
18/01/2024
MUNIR DANKWAMBO FOUNDATION
FREE JAMB REGISTRATION 2024
Thu, Jan 19, 2024
Amadadin Jagoran Gidauniyar Munir Dankwambo Foundation, Wato Alh Munir Dankwambo (Jagaban Tula)
Ina farin cikin sanar da al'umman Jahar Gombe da cewa kamar yanda muka Saba yi a baya,Duk Shekara wannan shekaran ma baza abarmu abaya Chiroman Talban Gombe Alh Munir Dankwambo Ya Amince Da Biyan Kudin Rubuta Jarrabawa na Shiga Makaranta Gaba Da Sakandari wato Jarrabawar Jamb Kyauta Ga Masu Kananan Karfi
Gidauniya ta Saba bada Jamb kyauta ga ma bukata, Idan bamu manta ba a shekaran da ya gabata na 2023 Gidauniyar Munir Dankwambo Foundation Tabiyawa mutum 670 Registration na JAMB kyauta a Fadin Jahar Mu Ta Gombe Dama Kananan Hukumomi .
Wannan Shine Link Din Da Mutum Zaibi Domin Samun wannan tallafi Gashi Nan A Kasa
https://bit.ly/3vIVH4U
Sannan Form Da Komai Da Komai Kyauta Gidauniyar Mu Bata Amince Ga Wani Ko Wata Yabiya sisin kobold domin cike form din mu komai da komai kyauta ne .
REQUIREMENTS
1. Dole me cikawa ya kasance Dan Jahar Gombe ne (Any of the 11 local Governments Indigine).
2. Ya kasance Mai karamin karfi (less privilege).
3. Ya kasance yanada (7 credits including Maths and English).
Mun samar da wayannan gyare-gyaren ne saboda yanda wasu suke wasa da damar idan an basu. Insha Allah wannan karon za'ayi dubi ga asalin mabukata kuma wanda suke da son cigaba da karatun bayan sunyi jarabawan ta JAMB.
Bayan Gama cikawa (Online Registration), Gidauniyan zata saka rananda za'a tantance kowa( Physical Screening) kafun biyawa wanda yaci tantancewan rajistan.
A kula, Gidauniya kowani dan cikinta bazasu bada dama ga kowa ba se wanda yaci screening da za'ayi.
Da wannan muke sanarda Al'umman gari cewa yau zamu bude kofa domin fara cikawa.
Allah ya bada sa'a ya kuma biyawa Jagaban Tula bukatunsa na alkhairi, Ameen.
Signed
Zakariya Abubakar Kumo (chairman munir Dankwambo Foundation)
19/01/2024