22/01/2022
VOICE OF COCIN KWANO
SAƘON ALHINI DA TA'AZIYYA DA KIRA GA GWAMNATI
Amadadin wannan ƙungiya, na amfani da wannan dama ta miƙa saƙon alhini da ta'aziyya ga iyayen wannan yarinya da dukkanin al'umma musulmi.
Wannan ƙungiya tayi Allah waddai da abunda wannan mutumi yayiwa wannan yarinya na rashin imani, Tabbas wannan babban abun baƙincikine ga musulmai da dukkan al'ummar wannan ƙasa tamu.
Wannan ƙungiya na amfani da wannan dama tayi kira ga gwamnatin jahar kano da gwamnatin tarayya da a tabbatar da anyankewa wannan mutumin hukunci dai dai da abunda ya aikata, domin yazama izna ga masu kalar zuciyarshi, damasu tunanin yin kalar wannan abu da yayi.
Allah yajiƙan wannan yarinya, yabawa iyayenta rayayya, dasu damu Allah yabamu haƙurin jure rashinta, Allah yamuna maganin dukkan ɓata gari, Allah yabawa ƙasarmu zaman lafiya mai ɗorewa, Ameen
✍️ VOICE OF COCIN KWANO