11/06/2020
alimullah Ahmad Hinna
MENE NE YAN MADAKHILA (MURJI'A) SUKE TANTAMA DA
BANKAURA AKAI GAME DA KAFA QUNGIYA?
Ts**akken shirmen furucin su irin ta Manhajin Madakhila
(Murji'a) shine, yawan maimaita cewa mu Yan Qungiya ne
(Hizbiyoun). Rashin sanin Nassoshi da rashin dogon nazari kan
maganganun magabata ke sanya mutum kaji yana wannan irin
furuci ta Jahilci. Wa yace maka don mutum yana Qungiya ya fita
daga Da'irar Sunnah? Matukar Dan qungiya yana kan tafarkin
Sunnah da kiyaye dokokin Allah, ko shakka babu, babu abunda ya
fitar dashi daga Sunnah. Mafi illar dake sanya Qungiya ta zama
abun zargi shine wuce gona da iri wajen nuna Ta'assubanci ko
Guluwwiy kan ita Qungiyyar da zimmar duk wanda bai shiga
Qungiyar ka ba koda yana bin Qur'ani da sunnah sai ka dinga
ganin sa ba akan daidai yake ba, to daga nan kowace irin
Qungiya kake, ko shakka babu ya zama abun zargi da tuhuma
dalilin ta'assubancin da ka nuna, aikata hakan Qungiyanci ne.
Idan kuma nazarin ka bai kai nan ba kai mai yawan ambaton
cewa mu Yan Qugiya ne (Hizbiyyoun) saboda wata son zuciya
irin taka. Ga abunda Allah madaukain sarki yake cewa:
ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦ ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ﻭَﺃُﻭْﻟَﺌِﻚَ ﻫُﻢُ
ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ 104
Fassara:
"A cikin ku a samu wata al'umma wanda zasu ke ƙira ga alkairi
kuma suke umarni da kyakkyawa suna hani daga mummuna,
wadancan sune maus rabauta"
YANDA MALAMAN TAFISIRI S**A FASSARA:
Bari muga manyan Malaman tafsiri me s**a ce game da wannar
Ayah. Ga abunda Ibnu Kathir yake cewa:
ﺍﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ : ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦ ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨﻜَﺮِ ۚ
ﻭَﺃُﻭﻟَٰﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ
ﻭﺍﻟﻤﻘﺼﻮﺩ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻵﻳﺔ ﺃﻥ ﺗﻜﻮﻥ ﻓﺮﻗﺔ ﻣﻦ ﺍﻷﻣﺔ ﻣﺘﺼﺪﻳﺔ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﺸﺄﻥ ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺫﻟﻚ
ﻭﺍﺟﺒﺎ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻓﺮﺩ ﻣﻦ ﺍﻷﻣﺔ ﺑﺤﺴﺒﻪ ، ﻛﻤﺎ ﺛﺒﺖ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻗﺎﻝ
: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : " ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻨﻜﺮﺍ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻩ ﺑﻴﺪﻩ ، ﻓﺈﻥ ﻟﻢ
ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻠﺴﺎﻧﻪ ، ﻓﺈﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻘﻠﺒﻪ ، ﻭﺫﻟﻚ ﺃﺿﻌﻒ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ . " ﻭﻓﻲ ﺭﻭﺍﻳﺔ : "
ﻭﻟﻴﺲ ﻭﺭﺍﺀ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺣﺒﺔ ﺧﺮﺩﻝ " .
Fassara:
"Abunda ake nufi daga wannar Ayar shine, ta kasamce
"QUNGIYA" daga al'ummah tsayayyu domin wannan sha'ani, idan
hakan ya ksance wajibi ne akan kowa mutum da cikin al'ummah
gwargwadon sa, kamar yanda ya tabbata a cikin Sahihu Muslim.
Daga Abu Huraira (Allah ya qara masa yarda), yace: Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi yace: "Duk
wanda yaga abun qi, toh ya chanja shi da hannun sa, idan bazai
iya ba, yayi da harshen sa, idan bazai iya ba, yayi zuciyar sa.
