09/02/2022
Assalamu Alaikum
His Royal Highness Yusuf Abubakar Sambo II (National Vice Chairman 1 of Inter-Tribal Traditional Leaders Association of Nigeria ITTLAN and Sarkin Hausawan Enugu) held a meeting with Garriki Youths Association on Sunday 6th Febuary 2022.
Recall that few weeks ago, some members of the association met him and reported the problems the association is facing in the process of electing new executives of the association which resulted to divisions within the members of the association.
Due to his love for the unity and progress of youths, he intervened immediately to ensure that peace is restored to the association, which after series of meetings with the executives and other members of the association, a consensus candidate for the position of chairman of the association was agreed by both sides.
Mal Auwal Muhammad who is the current Secretary of the association was selected to be the incoming chairman of the association by consensus.
His Royal Highness Yusuf Abubakar Sambo II further instructed the members of the association to go and fill in other capable members in the remaining executives positions for proper innauguration and presentation of certificate.
✍️
Aliyu Adamu kwankwaso
(Media Aide to Enugu State Hausa Emirate Council)
Assalamu Alaikum
Mai Martaba Yusuf Abubakar Sambo II (Maitaimakin Ciyaman na daya na kungiyar Shuwagabanin kabilu na kasar Nijeriya kuma Sarkin Hausawan Enugu) ya gudanar da taro da kungiyar matasan Garriki a ranar Lahadi 6 ga watan Fabrairu 2022.
Idan dai ba a manta ba a makonnin da s**a gabata ne wasu ‘ya’yan kungiyar s**a gana da shi inda s**a kawo rahoton matsalolin da kungiyar ke fuskanta wajen zaben sabbin shugabannin kungiyar wanda ya haifar da baraka a tsakanin ‘ya’yan kungiyar.
Saboda son hadin kai da ci gaban matasa, Mai Martaba Yusuf Abubakar Sambo II ya sa baki cikin gaggawa don ganin an dawo da zaman lafiya a kungiyar, wanda bayan taruka da shugabannin kungiyar da sauran mambobin kungiyar s**a yi, bangororin sun fito da wanda zai kasance Ciyaman din kungiyar.
Mal Auwal Muhammad wanda shine Sakataren kungiyar a halin yanzu aka zaba ya zama Ciyaman din kungiyar mai jiran gado.
Mai Martaba Yusuf Abubakar Sambo II ya kuma umurci ’ya’yan kungiyar da su je su cike wasu jiga-jigan membobin kungiyar a matsayin sauran guraben Shuwagabanin kungiyar da s**a rage domin kaddamar da su da kuma basu da satifiket.
✍️
Aliyu Adamu kwankwaso
(Mai Magana da yawun Masarautar Hausa ta Jihar Enugu)