Kebbi State Hisbah

Kebbi State Hisbah official page of kebbi state hisbah Board, cabinet office Birnin Kebbi

HUKUMAR HISBAH TA JAHAR KEBBI TA DAKILE TARON "SIGN OUT" NA WASU ƊALIBAI A BIRNIN KEBBIHukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta ...
25/07/2026

HUKUMAR HISBAH TA JAHAR KEBBI TA DAKILE TARON "SIGN OUT" NA WASU ƊALIBAI A BIRNIN KEBBI

Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta samu rahoton sirri cewa wasu ɗalibai maza da mata sun shirya gudanar da wani taro da ake kira "Sign Out", wanda ya saɓa da koyarwar Addinin Musulunci, a tsohon ginin Ministry for Women's Affairs da ke Birnin Kebbi.

Bayan samun wannan rahoto, Hukumar Hisbah ta tura dakarunta cikin gaggawa domin dakile faruwar wannan taro.

Alhamdulillah, dakarun Hisbah sun yi nasarar dakile wannan taro na maza da mata kafin a gudanar da shi.

Don haka, Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi tana ƙara kira ga iyaye da masu kula da yara da su ƙara sanya ido kan 'ya'yansu, tare da tabbatar da cewa suna nisantar duk wani abu da ya saɓa wa koyarwar Addinin Musulunci da kyawawan ɗabi'u.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara shiryar da 'ya'yanmu baki ɗaya, Ya kuma kare su daga dukkan abin da zai cutar da addininsu da tarbiyyarsu. Ameen.

24/07/2026

SANARWA SANARWA SANARWA

Wani bawan Allah Dan kishin kasa mazauni garin Argungu Yana Bada cigiyar dangin wannan matar ko Wanda yassan ta da yaje offishin Hisbah dake garin Argungu don asada su dashi matar tana cikin damuwa ko yanayi tabin hankali tace ita Mutunniyar Kauyen Mai Garaya Ce Daga Magami Local Government Niger State Don haka ake Neman duk Wanda keda bayani akanta da ya taimaka, Kakakin Cikin Gida

22/07/2026

SANARWA SANARWA SANARWA

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi na sanar da daukacin shugabannin makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu cewa, an haramta gudanar da duk wani jerin gwano (Sign-Out) ko wani taro da ke da alaka da kammala jarabawar sakandare.

An dauki wannan mataki ne domin kare tarbiyyar matasa da kuma tabbatar da bin koyarwar addinin Musulunci da kyawawan dabi'un al'ummar Jihar Kebbi.

Hukumar tana kira ga iyaye, masu kula da makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken hadin kai wajen tabbatar da bin wannan umarni.

Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

Surajo Usman Kamba
Director Shari'a
Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi

ANGANE UWAYEN WANNAN YARONAI SUNA NAFIU HUKUMAR HISBAH TA HANNANTA SHI GA IYAYENSA ALHAMDULILLAH @ FOLLOWERS
10/07/2026

ANGANE UWAYEN WANNAN YARONAI SUNA NAFIU HUKUMAR HISBAH TA HANNANTA SHI GA IYAYENSA ALHAMDULILLAH @ FOLLOWERS

SANARWA SANARWA SANARWA Hukumar hisbah ta jihar kebbi na bada sanarwar ankawo mata wannan yaron Mai hoto a kasa yaron Ba...
10/07/2026

SANARWA SANARWA SANARWA

Hukumar hisbah ta jihar kebbi na bada sanarwar ankawo mata wannan yaron Mai hoto a kasa yaron Bai iya cikakken bayani da zai sa agane danginsa

Yace sunansa Nafi'u sunan mamarsa Gwaggo, sunan baban sa Mal umaru makaho, yanada yannansa guda 3, akwai Dan baba, da muddaha, sai Daha
Yaron yace Yana karantun allo gidan Mal Muhammad baban Abbasa mutawalle, yakara.da cewa sunan garinsu lageji kusa da wani gari da ake kira Bangi, yace kasuwar garinsu anace da ita yar kwano,

Yakara da cewa sunzo Birnin kebbi gudun hijira don garin su an kori kowa,.don haka hukumar hisbah ke rokon jamaa da cewa duk wanda.yassan shi ko wani bayani akansa da.ya tuntubi.hukumar Hisbah a office dinta dake tsohuwar cabinet office kusa da tashar haliru Abdu, ko wayannan lanbobin

07064854866, 07064419954 ko 08039367357
Allah sa adace ameen

HUKUMAR HISBAH TA JIHAR KEBBI TAKAI SAMAME WANI HOTEL GARIN ARGUNGU TAKAMA MUTUM 25 TSAKANIN MAZA DA MATAA yau, 03/07/20...
03/07/2026

HUKUMAR HISBAH TA JIHAR KEBBI TAKAI SAMAME WANI HOTEL GARIN ARGUNGU TAKAMA MUTUM 25 TSAKANIN MAZA DA MATA

A yau, 03/07/2026, Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta kai wani samame a wani otel da ke garin Argungu, inda ta yi nasarar k**a mutane 25 da ake zargi da aikata baɗala. Wadanda aka k**a sun haɗa da samari 12 da kuma 'yan mata 13.

An gudanar da samamen ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Hukumar Hisbah na ci gaba da yaƙi da munanan ɗabi'u da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaftar tarbiyya a faɗin Jihar Kebbi.

Hukumar ta bayyana cewa za a gudanar da bincike bisa doka domin tabbatar da gaskiyar lamarin, sannan duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci matakin da doka ta tanada.