Wannan shine mafi raunin Imani" A cikin wata riwaya ta daban:
Babu abunda ke bayan haka daga Imani daidai da qwayar zarra"
Ga kuma abunda Imam Addabariy yake cewa cikin tafsirin sa:
ﺍﻟﻄﺒﺮﻯ : ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻓﻲ ﺗﺄﻭﻳﻞ ﻗﻮﻟﻪ : ﻭَﻟْﺘَﻜُﻦْ ﻣِﻨْﻜُﻢْ ﺃُﻣَّﺔٌ ﻳَﺪْﻋُﻮﻥَ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟْﺨَﻴْﺮِ ﻭَﻳَﺄْﻣُﺮُﻭﻥَ
ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﻳَﻨْﻬَﻮْﻥَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨْﻜَﺮِ ﻭَﺃُﻭﻟَﺌِﻚَ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ ( 104 )
ﻗﺎﻝ ﺃﺑﻮ ﺟﻌﻔﺮ : ﻳﻌﻨﻲ ﺑﺬﻟﻚ ﺟﻞ ﺛﻨﺎﺅﻩ: " ﻭﻟﺘﻜﻦ ﻣﻨﻜﻢ " ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ "= ﺃﻣﺔ " ، ﻳﻘﻮﻝ:
ﺟﻤﺎﻋﺔ ( 74) "= ﻳﺪﻋﻮﻥ " ﺍﻟﻨﺎﺱ"= ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺨﻴﺮ " ، ﻳﻌﻨﻲ ﺇﻟﻰ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺷﺮﺍﺋﻌﻪ ﺍﻟﺘﻲ
ﺷﺮﻋﻬﺎ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻌﺒﺎﺩﻩ ( 75) "= ﻭﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ " ، ﻳﻘﻮﻝ: ﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﺎﺗﺒﺎﻉ ﻣﺤﻤﺪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺩﻳﻨﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺟﺎﺀ ﺑﻪ ﻣﻦ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ( 76 ) " ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ " ،:
ﻳﻌﻨﻲ ﻭﻳﻨﻬﻮﻥ ﻋﻦ ﺍﻟﻜﻔﺮ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺘﻜﺬﻳﺐ ﺑﻤﺤﻤﺪ ﻭﺑﻤﺎ ﺟﺎﺀ ﺑﻪ ﻣﻦ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ، ﺑﺠﻬﺎﺩﻫﻢ
ﺑﺎﻷﻳﺪﻱ ﻭﺍﻟﺠﻮﺍﺭﺡ، ﺣﺘﻰ ﻳﻨﻘﺎﺩﻭﺍ ﻟﻜﻢ ﺑﺎﻟﻄﺎﻋﺔ .
(74) ﺍﻧﻈﺮ ﺗﻔﺴﻴﺮ" ﺃﻣﺔ" ﻓﻴﻤﺎ ﺳﻠﻒ :1 221 / :3 74 ، 100 ، 128 ، 141 ، 275 -
277.
(75) ﺍﻧﻈﺮ ﺗﻔﺴﻴﺮ" ﺍﻟﺨﻴﺮ " ﻓﻴﻤﺎ ﺳﻠﻒ :2 505 .
(76) ﺍﻧﻈﺮ ﺗﻔﺴﻴﺮ "ﺍﻟﻤﻌﺮﻭﻑ " ﻓﻴﻤﺎ ﺳﻠﻒ :3 293 / 4 : 547 ، 548 / : 5 44 ، 76 ،
93 ، 137 ، 520 .
Fassara:
"Abu Ja'afar yace: Abunda Allah yake nufi da hakan shine: Ya
kasamce wata al'ummah daga cikin ku" Ku muminai wata
al'ummah" yana cewa: Jama'a (Qungiya), suna kiran mutane
zuwa ga alkhairi" yana nufin zuwa ga musulunci da Shari'o'in sa
wadanda Allah ya shar'anta ga bayin sa. "Su dinga umurni da
kyawawa ayyuka" yana nufin su dinga umurtan mutane da bin
Muhammad tsira da amincin Allah sh tabbata gare shi, da
Addinin sa wanda yazo dashi daga Allah. "Su dinga hani da abun
qi" ma'ana: Su dinga hani game da kafurci da Allah da qaryata
Muhammad da abunda yazi dashi daga Allah. Da jihadin su da
hannu da ga66ai har sun zama masu biyayyah"
MATSAYIN YIN QUNGIYA DAGA BAKIN MANYAN MALAMAN
SUNNAH. WA YACE MAKA YIN QUNGIYA LAIFI NE?
Bayan wancar Ayah da bayanin ta ya gabata daga manyan
Malaman tafsiri. Ga kuma abunda Manyan Malamai wanda s**a
gabace mu da wadanda muka yi zamani tare dasu suke cewa.
