Mansur Movement for Senator

Mansur Movement for Senator Shafin tallata ayyukan Hon. Mansur Manu Soro da kiran ya tsaya takarar Sanatan Bauchi ta Tsakiya.

25/12/2025
22/12/2025

Jawabin maman Accords, shugaban matan kiristocin Na Kafin madaki

22/12/2025

bidiyon godiya da addu'a daga bakin Shugaban Kiristoci, a madadin daukacin al'ummar Kirista na garin Kafin Madaki, biyo bayan tallafin buhunan shinkafa da Hon. Mansur Manu Soro (MMS) ya bayar domin bukukuwan Kirsimeti.

Wannan karamci ya kara dankon zumunci da nuna cewa Hon. MMS shugaba ne na kowa da kowa.

Muna godiya da wadannan kalamai masu dadi. Allah ya bar zumunci da zaman lafiya.πŸ™πŸ™

HON. MMS YA RABAR DA BUHUNAN SHINKAFA GA 'YAN UWA KIRISTOCI DAJE GARIN MIYA DOMIN BUKUKUWAN KIRSIMETIA wani yunkuri na t...
22/12/2025

HON. MMS YA RABAR DA BUHUNAN SHINKAFA GA 'YAN UWA KIRISTOCI DAJE GARIN MIYA DOMIN BUKUKUWAN KIRSIMETI

A wani yunkuri na tabbatar da cewa dukkanin bangarorin al'umma sun gudanar da bukukuwan karshen shekara cikin walwala, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Darazo/Ganjuwa, Hon. Mansur Manu Soro (MMS), ya kaddamar da rabon buhunan shinkafa ga 'yan uwa Kiristoci dake garin Miya.

Wannan tallafin na gaggawa ya zo ne daidai lokacin da ake tunkarar shagulgulan Kirsimeti, domin rage radadin rayuwa da kuma tabbatar da cewa iyalai sun samu damar gudanar da murnar su cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Al'ummar yankin sun nuna matukar godiyarsu bisa wannan karamci da ya zo a daidai lokacin da ake bukata.

Daga:



Ita siyasa aiki ce, ba surutu ba. Idan ko aka duba ayyukan da Hon. Mansur Manu Soro  ya shimfida, za a tabbatar cewa shi...
22/12/2025

Ita siyasa aiki ce, ba surutu ba. Idan ko aka duba ayyukan da Hon. Mansur Manu Soro ya shimfida, za a tabbatar cewa shi ne zaΙ“in da ya dace wanda zai iya ciyar da Bauchi Central gaba a 2027 duba da ire-iren manya-manyan ayyukan alheri da yake shimfida wa a halin yanzu da yake matakin Majalisar tarayya.

Koda yaushe muna kara jaddada goyon bayanmu dari-bisa-dari ga wannan tafiya ta alheri. Allah ya kaimu lokacin lafiya, ya sa mu dace. πŸ™


MMansur Movement for Senator


GASKIYAR HALIN DA ASIBITOCIN PEDIATRIC NA MMS KE CIKI A YANZU:Akwai jita-jita da ake yadawa cewa wai Hon. Mansur Manu So...
20/12/2025

GASKIYAR HALIN DA ASIBITOCIN PEDIATRIC NA MMS KE CIKI A YANZU:

Akwai jita-jita da ake yadawa cewa wai Hon. Mansur Manu Soro (MMS) ya watsar da asibitocin yara (Pediatric Hospitals) da ya gina, ko kuma wai ya maida su na kudi (Private).

Wannan ba gaskiya ba ne. Ga ainihin yadda tsarin yake:

DAGA 2021 ZUWA KARSHEN 2024: MMS ne ya dauki nauyin biyan Ma'aikata 64 da duk wani aiki na asibitocin kyauta 100%.

TSARIN DOREWA (SUSTAINABILITY): Don ganin asibitocin sun dore har abada, MMS ya sauya tsarin zuwa "Dogaro Kai". Tun farko MMS ya bada tallafin sama da N66M a matsayin jari da asibitocin zasu dogara da kansu dashi.

YADDA AKE GUDANAR DA ASIBITOTIN A YANZU: Asibitocin yanzu suna cin gashin kansu ne (Self-Sustaining) ta hanyar amfani da wancan jarin da MMS ya bayar.

SUBSIDIZED SERVICE (Rangwame): Ana duba majinyata da rangwamen kudi don a samu damar Juya kudaden (Revolving Fund).

Da wannan dan kudin ne ake biyan alawus din ma'aikatan da kuma sayo karin magunguna don kada asibitin ya durkushe.

Manufar MMS: Gina tsarin da zai tsaya da kafarsa koda bayan ya sauka daga mulki. Wannan shi ne tsarin da ya fi dorewa.

Daga:



HikimarMMS
20.12.2025

Alhamdulillah πŸ™
20/12/2025

Alhamdulillah πŸ™

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mansur Movement for Senator posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share