUTY.

A crew of five (5) firefighters of The Bauchi State Fire Service, were on a stand by duty at the venue of the official commissioning of the roads constructed by His Excellency, Senator Bala Abdkulƙadir Mohammed, Ƙauran Daular Uthmaniyya, The Executive Governor of Bauchi State and also at the venue of the official flag-off of the construction of the unity park, which were both performed by The Former President Of The Federal Republic Of Nigeria, His Excellency Goodluck Ebele Jonathan, today Monday the 10th of August.

The crew was led by PDFO Ahmad M Katagum, other members of the crew were:
DFO Tajuddeen Haladu.
StnO Mahmuda Husaini.
StnO Idris Ibrahim Gital and
StnO Nuhu Markus.

***********
ZAMAN SHIRIN KO TA KWANA

Tawagar jami'ai biyar na hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi ne, s**a yi zaman shirin ko ta kwana a wajen da
aka ƙaddamar da bikin buɗe hanyoyin da Mai Girma Gomnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed, Ƙauran Daular Uthmaniyya ya yi, da kuma wajen da aka aza tubalin ginin dandalin shaƙatawa na zamani wanda Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan
ne ya ƙaddamar da buɗe hanyar da kuma aza tubalin fara ginin dandalin, a yau Litinin, goma ga wata.

PDFO1 Ahmad M Katagum ne ya jagoranci tawagar wacce ta haɗa da:
DFO Tajuddeen Haladu.
StnO Mahmuda Husaini.
StnO Idris Ibrahim Gital da kuma
StnO Nuhu Markus.

A satin daya wuce shirin gidan rediyon BRC, na baƙonmuya karɓi baƙuncin shugaban hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, Bl...
09/08/2026

A satin daya wuce shirin gidan rediyon BRC, na baƙonmu
ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, Bldr Dauda B. Pali MNIOB, kasancewar ba'a gama tattaunawa da shugaban ba a satin daya gabata, hakan yasa a yau Lahadi Tara ga wata, shugaban ya sake komawa gidan rediyon inda aka sake gabatar da shirin ta re da shi.

A wannan karon, Bldr Pali, ya yi bayani akan yadda jami'an shi suke gudanar da ayyukan su da kuma irin ƙalubalen da a wasu lokutan suke fuskanta, musamman na yin katsalandar da wasu jama'a s**an yi musu a yayin gudanar da aikin su.

Shugaban, ya yi ƙarin bayani dangane da irin kayan aikin da Mai Girma Gomnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed, Ƙauran Daular Uthmaniyya, ya siya wa hukumar. Daraktan kuma ya yi bayani akan jami'an hukumar, inda yayi bayyani dangane da shirin tura jami'an domin ƙara samun horo, wanda tuni, shirye shirye sun yi nisa domin fara tura su.

A cikin irin gudunmawar da masu sauraron shiri s**a bayar a lokacin da aka basu damar kiran waya, sun yi godiya wa Mai Girma Gomna dangane da kayan aikin da ya samar wa hukumar, inda s**a roƙi Mai Girma Gomna da ya ƙara wa hukumar motocin aiki, kasancewar ayyukan Mai Girma Gomna na ci gaba daya aiwatar sun mayar da Bauchi zuwa babban birni.

THE PORTRAITS.
09/08/2026

THE PORTRAITS.

The meeting of The Bauchi State Security Council was held today Thursday 6th August at the executive council chamber of ...
06/08/2026

The meeting of The Bauchi State Security Council was held today Thursday 6th August at the executive council chamber of The Government House.

The Executive Governor of Bauchi State, His Excellency, Senator Bala Abdkulƙadir Mohammed, Ƙauran Daular Uthmaniyya, presided over the meeting.

The Director of The Bauchi State Fire Service, Bldr Dauda B. Pali, MNIOB being a member of the security council, attended the meeting.

Also in attendance were The heads of all the military formations in the state, The Police Commissioner, State Director of The DSSS, All The heads of The Paramilitary in the state and The Heads of other security agencies.

The Deputy Governor of Bauchi, Hon. Auwal Jatau and His Royal Highness, The Emir of Bauchi, Dr Rilwanu Sulaiman Adamu were also in attendance.

***********

Majalisar tsaro ta jihar Bauchi, a yau Alhamis, shida ga wata, tayi zaman taron ta a babban zauren majalisar zartarwa na gidan gomnatin jiha.

Mai girma Gomnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdkulƙadir Mohammed, Ƙauran Daular Uthmaniyya, shi ne ya jagoranci zaman.

Shugaban hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, Bldr Dauda B. Pali MNIOB, kasancewar shi ɗan majalisar tsaron, ya halarci zaman da majalisar tayi.

Sauran 'yan majalisar tsaron da s**a halarci zaman, sun haɗa da, dukkanin shugabannin hukumomin sojoji da ke jiha, komishinan 'yan sanda, shugaban hukumar DSSS, dukkanin shugabannin hukumomi masu ɗamara.

Mai Girma Mataimakin Gomnan Jihar Bauchi, Hon. Auwal Jatau da kuma Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Sulaiman Adamu, suma sun halarci zaman taron.

SEEING IS BELIEVING.Some of the achievements recorded by Bldr Dauda B. Pali, MNIOB, during the period of his acting capa...
05/08/2026

SEEING IS BELIEVING.

Some of the achievements recorded by Bldr Dauda B. Pali, MNIOB, during the period of his acting capacity as The Director of The Bauchi State Fire Service.