Shaykhul Islma yana cewa:
ﻳﻘﻮﻝ ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ: " ﻭﺃﻣﺎ [ ﺭﺃﺱ ﺍﻟﺤﺰﺏ ] ﻓﺈﻧﻪ ﺭﺃﺱ ﺍﻟﻄﺎﺋﻔﺔ
ﺍﻟﺘﻲ ﺗﺘﺤﺰﺏ، ﺃﻯ ﺗﺼﻴﺮ ﺣﺰﺑًﺎ، ﻓﺈﻥ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻣﺠﺘﻤﻌﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻣﻦ
ﻏﻴﺮ ﺯﻳﺎﺩﺓ ﻭﻻ ﻧﻘﺼﺎﻥ ﻓﻬﻢ ﻣﺆﻣﻨﻮﻥ، ﻟﻬﻢ ﻣﺎ ﻟﻬﻢ ﻭﻋﻠﻴﻬﻢ ﻣﺎ ﻋﻠﻴﻬﻢ. ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻗﺪ ﺯﺍﺩﻭﺍ
ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻭﻧﻘﺼﻮﺍ ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺘﻌﺼﺐ ﻟﻤﻦ ﺩﺧﻞ ﻓﻲ ﺣﺰﺑﻬﻢ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﺒﺎﻃﻞ، ﻭﺍﻹﻋﺮﺍﺽ ﻋﻤﻦ
ﻟﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﻓﻲ ﺣﺰﺑﻬﻢ، ﺳﻮﺍﺀ ﻛﺎﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﺒﺎﻃﻞ، ﻓﻬﺬﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻔﺮﻕ ﺍﻟﺬﻯ ﺫﻣﻪ ﺍﻟﻠﻪ
ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﺃﻣﺮﺍ ﺑﺎﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻭﺍﻻﺋﺘﻼﻑ، ﻭﻧﻬﻴﺎ ﻋﻦ ﺍﻟﺘﻔﺮﻗﺔ
ﻭﺍﻻﺧﺘﻼﻑ، ﻭﺃﻣﺮﺍ ﺑﺎﻟﺘﻌﺎﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺘﻘﻮﻯ، ﻭﻧﻬﻴﺎ ﻋﻦ ﺍﻟﺘﻌﺎﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﺛﻢ
ﻭﺍﻟﻌﺪﻭﺍﻥ "
( ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ، ﺍﻟﻤﺠﻠﺪ 11 ﺻﻔﺤﺔ 92 ).
Fassara:
"Dangane da Jagorancin Qungiya, jagorancin al'ummah wacce
take gungiyantuwa, ma'ana ta zama wata Qungiya. Idan sun
kasance sun hadu ne kan abunda Allah da Manzon sa s**a yi
umurni dashi ba tare da yin qari ko ragi ba, su muminai ne.
Abunda ke nasu nasu ne, abunda ke kan su yana kansu. Idan ko
sun kasance sunyi qari cikin haka, kuma s**a yi ragi, misalin
Ta'assubanci ga wanda ya shiga Qungiyar su da abunda yake
gaskiya ko na 6ata, da juya baya ga wanda bai shiga Qungiyar su
ba, koda ace mai shi ya kasance akan gaskiya da 6ata. To
wannan shine irin Qumgiyacin da Allah madaukakin sarki ya
kushe shi da Manzon sa. Domin Allah da Manzon sa sunyi
umurni ne da Jama'a da hadin kai, da kuma hani game da
rarrabuwa da sa6ani. Kuma yayi umurni da taimakekeniya akam
nagarta da jin tsoron Allah, da hani kan taimakekeniya kan
zunubi da qiyayyah"
Bayan haka, ga maganar Sheikh Nasiriddeen Albaniy (Allah ya
masa rahama) dake qarfafuwa kan haka:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﻣﺤﻤﺪ ﻧﺎﺻﺮ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ : « ﺃﻱُّ ﺟﻤﻌﻴﺔ ﺗﻘﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﺃﺳﺎﺱٍ ﻣﻦ
ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ، ﺍﻟﻤﺴﺘﻨﺒﻄﺔِ ﺃﺣﻜﺎﻣُﻬﺎ ﻣﻦ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻣﻦ ﺳﻨﺔ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻣﻤﺎ ﻛﺎﻥ
ﻋﻠﻴﻪ ﺳﻠﻔﻨﺎ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ، ﻓﺄﻱُّ ﺟﻤﻌﻴﺔٍ ﺗﻘﻮﻡ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ ﺍﻷﺳﺎﺱ؛ ﻓﻼ ﻣﺠﺎﻝ ﻹﻧﻜﺎﺭﻫﺎ ﻭﺍﺗﻬﺎﻣﻬﺎ
ﺑﺎﻟﺤﺰﺑﻴﺔ؛ ﻷﻥ ﺫﻟﻚ ﻛﻠَّﻪ ﻳﺪﺧﻞ ﻓﻲ ﻋﻤﻮﻡ ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ( ﻭﺗﻌﺎﻭﻧﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺘﻘﻮﻯ)
[ ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ 2:] ، ﻭﺍﻟﺘﻌﺎﻭﻥُ ﺃﻣﺮٌ ﻣﻘﺼﻮﺩ ﺷﺮﻋﺎً، ﻭﻗﺪ ﺗﺨﺘﻠﻒ ﻭﺳﺎﺋﻠﻪ ﻣﻦ ﺯﻣﻦ ﺇﻟﻰ ﺯﻣﻦ، ﻭﻣﻦ
ﻣﻜﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﻣﻜﺎﻥ، ﻭﻣﻦ ﺑﻠﺪﺓ ﺇﻟﻰ ﺃﺧﺮﻯ، ﻭﻟﺬﻟﻚ ﻓﺎﺗﻬﺎﻡُ ﺟﻤﻌﻴﺔٍ ﺗﻘﻮﻡ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ ﺍﻷﺳﺎﺱِ
ﺑﺎﻟﺤﺰﺑﻴﺔِ ﺃﻭ ﺑﺎﻟﺒﺪﻋﻴﺔِ، ﻓﻬﺬﺍ ﻻ ﻣﺠﺎﻝ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﺑﻪ، ﻷﻧﻪ ﻳﺨﺎﻟﻒ ﻣﺎ ﻫﻮ ﻣﻘﺮﺭ ﻋﻨﺪ
ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻖ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﺍﻟﻤﻮﺻﻮﻓﺔ – ﺑﻌﺎﻣﺔ – ﺑﺎﻟﻀﻼﻟﺔ، ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺴُّﻨﺔِ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ
(1) ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ، ﺳﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﺍﻟﻨﻮﺭ، ﺷﺮﻳﻂ ﺭﻗﻢ ( 590 ).
