10/09/2022
WANKAN TSARKI A TAKAICE
⚫ Wankan tsarki shine wankan da akeyi domin tsarkake jiki bayan mace ta kammala jinin haila, ko jinin biƙi (jinin haihuwa), ko bayan saduwa, ko mafarkin da zai kai ga fitar maniyyi, haka zalika irin sa ake yi idan mutum ya shiga musulunci da sauransu.
⚫ Wankan tsarki ya kasu kashi biyu, wato akwai wanda yake da siffa ta kamala da kuma wanda yake da siffa ta isarwa. Sai dai mai siffa ta kamala shine mafi a'ala da karbuwa a shari'a.
⚫ WANKAN TSARKI A SIFFA TA KAMALA
* Da farko Mai wanka zai samu ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa. Ma'ana, wanda launinsa, ɗanɗanonsa ko ƙamshinsa bai canza ba.
* Bayan an samu ruwa.mai tsarki kuma mai tsarkakewa,, sai a fara wanke hannaye sau uku kafin a tsoma su cikin ruwan.
*Bayan wanke hannaye sau uku,, sai a ƙulla niyya. Ita dai niyya kamar yadda muka sani, a zuci ake ƙudirce ta, kuma karantata a fili kamar yadda wasu malaman Malikiyya s**a koyar babu laifi. Haka zalika, wasu malaman na ganin daga sanda mutum ya dauki ruwa da tunanin yin wankan tsarki, to niyya ta shiga. Don haka, babu bukatar sake maimaita niyya.
*Daga nan sai a wanke daga cibiya zuwa mara, har sau uku, wato inda aka fi zaton najasar ta taba; mutum zai wanke gabansa kenan sosai.
* Bayan an wanke sau uku sai a yi alwala irin alwalar da ake yi yayin da za a yi salla, sai dai ba za a wanke ƙafa ba, ƙafa ce kawai ba za a wanke ba.
* Bayan nan, sai a koma a shafi kai, sai a tsoma hannaye biyu cikin ruwan, sai a fito da su, sai a sanya hannayen nan a kai a dan cuccuɗa ko’ina ta yadda damshin ruwan dake hannun mutum zai samu ko’ina a kan
* Daga nan kuma, sai a wanke kai zuwa wuya har sau uku. Idan mutum yayi marra daya ma babu laifi. Ahammu dai a game wurin da ruwa.
* Sai a koma a wanke jiki, a fara da ɓarin dama a wanke daga kafaɗa zuwa ƙasa sau uku, sai ɓarayin hagu shi ma haka sau uku, amma a tabbatar bayan ma ya samu ruwa.
* Bayan wannan sai a yi taku ɗaya daga inda ake, bayan an yi taku ɗaya sai a je a wanke ƙafa, wato cikon alwalar da ba a yi ba.
* Daga nan kuma sai a game jiki da ruwa. A tabbatar ko'ina ya samu ruwa ba tareda an bar lam'a ba. Yin hakan wajibi ne.
Shikenan wanka ya kammala. Kuma malamai da dama sun tafi akan cewa, wannan alwala ta cikin wanka ta ishi mutum yayi Sallah. Matukar bai shafi al'aurarsa da zahirin hannunsa ba.
Haka zalika idan mutum yayi wanka bisa tsarin marra daidai, to wankansa yayi. Sai dai anfi so abi wancan tsari.
Wallahu A'alam.
10-09-2022