Mujaddadi TV

Mujaddadi TV WANNAN GIDAN TV AN KIRKIROSHI NE DOMIN TALLATA AYYUKAN SANATAN BAUCHI TA KUDU SANATA SHEHU BUBA UMAR

09/08/2026

Mujaddadi Gwamnan Bauchi 2027

09/08/2026

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un!
Muna mika ta'aziyyar mu zuwa ga Alhaji Muhammad Bello Kirfi (Baba Waziri) bisa ga rasuwar iyalinsa (kuma Uwa gare mu).
Muna mika ta'aziyyar mu zuwa ga ya'ya, da yan'uwa da jikoki tare da addu'ar Allah Ya sanya Aljannah ce makoma gare ta tare da sauran iyayenmu da malamanmu da zurriyyarmu da aminanmu da yan'uwanmu.

08/08/2026

Sannu sa kokari DG SBU VANGUARD Engr Ishaq Dabo da zamu samu irin wannan a tafiyar nan guda 5 da ko Campaign Sanata Shehu Buba bazai fita ba.

Shine kawai Bazai Rushe sarakuna kuma zai kyautatawa yan kasuwa domin mutum ne mai tausayi
08/08/2026

Shine kawai Bazai Rushe sarakuna kuma zai kyautatawa yan kasuwa domin mutum ne mai tausayi

Karamci ne kawai na Al'umma jahar Bauchi yasa muka zabi M.A matsayin Gwamnan jahar Bauchi a 2015 amma munsan badan jahar...
08/08/2026

Karamci ne kawai na Al'umma jahar Bauchi yasa muka zabi M.A matsayin Gwamnan jahar Bauchi a 2015 amma munsan badan jahar bauchi bane, kuma daga karshe yazo ya nuna mana halin baki.

Inji: Alh. Biyali.

SBU VANGUARD TA KADDAMAR DA RABON BILLBOARD DA POSTER A KANANAN HUKUMOMI 20Kungiyar SBU Vanguard ta kaddamar da rabon bi...
08/08/2026

SBU VANGUARD TA KADDAMAR DA RABON BILLBOARD DA POSTER A KANANAN HUKUMOMI 20

Kungiyar SBU Vanguard ta kaddamar da rabon billboards da posters domin tallata ayyuka da manufofin Sanata Shehu Buba Umar a kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi.

Shugaban kungiyar, Engr. Ishaq Dabo, ne ya jagoranci kaddamar da rabon a babbar sakatariyar kungiyar da ke cikin garin Bauchi.

A ranar kaddamarwar, kananan hukumomi hudu ne s**a karbi nasu kayan tallan, wadanda s**a hada da Alkaleri, Ganjuwa, Ningi da Darazo.

Kungiyar ta bayyana cewa rabon zai ci gaba da zuwa sauran kananan hukumomin jihar.

08/08/2026

Sabon Shirin Kafar MUJADDADI TV mai suna MA'AUNIN SIYASA Tare Da Mikael A. Haruna.

ANA NEMAN IYAYEN WANNAN YARINYAR An tsinci wannan yarinyar Tunda yammacin jiya Juma'a 7/8/2026 a wajen Sabuwar kasuwa ta...
08/08/2026

ANA NEMAN IYAYEN WANNAN YARINYAR

An tsinci wannan yarinyar Tunda yammacin jiya Juma'a 7/8/2026 a wajen Sabuwar kasuwa tace:

Sunanta:-Suhaima
Sunan Babanta:-Baban Suhaima
Sunan Mamanta:-Maman Suhaima

Iyayenta ko wanda yasanta zasu iya Tuntubar Wannan Lambar:-0803 887 9870

SANATA SHEHU BUBA UMAR YA HALARCI DAURIN AURE A KANOSanata Shehu Buba Umar ya halarci bikin ɗaurin auren Zainab Rabi'u M...
07/08/2026

SANATA SHEHU BUBA UMAR YA HALARCI DAURIN AURE A KANO

Sanata Shehu Buba Umar ya halarci bikin ɗaurin auren Zainab Rabi'u Muhammad Gwate da angonta Ibrahim Abdullahi Shu'aibu, wanda aka gudanar bayan kammala Sallar Jumu'a a Masallacin Jumu'a na Sheikh Isiyaka Rabi'u da ke Gwauron Dutse, cikin birnin Kano.

Daga cikin manyan baƙi da s**a halarci bikin akwai Mai Girma Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar (Marafan Sokoto), Alhaji Abubakar Muhammad Ɗantabawa (Marafan Bunguɗu), Sanata Lawal Hassan Anka, Hon. Abdulmalik Zubairu (Zannan Bunguɗu), tare da dattawan Jam'iyyar APC na reshen Jihar Zamfara.

A yayin bikin, Mai Girma Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar ne ya bayar da amaryar Zainab Rabi'u Muhammad Gwate ga waliyyin ango, Ibrahim Abdullahi Shu'aibu, bisa koyarwar addinin Musulunci.

An gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali tare da addu'o'in neman albarka ga sabbin ma'auratan domin Allah Ya sanya zaman aurensu ya kasance mai ɗorewa cikin ƙauna, fahimtar juna da albarka.

Mujaddadi Tv
7th August 2026

07/08/2026

DG SBU VANGUARD Engr. ISHAQ DABO YA KADDAMAR DA RABON POSTER DA BILBOARD NA SANATA SHEHU BUBA UMAR......

A yau Juma'a, 7/8/2026 Jagoran Kungiyar nan mai fafutukar ganin sanata Shehu Buba Umar yazama Gwamnan Jihar Bauchi a 2027 Engr. Ishaq Dabo ya kaddamar da rabon kayan tallen Dantakarar Gwamna na jam’iyyar PRP wanda ya fara da kananun hukumomi 4 wanda s**a hada da Alkaleri, Ningi,Ganjuwa da Warji inda duk sun karbi kayansu.

Allah tabbatar mana da Nasara 2027.

PRP NASARA.

Address

Bauchi

Telephone

+2348158383858

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mujaddadi TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share