01/07/2026

WATA MATA TA DAURA AURE CIKIN AURE MIJI BIYU MATA DAYA BATARE DA SANIN IYAYENTA BA AKWAI ZARGIN TABIN HANKALI.GARETA

ABIN AL'AJABI!

Wani lamari mai cike da mamaki ya taso, inda wani mutum ya auri wata mata ba tare da sanin cewa tana ƙarƙashin auren wani ba.

Bisa bayanan da aka samu, mutumin ya haɗu da matar a kan hanya, inda ya bayyana mata ƙaunarsa. Ita ma ta amince da tayin auren, har s**a cimma yarjejeniya kan sadakin naira ₦500,000, wanda ya biya ta hanyar tura kuɗi zuwa asusun bankinta.

Daga nan, matar ta umurce shi da ya nemo masu ɗaura aure, kuma aka gudanar da ɗaurin auren. Bayan an kammala, mutumin ya kira mahaifinta domin sanar da shi cewa ya auri 'yarsa. Mahaifin ya taya su murna tare da yi musu fatan alheri.

Bayan haka, matar ta sanar da shi cewa za ta tare da shi ne bayan ya kammala shirye-shiryen gidan da za su zauna. Yayin da mutumin ke ci gaba da gyare-gyaren gidan, sai matar ta sake kiransa ta bayyana masa cewa shi ba mijinta ba ne, domin a lokacin da ya aure ta tana ƙarƙashin auren wani mutum.

A yayin gudanar da bincike, an gano cewa wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan lamari ya faru da ita ba. Da aka tambayi mahaifinta ko yana da masaniya kan auren da ta taɓa yi a baya, sai ya bayyana cewa ya san da auren farko, domin an sanar da shi a lokacin. Amma bai san da auren na biyu ba, saboda ba a sanar da shi ba. Wannan kuwa shi ne aure na uku da ya samu labarinsa.

Hukumar Hisbah ta kuma tuntubi mutumin da matar ta yi iƙirarin cewa tana ƙarƙashin aurensa. Shi kuwa ya tabbatar wa Hukumar Hisbah cewa tun tuni ya sake ta, don haka ba ta ƙarƙashin aurensa a lokacin da ta yi wannan iƙirari.

Haka kuma, akwai alamun da s**a sa ake zargin matar na iya fuskantar wata matsala da ke buƙatar ƙarin bincike da kulawar masana, saboda haka ba za a iya yanke hukunci kan lamarin ba sai an kammala bincike.

Wannan al'amari ne ya haifar da ruɗani da rikici, wanda ya sa aka kai ƙorafi ga Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi domin ta binciki lamarin tare da samar da mafita bisa koyarwar addinin Musulunci da kuma bin hanyoyin doka.

Jama'a, mene ne ra'ayinku ko shawararku kan wannan lamari?

22/06/2026

HUKUMAR HISBAH TA JIHAR KEBBI TA CHAFKE WASU BATA GARI DAKE KARBAN KUDDI GA MASU LAIFI DA SUNAN SU JAMIAN HISBAH NE AMMA.NA BUGI

Yau litinin wata bayani da yafito da Dan leken asirrin farin kaya dake aiki.da hukumar Hisbah ya rubutama office shin su cewar yanzu haka akwai mutun biyu dake hannun hukumar Hisbah wadanda sunka shahara wajen karban kuddi ga mutane masu aikatar badala.da sunan su Yan Hisbah ne inda s**a k**a wani.mutum da yacce sun karbi.kuddi har #150,000 hannun sa Dan leken asirrin yace wayanda ake tuma sun tabbatar da karban kuddin har sun mai.da masa abin sa rahoton yaci.gaba da cewa wadanda da ake tuma ba maaikatan Hisbah bane k**ar yadda rahoton ya bayyana dayan maaikacin Yan Banga ne dayan kuma maaikacin hukumar gyaran hali ne ta kasa inda shi Dan leken asirrin ya sanar da offishin su don sanin abin da ake ciki da kuma daukar matakin na gaba.

12/06/2026

WASU SAMARI SUN SHIRYA YIN AUREN DA BA MASA NIYAR IYAYENSU KO WALI DAGA KOWANE
BANGARE, SUN SHIGA HANNUN HISBAH

A jiya Alhamis, 11/06/2026, Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta samu nasarar dakile wani yunƙurin aure da wasu matasa s**a shirya gudanarwa ba tare da sani ko amincewar iyayensu ba.

Binciken farko ya nuna cewa matasan sun gayyaci abokai da ƙawaye domin halartar da kuma gudanar da wannan aure ba tare da bin ƙa'idodi da sharuddan da Shari'a da doka s**a tanada ba.

Hukumar Hisbah ta samu rahoton wannan al'amari ne daga wani mazaunin unguwar Nassarawa da ke Birnin Kebbi, inda jami'anta s**a gaggauta kai dauki tare da dakatar da shirin kafin a aiwatar da shi.

A halin yanzu, Hukumar na ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin yadda lamarin ya kasance da kuma ɗaukar matakan da s**a dace bisa tanadin doka.

Hukumar Hisbah tana jan hankalin matasa da su guji shiga duk wani al'amari da ya shafi aure ba tare da bin hanyoyin da Shari'a da doka s**a tanada ba, musamman samun yardar iyaye da waliyyai. Haka kuma tana kira ga iyaye da su ƙara sanya ido kan harkokin 'ya'yansu tare da ba su tarbiyya da shawarwari masu kyau domin kaucewa fadawa cikin irin waɗannan matsaloli.

Address

Cabinet Office Birnin Kebbi
Birnin-Kebbi
860101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kebbi State Hisbah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share