12/10/2022
ASSALAMU ALAIKUM MUTANEN GOMBE, KWAMI DA FUNAKAYE.
Muna Gabatar Muku Da Hon Adamu Muhammad Gargajiga (Malam) A Matsayin Dan Takarar Majalisar Tarayya Domin Samun Wakilci Nagari.
Hakika mazabarmu ta Gombe, Kwami, Funakaye idan muka zabi Gargajiga zamu samu wakilci nagari a zauren majalisa.
A shekaru kusan takwas kowa yasan irin yanda wakilcin wannan yanki a majalisar taraiya ya kasance, babu wani da zamuce gashi an cimma sakamakon tura kurma wakilci.
A wasu mazab'u dake jihar nan da s**a samu wakilci mai inganci a majalisar taraiya munga irin cigaba da al'ummar suke samu saboda jajirtattun wakilai da s**a samu wajen shiga duk inda ya dace don samo abubuwan cigaba, sab'anin namu yankin.
Wannan kurman wakilci da muka tura yasa mukayi yunkurin canjawa da nagartacce, idan muka zab'i Hon Gargajiga munada tabbacin samun wakilci nagari da dukkanin aiyukan cigaba ba tareda nuna banbanci ko kabilanci ba.
Hon Adamu Gargajiga tsohon malamin makaranta ne yasan matsalolin al'umma da yanda za'a magance su, musamman mata da matasa, gamida girmama mutane da al'ummar yankin bai daya.
Allah yabamu nasara.