Fassara:
Kowace irin Jam'iyyah (Qungiya) da take tsaye akan ginshiqin na
Musulunci ingantacce, wacce aka ciro (Istimbadi), hukunce
hukucen ta daga littafin Allah (Qur'ani) da Sunnar Manzon Allah,
da abunda magabatan mu na qwarai s**a kasance akai. Duk
Jam'iyyar take tsaye kan wannan Ginshiqi, babu wani zancen a
dinga Inkarin ta da tuhumar ta da Qungiyanci, domin dukkan
hakan yana shiga cikin fadin Allah madaukakin Sarki: (Kuyi
taimakekeniya kan nagarta da jin tsoron Allah). Shiko
taimakekeniya al'amari ne da manufa a Shari'ance. Haqiqa
hakan yana sa6awa isarwar sa daga zamani zuwa zamani, dava
waje zuwa waje, daga gari zuwa ga wani garin. Saboda haka,
tuhumar irin wannan Jam'iyyah (Qungiya) da take tsaye kan
wannan ginshiqi da Qungiyanci ko da Bidi'anci, wannan sam bai
dace da furucin haka ba dashi. Domin ya sa6a da abunda yake
tabbatacce wajen manyan Malamai daga rarrabewa tsakanin
Bidi'a da abunda ake siffantawa, da kuma gamayyar da cewa
6ata ce da tsakanin Sunnah wacce mai kyau.
SHIN AKWAI ALKHAIRI CIKIN ASSASA QUNGIYA?. ME
MALAMAN SUNNAH S**A CE KAN HAKA?!
A cikin tsarin tafiyar da addini musulumci wajen taimakekeniya
tsakanin al'ummah kan abunda yake na nagarta da tsoron Allah
domin cigaban addinin musulumci bisa karantarwan Sunnah,
shine haduwar da babu zargi cikin ta matuqar hadafin su da
manufofin su shine daukaka kalmar Allah da Sunnah ta Manzon
Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi). Wanda hakan
shike halattuwa wajen assasa qungiya domin gudanar da ire iren
wadannan ayyuka na alkhairi. Kamar yanda muka sani, kowace
irin Qungiya tana zama abun zargi ne daga lokaci da aka sanya
Ta'aasubanci da Guluwwiy ko Taqalidanci cikin ta. Haka kuma,
Qungiya takan zama alkhairi da kuma albarka idan ya kasance
manufarta shine kawo cigaban addini da tabbatar da Sunnar
Manzon Allah. Ya za'ayi mu gane haka? Sannan daga bakin wa
ya kamata mu san abunda dake tattare da haka? Ba tareda
munyi nisa ba. Ga abunda Sheikh Abdul'Azeez Bin Baza (Allah ya
masa rahama) yake cewa:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ـ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺠﻤﻌﻴﺎﺕ ﺇﺫﺍ ﻛﺜﺮﺕ ﻓﻲ ﺃﻱ ﺑﻠﺪ ﺇﺳﻼﻣﻲ ﻣﻦ ﺃﺟﻞ
ﺍﻟﺨﻴﺮ ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﻋﺪﺍﺕ ﻭﺍﻟﺘﻌﺎﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺘﻘﻮﻯ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﺩﻭﻥ ﺃﻥ ﺗﺨﺘﻠﻒ ﺃﻫﻮﺍﺀ
ﺃﺻﺤﺎﺑﻬﺎ ﻓﻬﻲ ﺧﻴﺮ ﻭﺑﺮﻛﺔ ﻭﻓﻮﺍﺋﺪﻫﺎ ﻋﻈﻴﻤﺔ، ﺃﻣﺎ ﺇﻥ ﻛﺎﻧﺖ ﻛﻞ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﺗﻀﻠﻞ ﺍﻷﺧﺮﻯ
ﻭﺗﻨﻘﺪ ﺃﻋﻤﺎﻟﻬﺎ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻀﺮﺭ ﺑﻬﺎ ﺣﻴﻨﺌﺬ ﻋﻈﻴﻢ ﻭﺍﻟﻌﻮﺍﻗﺐ ﻭﺧﻴﻤﺔ .
( ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﻭﻣﻘﺎﻻﺕ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ: /4 134 ).
"Idan Jam'iyoyi (Qungiya) s**a yawaita a cikin kowani irin Kasa
ta musulunci ta daga dalilin alkhairi da taimakekeniya, taimako
akan nagarta da jin tsoron Allah tsakanin musulmai, ba tare da ta
sa6a son zuciyar ma'abotan ta ba (Membobi), tana da alkhairi
da albarka da fa'idoji mai girma. Amma idan ta kasance
kowanne tana 6atar da dayan ta tana ware ayyukan ta, toh irin
wannan a daidai wannan lokaci cutar dake cikin ta mai girma ne
uqubar da masaukin ta".
Da wannan zamu iya fahimtar alkhairin dake cikin kafa Qungiya
domin gudanar da ayyukan addini wajen taimakawa juna. Kuma
babu laifi idan sun sanya wami a matsayin shugaba domin
gudanar da tsare tsaren da ya kamata. Hakan ya tabbata daga
abunda Shaykhul Islam Ibn Taymiyyah (Allah ya masa rahama)
yake cewa:
ﻗﺎﻝ ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﻓﻲ ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ:
ﺃﻣﺎ ﻟﻔﻆ ))ﺍﻟﺰﻋﻴﻢ (( ؛ ﻓﺈﻧﻪ ﻣﺜﻞ ﻟﻔﻆ ﺍﻟﻜﻔﻴﻞ ﻭﺍﻟﻘﺒﻴﻞ ﻭﺍﻟﻀﻤﻴﻦ، ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ } : ﻭَﻟِﻤَﻦْ ﺟﺎﺀَ
ﺑِﻪِ ﺣِﻤْﻞُ ﺑَﻌﻴﺮٍ ﻭﺃﻧﺎ ﺑِﻪِ ﺯَﻋﻴﻢٌ { ، ﻓﻤﻦ ﺗﻜﻔﻞ ﺑﺄﻣﺮ ﻃﺎﺋﻔﺔ؛ ﻓﺈﻧﻪ ﻳﻘﺎﻝ: ﻫﻮ ﺯﻋﻴﻢ، ﻓﺈﻥ ﻛﺎﻥ
ﻗﺪ ﺗﻜﻔﻞ ﺑﺨﻴﺮ ﻛﺎﻥ ﻣﺤﻤﻮﺩﺍً ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺷﺮﺍً ﻛﺎﻥ ﻣﺬﻣﻮﻣﺎً ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ .
"Amma lafazin "ZA'EEM" (Shugaba), lallai shi kwatankwacin
dandazon Jama'a ne. Allah madaukain Sarki, Yace: {Kuma
wanda ya zo da shi, yana da kayan rakumi daya, kuma ni ne
lamuni game da shi). Duk wanda aka daura masa nauyin
al'amari na wasu mutane (Qungiya), sai ace shine shugaba. Idan
ya kasance haqiqa ya dauki nauyin da alkhairi, sai ya zama abun
yabawa kan haka. Idan ko ya kasance sharri ne, sai ya zama
abun kushewa da zargi kan haka"
Bayan da Sheikhul Islam ya gama bayyana haka, a qarqashin
wannan shine ya qara da wannan maganar duk wake daya yayi
cikin Fatawa nashi. Domin qara da tabbatar da haka, sai ya
cigaba da cewa:
ﻭﺃﻣﺎ )) ﺭﺃﺱ ﺍﻟﺤﺰﺏ (( ؛ ﻓﺈﻧﻪ ﺭﺃﺱ ﺍﻟﻄﺎﺋﻔﺔ ﺍﻟﺘﻰ ﺗﺘﺤﺰﺏ؛ ﺃﻱ: ﺗﺼﻴﺮ ﺣﺰﺑﺎً، ﻓﺈﻥ ﻛﺎﻧﻮﺍ
ﻣﺠﺘﻤﻌﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺯﻳﺎﺩﺓ ﻭﻻ ﻧﻘﺼﺎﻥ؛ ﻓﻬﻢ ﻣﺆﻣﻨﻮﻥ، ﻟﻬﻢ ﻣﺎ
ﻟﻬﻢ ﻭﻋﻠﻴﻬﻢ ﻣﺎ ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻗﺪ ﺯﺍﺩﻭﺍ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻭﻧﻘﺼﻮﺍ ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺘﻌﺼﺐ ﻟﻤﻦ ﺩﺧﻞ
ﻓﻲ ﺣﺰﺑﻬﻢ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﺒﺎﻃﻞ ﻭﺍﻹﻋﺮﺍﺽ ﻋﻤﻦ ﻟﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﻓﻲ ﺣﺰﺑﻬﻢ، ﺳﻮﺍﺀ ﻛﺎﻥ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﺒﺎﻃﻞ؛ ﻓﻬﺬﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻔﺮﻕ ﺍﻟﺬﻱ ﺫﻣﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﺃﻣﺮﺍ
ﺑﺎﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻭﺍﻻﺋﺘﻼﻑ، ﻭﻧﻬﻴﺎً ﻋﻦ ﺍﻟﺘﻔﺮﻗﺔ ﻭﺍﻻﺧﺘﻼﻑ، ﻭﺃﻣﺮﺍ ﺑﺎﻟﺘﻌﺎﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺘﻘﻮﻯ،
ﻭﻧﻬﻴﺎ ﻋﻦ ﺍﻟﺘﻌﺎﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﺛﻢ ﻭﺍﻟﻌﺪﻭﺍﻥ ) ( 2) .