* General renovation and refurnishing of the recreational room of the BSFS.

* Upgrading the control room of BSFS to a modern one
by providing modern communication equipment.

*Refurbishing of the 18 seater utility bus.

* Annual distribution of uniform materials and accessories to the personnel.

* Became the first State Fire Service Director from the northern part of Nigeria that hosted The Annual Conference of The 36 States Fire Services Directors and Chiefs.

* Became The First Director in the history of The BSFS that commemorated the international fire safety day, during which the personnel of The BSFS went round the major streets in the Bauchi metropolis and also visited the major markets and motor parks to sensitize the people on fire safety.

* Embarked on sensitization and enlightenment campaign tour of the major Juma'at mosques and churches.

* Paid a courtesy visit to all the security agencies in the state.

* Paid a courtesy visit to all the media outlets in the state.

*Led his team of gallant personnel that successfully rescued six persons from a two storey building that collapsed on them at Sir Kasim Ibrahim road, old GRA.

* Led the team of fire investigators to Bill and Melinda Gates College Of Health Technology Ningi, where they investigated the cause of the fire outbreak that destroyed the college library, computer laboratory and other facilities.

************

GANI YA KORI JI.

Wasu daga cikin ayyuka da kuma nasarorin da Bldr Dauda B. Pali, MNIOB ya samu a lokacin da yake muƙadassin shugaban hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi.

*Yin kwaskwarima wa ɗakin kwanan jami'an hukumar da kuma sanya duk kayan da s**a kamata.

* Ɗaga darajan ɗakin gudanarwa (control room) na hukumar zuwa na zamani, inda aka sanya mi shi kayan sadarwa na zamani.

*Gyaran Bus ɗin hukumar.

*Raba yadin uniform, hula, belt da sauran kayayyakin da s**a kamata.

* Bldr Pali, shi ne ya kafa tarihi a matsayin shugaban hukumar kwana kwana na farko daga arewacin ƙasar nan da ya karɓi baƙoncin taron dukkanin shugabannin hukumomi kwana kwana na jihohi 36 na ƙasar nan.

* Shugaban ya sake kafa wani tarihin, a inda shi ne shugaba na farko a jerin wanda s**a shugabanci hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, da ya shirya bikin tunawa da ranar kare afkuwar gobara ta duniya, wanda a lokacin jami'an hukumar s**a zagaya manyan hanyoyin cikin garin Bauchi, s**a kuma ziyarci kasuwanni da kuma tashoshin mota inda s**a faɗakar da al'umma akan matakan kariya daga iftila'in gobara.

*Shugaban, ya shirya ziyarar ran gadin masallatan Juma'a da kuma majami'u domin ƙara wayar wa jama'a kai dangane da ɗaukar matakan kariya daga iftila'in gobara.

* Ziyarar dukkanin hukumomin tsaro.

*Ziyarar kafafen watsa labarai.

* Shugaban, ya jagoranci jami'an shi zuwa aikin ceton wasu mutane shida da gini ya rushe a kan su, inda da taimakon Allah, dukkan su shida, aka ceto su da ransu.

* Shugaban, ya jagoranci tawagar masu bincike na hukumar zuwa makarantar koyar da jinya ta Ningi, inda s**a gudanar da binciken dalilin da ya haddasa gobarar da ta ƙona ɗakin karatu da kuma ɗakin na'urori masu ƙwaƙwalwa na makarantar gami kuma da wasu gine-gine.

CONGRATULATIONS ON YOUR  MERITORIOUS AND WELL DESERVED CONFIRMATION.We are expressing our profound gratitude to The Almi...
05/08/2026

CONGRATULATIONS ON YOUR MERITORIOUS AND WELL DESERVED CONFIRMATION.

We are expressing our profound gratitude to The Almighty Allah, through Whose willpower, The Bauchi State Civil Service Commission, on its weekly sitting which was held on Tuesday 4th August, confirmed the appointment of Bldr Dauda B. Pali, MNIOB as The Full Director of The Bauchi State Fire Service.

We are praying to Almighty Allah to continue assisting our amiable Director in his efforts of transforming The BSFS into one of The best State Fire Service in Nigeria.

Once again, congratulations Sir.


***********

SAƘON TAYA MURNA BISA TABBATAR DA NAƊA KA A MATSAYIN DAREKTA MAI CIKAKKEN IKO.

Godiya marar iyaka ga Allah Maɗaukakin sarki, wanda a cikin ikon Shi ne, hukumar kula da ma'aikata ta jihar Bauchi (CSC), a zaman da tayi a ranar Talata Huɗu ga watannan, ta tabbatar da naɗin Bldr Dauda B. Pali MNIOB, a matsayin SHUGABA MAI CIKAKKEN IKO na hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi.

Muna roƙon Allah da Ya ci gaba da yiwa Shugabanmu jagora a bisa kan hanya madaidaiciya kuma muna ƙara roƙon Shi da Ya ci gaba da taimakawa Shugabanmu a ƙoƙarin daya ke yi na ganin ya mai da hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, ɗaya daga cikin hukumomin kwana kwana na jiha mafi inganci a Najeriya.

Muna taya ka murna, Muna taya ka murna, Muna ƙara taya ka murna.

Address

ADAMU JUMBA Road, G. R. A. BAUCHI
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bauchi State Fire Service posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Bauchi State Fire Service:

Shortcuts

Share