Bala Wunti Online

Bala Wunti Online "This is the official page of Bala Wunti Online Media Team"
(BW Online Media Team)
Please kuyi following din mu masoya😍🙏

CEO, World Energy Council Nigeria.ACTIVE!
07/09/2026

CEO, World Energy Council Nigeria.

ACTIVE!

Ganjuwa/Darazo ga layin mu nan!ACTIVE!🥳🛜✌️
06/09/2026

Ganjuwa/Darazo ga layin mu nan!

ACTIVE!🥳🛜✌️

Tallafin Filin Masallacin Idi Daga Dr. Bala Wunti - (CEO, WEC Nigeria.)A wani mataki na kishin al'umma da karramawa ga h...
06/09/2026

Tallafin Filin Masallacin Idi Daga Dr. Bala Wunti - (CEO, WEC Nigeria.)

A wani mataki na kishin al'umma da karramawa ga harkar addini, Dr. Bala Wunti ya saye katafaren fili gaba ɗaya domin zama Tabbataccen Filin Masallacin Idi na mutanen Unguwar Wuntin Dada—sakamakon kasancewar al'umar ba su da filin gudanar da sallar Idi na kansu a baya.

Wannan muhimmin aiki zai lakume zunzurutun maƙudan ƙudade, musamman wajen gudanar da babban ciko da gyaran filin domin ya dace da taron al'umma. Babban abin ban girmamawa shi ne, ba tare da wata takara ko neman muƙamin siyasa ba, zuciyarsa na ci gaba da kasancewa buɗe wajen shimfiɗa alheri da hidimta wa jama'a.

Daukacin al'umma da shugabannin Unguwar Wuntin Dada sun mika godiyarsu ta musamman bisa wannan gagarumin tallafi mai tarin albarka.

Muna addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya karɓi wannan sadaƙa mai gudana (Sadaqatul Jariyya), Ya ninka masa dukiya da albarka, kuma Ya sakawa iyayensa da gidan Aljanna. 🤲🕊️

DG. Bala Wunti Online

Abuja National Convention ACTIVE!
06/09/2026

Abuja National Convention ACTIVE!

DR. BALA WUNTI (SHUGABAN WEC NIGERIA): JAGORA MAI HANGEN NESA DA SADAUKARWA 🌐🌟Dr. Bala Wunti, Shugaban Hukumar WEC Niger...
05/09/2026

DR. BALA WUNTI (SHUGABAN WEC NIGERIA): JAGORA MAI HANGEN NESA DA SADAUKARWA 🌐🌟

Dr. Bala Wunti, Shugaban Hukumar WEC Nigeria, na ci gaba da tsayawa a matsayin jagora mai kwarjini da nagarta, wanda jajircewarsa wajen samar da inganci, gaskiya, da ci gaban ƙasa ba ta girgiza. Ta hanyar kyakkyawan hangen nesansa, ya kasance yana samar da ci gaba mai ma'ana tare da zaburar da sauye-sauye masu kyau a fannin makamashin ƙasa da ma baki ɗaya.

Tarihinsa na sauƙin kai, sadaukar da kai wajen aiki, da sha'awar tallafa wa al'umma ya sanya ya samu girmamawa da soyayya mai ɗaurewa. Ya ci gaba da kasancewa jigo na abin koyi da ginshiƙin kyakkyawan shugabanci.

Allah Ya ci gaba da yi masa jagoranci, Ya kare shi, kuma Ya ɗaukaka shi zuwa maƙasudi mafi girma na nasara. 🤲✨

03/09/2026

Naji sun kaddamar da APM free Internet a kasuwar muda lawan😂 Ma sha Allāh

And all credit goes to Balan Alheri for starting the initiative . Muje zuwa Bauchi — Qatar is possible .
ACTIVE ! 🥳🛜✌🏻

02/09/2026

Arc Usman Darazo Ya Raba Taki Buhu 200 Ga Manoman Ganjuwa-Darazo

A yau Laraba, ɗan takarar kujerar Majalisar Tarayya 2027 na mazabar Ganjuwa/Darazo a jam’iyyar APC, Arc. Usman Ya’u Darazo, ya ƙaddamar da rabon takin zamani buhu 200 ga manoma da sauran masu ruwa da tsaki a mazabar, a wani sabon yunƙuri na ƙarfafa harkokin noma da samar da wadataccen abinci.