( 1 ) ﻳﻮﺳﻒ: .72
( 2 ) * )) ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ (( ( / 11 92 )
"Dangane da Jagorancin Qungiya, jagorancin al'ummah wacce
take gungiyantuwa, ma'ana ta zama wata Qungiya. Idan sun
kasance sun hadu ne kan abunda Allah da Manzon sa s**a yi
umurni dashi ba tare da yin qari ko ragi ba, su muminai ne.
Abunda ke nasu nasu ne, abunda ke kan su yana kansu. Idan ko
sun kasance sunyi qari cikin haka, kuma s**a yi ragi, misalin
Ta'assubanci ga wanda ya shiga Qungiyar su da abunda yake
gaskiya ko na 6ata, da juya baya ga wanda bai shiga Qungiyar su
ba, koda ace mai shi ya kasance akan gaskiya da 6ata. To
wannan shine irin Qumgiyacin da Allah madaukakin sarki ya
kushe shi da Manzon sa. Domin Allah da Manzon sa sunyi
umurni ne da Jama'a da hadin kai, da kuma hani game da
rarrabuwa da sa6ani. Kuma yayi umurni da taimakekeniya akam
nagarta da jin tsoron Allah, da hani kan taimakekeniya kan
zunubi da qiyayyah"
Sai Manyan Malaman Sunnah s**e cewa:
ﺃﻣﺎ ﻣﻦ ﺗﺤﺰُّﺏ ﻟﻨﺼﺮﺓ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﻟﺪﻓﺎﻉ ﻋﻨﻪ ﻓﻠﻴﺲ ﺩﺍﺧﻠًﺎ ﻓﻴﻤﻦ ﺫﻣﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺎﻟﺘﻔﺮﻕ
ﻭﺍﻟﺘﺤﺰﺏ، ﻭﺇﻻ ﺳﻮَّﻳﻨﺎ ﺑﻴﻦ ﺟﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺃﻭﻟﻴﺎﺋﻪ، ﻭﺟﻨﻮﺩ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻭﺃﻭﻟﻴﺎﺋﻬﻢ !
ﺍ. ﻫـ ( ﺍﻹﺳﻼﻣﻴﻮﻥ ﻭﺍﻟﻌﻤﻞ ﺍﻟﺴﻴﺎﺳﻲ ﺹ 90 ) .
"Duk wanda s**a yi Qungiya domin taimakon Addini da kariya
gare shi, baya daga cikin wanda Allah ya kushe da rarrabuwa da
Qunguyanci. In ba haka ba zamu daidaita sojojin Allah da
masoyan sa, da kuma sojojin Shaidan da masoyan sa"
Wasun su s**a ce:
ﻭﺍﻟﺮﻣﻲ ﺑﺎﻟﺤﺰﺑﻴﺔ ﺭﻣﻲ ﺑﺎﻟﺒﺎﻃﻞ ﻭﻣﻨﺸﺄﻩ : ﺍﻟﺠﻬﻞ ﺑﻤﻌﻨﻰ ﺍﻟﺤﺰﺑﻴﺔ، ﻓﺄﻱ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ
ﻋﻠﻰ ﻧﺼﺮﺓ ﻣﺒﺪﺃ ﻣﺎ، ﻓﻬﻢ ﺣﺰﺏ، ﻓﺈﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻤﺒﺪﺃ ﺍﻟﺬﻱ ﺍﺟﺘﻤﻌﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﻧﺼﺮﺗﻪ ﺣﻘًﺎ،
ﻓﺤﺰﺑﻴﺘﻬﻢ ﻣﺤﻤﻮﺩﺓ، ﻭﺇﻻ ﻓﺤﺰﺑﻴﺘﻬﻢ ﻣﺬﻣﻮﻣﺔ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ـ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ـ ﻗﺪ ﻣﺪﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ
ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ ﺣﺰﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻘﺎﻝ : ( ﺃُﻭْﻟَﺌِﻚَ ﺣِﺰْﺏُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺃَﻻ ﺇِﻥَّ ﺣِﺰْﺏَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻫُﻢُ ﺍﻟْﻤُﻔْﻠِﺤُﻮﻥَ ) ؛
"Jifan da Qungiyanci da jifar qarya da yada shi: Jahiltar ma'anar
Qungiyamci ne. Duk wata Jama'a da ta hadu akan taimako dake
da manufa, su yan Qungiya ne, idan manufar ya kasance wanda
aka hadu ne akan taimakon gaskiya. Toh Qungiyar su abun
yabawa ne. Idan bai zama haka ba, sai ya zama abun kushewa.
