05/08/2026
Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris, ya sake kiran wani taron gaggawa kan harkokin tsaro domin ƙara ƙarfafa tsarin tsaro da kuma magance sabbin matsalolin tsaro da s**a bayyana a wasu sassan jihar.
Kwamishinan Harkokin Cikin Gida da Tsaro na Jihar Kebbi, Alhaji Haliru Wasagu, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin bayani bayan kammala taron.
Ya ce an gudanar da taron ne domin yin cikakken nazari kan halin tsaro a jihar, tare da sake duba da inganta dabarun da ake amfani da su wajen yaƙi da masu aikata laifuka, domin tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin al'umma.
Alhaji Haliru Wasagu ya ce Gwamna Nasir Idris ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar, yana mai cewa za a ci gaba da farautar masu aikata laifuka tare da rusa maboyarsu.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka k**a da hannu wajen aikata laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada ba tare da sassauci ba.
Kwamishinan ya yi kira ga al'ummar jihar da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin lokaci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen gano da k**a masu aikata laifuka cikin sauri.
A ƙarshe, ya yaba da ƙoƙari, jajircewa da sadaukarwar jami'an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Jihar Kebbi.