Waɗan da su ka ci gajiyar shirin sun haɗa da manoma, jagororin addinai, sarakunan gargajiya, shugabannin jam’iyya, ƙungiyoyin mata da matasa da sauran masu ruwa da tsaki, inda aka zaɓo su daga ward 22 na ƙananan hukumomin Ganjuwa da Darazo.

Kowace ƙaramar hukuma ta samu kaso na buhu 100.

Wannan ba shi ne karon farko da Arc. Usman Darazo ke tallafa wa manoma da takin zamani ba, lamarin da ke ƙara nuna yadda yake mayar da hankali kan bunƙasa noma a matsayin ginshiƙin dogaro da kai, samar da abinci da inganta rayuwar al’ummar yankin.

A ranar 23 ga watan da ya gabata, Arc Usman Darazo ya raba tallafin jari da ya kai kimanin Naira miliyan shida ga mata domin ƙarfafa sana’o’insu da taimaka musu wajen dogaro da kansu.

Da yake bayyana manufar shirin, Darakta-Janar na yakin neman zaben Arc. Usman Ya’u Darazo, Mai Girma Sarkin Soro, Alhaji Abdullahi Shehu Yakubu, ya bayyana rabon takin a matsayin matakin farko cikin jerin ayyukan alheri da Arc. Usman Darazo ya ƙuduri aniyar aiwatarwa domin amfanin al’ummar Ganjuwa-Darazo.

Ya buƙaci shugabannin da aka ɗora wa alhakin raba takin da su tabbatar an gudanar da rabon cikin gaskiya, adalci da riƙon amana.

A nasa jawabin, Sakataren yaƙin neman zaben Arc. Usman Ya’u Darazo, Hon. Sha’abdin Bello Zalanga, ya ce tallafin wani ɓangare ne na hangen nesa na Arc Usman Darazo na ganin an ƙarfafa manoma da sauran ƙananan ’yan kasuwa a mazabar.

Ya ƙara da cewa irin waɗannan shirye-shirye na nuna cewa ci gaban al’umma ne babban abubun da Arc. Usman Darazo ya sa a gaba.

Shi ma Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Ganjuwa, Hon. Abdulrahman Umar, ya yaba da shirin, yana mai cewa tallafin zai taimaka wa manoma wajen rage musu kuɗin noman damina. Ya kuma yi kira ga masu cin gajiyar tallafin da su yi amfani da takin yadda ya kamata domin samun amfanin da ake fata.

Taron rabon takin ya samu halartar tsohon Ɗan Majalisar Jiha, Hon. Sale Umar Nabayi, dukkanin Shugabannin APC na ward, Lobito Group Ganjuwa LGA Contact and Mobilisation, Haj. Sadiya Alhassan, Hon. Ɗanliti Miya, Hon. Halilu Firo, Hon. Aminu Lasisi, Hon. Abdulkadir Madaki Gamji, da sauran shugabannin ƙungiyoyin NURTW, mata da matasa.

🖊️ Kamal Ibrahim

01/09/2026

This is not QATAR.
This is Wunti International Academy, WUNTI, Bauchi State.

Some time back, Dr. Bala Wunti spoke about his readiness to "emulate Qatar" to transform Bauchi under his EISY Agenda. A number of us laughed and played with the idea.

Today, this is the proof.
The least he can do.
With visionary people like him, Bauchi — Qatar is possible.

01/09/2026

A kan idonku, Dr. Bala Wunti zai ci gaba da aiwatar da kudurorinsa a kan talakawan Jihar Bauchi.

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bala Wunti Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share