Allah madaukakin Sarki haqiqa yayi yabi cikim Qur'ani ga
Qumhiyar Allah, sai Yace: (Wadancan sune Qimgiyar Allah, ku
saurara kuji, lallai Qungiyar Allah sune masu rabauta)"
Ashe kena zalunci mutum yazo yana jifar wata Qungiya da
kalmar Bidi'ntarwa ba tare da yayi la'akari da irin ayyikan su ba,
da kuma irin abunda suke gudanaewa cikim karantarwar su
saboda wata ra'ayi na hassada ko baqin ciki yake da ita
qungiyar. Domin duk Qungiyar da take bisa hanyar daidai ba tare
da kauce wa karantawar Sunnah, ko shakka babu, abun yabawa
ne.
TA'ASSUBANCI KAN WANI MALAMI BAI TA6A MANHAJIN
SALAF BA, QUNGIYANCI NE:
Tabbatarwar gaskiya ne bisa hanyar dacewa domin warware
shubuhar masu da'awar SALAFIYYAH cikin ta'assubanci da
qoqarin kore alkhairan dayawa daga malamai na Sunnah
wadanda s**a jima suna khidimta wa addinin musulunci bisa
karantawan Kitabu Wassunnah, musamman idan akwai sa6anin
fahimta wanda tasha banban da abun da malamin su ya tafi
akan sa. Galibin su zaka ji suna cewa gorgodon yanda malami
wane ya auna wani malami, suma a hakan zasu auna shi. Kuma
duk hakan ya qunshi yanda shi malami ya auna shi a babin yabo,
ko jarraha shi. Abun tambaya anan shine, shin hakan da suke, ya
dace da karantarwan magabata ko a'a? Shin hakan hada kan
al'ummah ne, ko wargaza kan al'ummah? Bari muga me manyan
Malaman Sunnah S**a ce game da wannan irin ta'assubanci
marar anfani:
ﻗﺎﻝ ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ – ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :-
ﻛﺜﻴﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻳﺨﺒﺮ ﻋﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻔﺮﻕ ﺑﺤﻜﻢ ﺍﻟﻈﻦ ﻭﺍﻟﻬﻮﻯ ﻓﻴﺠﻌﻞ ﻃﺎﺋﻔﺘﻪ ﻭﺍﻟﻤﻨﺘﺴﺒﺔ
ﺇﻟﻰ ﻣﺘﺒﻮﻋﻪ ﺍﻟﻤﻮﺍﻟﻴﺔ ﻟﻪ ﻫﻢ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ؛ ﻭﻳﺠﻌﻞ ﻣﻦ ﺧﺎﻟﻔﻬﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﻫﺬﺍ
ﺿﻼﻝ ﻣﺒﻴﻦ . ﻓﺈﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻻ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﺘﺒﻮﻋﻬﻢ ﺇﻻ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻟﺬﻱ ﻻ ﻳﻨﻄﻖ ﻋﻦ ﺍﻟﻬﻮﻯ ﺇﻥ ﻫﻮ ﺇﻻ ﻭﺣﻲ ﻳﻮﺣﻰ ﻓﻬﻮ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺠﺐ ﺗﺼﺪﻳﻘﻪ ﻓﻲ ﻛﻞ
ﻣﺎ ﺃﺧﺒﺮ ؛
" ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ "
Fassara:
"Shaykhul Islam Ibnu Taymiyyah (Allah ya masa Rahama), Yace:
Dayawa daga mutane, suna labartawa game da wannar Qungiya,
da hukunci na zato da son zuciya, sai su suma sanya gungun
mutane (wata Jama'a), masu dangantuwa zuwa ga bin sa, da
ji6antuwa gare shi, su kuma Ahlssunnah wal Jama'a ne, sai su
sanya duk wanda ya sa6a wa ita Qungiyar tasu cewa ya zama
Dan Bidi'a, wannan 6ata ce mabayyani. Domin lallai su
Ahlusssunah basu da mabiyi face Manzin Allah tsira da amincin
Allah su tabbata gare shi, wamda baya magana bisa son zuciya,
sai idan har wahayi aka masa, shine wanda ya wajaba a gaskata
shi cikin dukkan abunda ya bada labari."
Shaykhul islam bai tsaya nan ba. Ya kuma qara da wannan:
ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ – ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ":- ﻓﻼ ﻳﺠﻮﺯ ﻷﺣﺪ ﺃﻥ ﻳﺠﻌﻞ ﺍﻷﺻﻞ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻟﺸﺨﺺ ﺇﻻ
ﻟﺮﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻻ [ﻟـ ]ﻗﻮﻝ ﺇﻻ ﻟﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ـ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ـ.
ﻭﻣﻦ ﻧﺼﺐ ﺷﺨﺼﺎ ﻛﺎﺋﻨﺎ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻓﻮﺍﻟﻰ ﻭﻋﺎﺩﻯ ﻋﻠﻰ ﻣﻮﺍﻓﻘﺘﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻭﺍﻟﻔﻌﻞ ﻓﻬﻮ
} ﻣﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻓﺮﻗﻮﺍ ﺩﻳﻨﻬﻢ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﺷﻴﻌﺎ { ﺍﻵﻳﺔ ﻭﺇﺫﺍ ﺗﻔﻘﻪ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻭﺗﺄﺩﺏ ﺑﻄﺮﻳﻘﺔ ﻗﻮﻡ ﻣﻦ
ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻣﺜﻞ : ﺍﺗﺒﺎﻉ : ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻭﺍﻟﻤﺸﺎﻳﺦ ؛ ﻓﻠﻴﺲ ﻟﻪ ﺃﻥ ﻳﺠﻌﻞ ﻗﺪﻭﺗﻪ ﻭﺃﺻﺤﺎﺑﻪ ﻫﻢ
ﺍﻟﻌﻴﺎﺭ ﻓﻴﻮﺍﻟﻲ ﻣﻦ ﻭﺍﻓﻘﻬﻢ ﻭﻳﻌﺎﺩﻱ ﻣﻦ ﺧﺎﻟﻔﻬﻢ .
ﻓﻴﻨﺒﻐﻲ ﻟﻺﻧﺴﺎﻥ ﺃﻥ ﻳﻌﻮﺩ ﻧﻔﺴﻪ ﺍﻟﺘﻔﻘﻪ ﺍﻟﺒﺎﻃﻦ ﻓﻲ ﻗﻠﺒﻪ ﻭﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﻪ ﻓﻬﺬﺍ ﺯﺍﺟﺮ .
(10): " ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ 9-8/20)" ).
Fassara:
Ya kuma ce: "Baya halatta ga wani ya sanya asali cikin addini ga
wani mutum face wa Manzon Allah (SAW), ko wani magana face
littafin Allah madaukakin sarki (Qur'ani). Duk wanda ya danganta
wani mutum halittace, wanda yake nuna soyayyah da kuma nuna
qiyayyah kan abunda ya wafaqa cikin magana ko aiki, toh irin
wannan mutumin, {Yana daga cikin wadanda s**a rarraba
addinin su kuma s**a kasance masu 6angarewa} Ayah. Idan
mutumin ya fahimtar, ya kuma ladabtar da wata hanyar mutane
da muminai, Misali: Bin shugabanni da manyan Malamai; toh bai
cancanta ya sanya ikon sa da ma'abotan shi sune s**a fi kowa
ba, har yan dinga nuna soyayyah ga dukkan wanda ya yarda
dasu, da kuma nuna qiyayyah ga dukkan wanda ya sa6a musu.
Saboda haka, abun da yafi dacewa ga mutum shine, ya kimtsa
kansa fahimtar sa 6oyayyah a zuciyar sa da aiki dashi, toh
wannan shine wanda ya wa'azantu"
Saboda haka, babu wani wanda zai zo ya dinga rushe abun da
al'umma suke kai na alkhairi don kawai malamin sa ya sa6a
musu bisa fahimtar sa. Domin aikata hakan, baya daga abunda
magabata na qwarai (SALAF) s**a tafi akan sa. Idan kuma
mutum ya haqiqan ce akan haka, ko shakka babu, ya tabbata
mai tsananin son zuciya da nuna ta'assubanci tsakanin al'umma
masu qoyi kan karantarwan Kitabu. Wassunnah.
Shima wannan kenan a taqaice. Sai a kashi na gaba zamu ga,
shin don malaman sunnah wadanda aka san su, don sun ta6a
yabon wani malami, shike nuna yafi karfin a sa6a masa ko a'a.
Allah ya datar damu bisa hanyar gaskiya
Signed: Motivator & Author Kalimullah Ahmad Hinna
23 hrs · Facebook for Android · Public