27/01/2026
Assalamu Alaikum
Al-ummar Bukkuyum ta kudu Barkar ku da Wannan Lokachi
Ga wani Matashin Dan Siyasa Haziƙi, wanda ya fito takarar Dan Majalisar Dokoki ta Jahar Zamfara a ƙarƙashin tutar jam'iyyar (P.R.P) mai Alamar Makullin Nasara domin wakiltar Al'ummar (Bukkuyum ta Kudu.)
Hon. Jamilu Abdullahi mutun ne dake sun chigaban Al'ummar sa musamman,
•Matasa,
•Mata,
•Tsofaffi
•Marayu,
•Dalibbai,
Da dai sauran Al'umma,
Yana son bayyana ma Al-ummar Bukuyyum ta kudu manufofinsa Wanda za suyi dai-dai da Abinda Al-umma ke buƙata.
√ Kai kudurin samar da makaranta ta gaba da secondary a Karamar hukumar mulki ta Bukuyyum.
√ zai Mike tsaye a zauren Majalisa , ya Kai kuken karanchin Hanyoyi da muke dasu a kauyukkan Bukuyyum.
√ zai tabbatar Cewa matasanmu sunyi Karatu kuma Mun ɗauki Nauyin su har su kammala.
√ Kai kudurin inganta manyan Assibitocin mu da inganta su.
√ zamu Yi Kokari muga Gomnati ta taimaki uwayenmu manoma, ta Hanyar samarda takin zamani, maganin feshi, injinona na ban ruwa tare da iri Mai Kyau da sauran kayan aikin gona na zamani.
√ yayi Alkawarin ba zai bari ayi kasa a guywa ba sai tsaron yanki nai da jaha ya samu, kuma Duk wani taimako da jami'an tsaro ke buqata zamu Basu Chikin gaggawa.
√ matan Aure , Samari zamu koyarda su sana'ar Hannu tare taimaka Masu jari, Matasa kuma Zasu samu ilimi domin dogaro da Kai.
Da sauran Kudurori na chigaba da kuma kokenku da za'a karba da isar dasu tare tabbatar da Cewa bukatun Al-ummar Bukuyyum ta kudu ta biya.
Don haka ne, Hon. Jamilu Abdullahi yake neman goyon bayan ku a wannan zaɓe dake tafe a shekarar (2027) domin kawo abubuwan more rayuwa, chigaba, bunƙasar tattalin arziki, noma, samar da aikin yi, Ilmi, Lafiya, zaman lafiya da dai sauransu.
Saboda haka, yake kira ga Al'ummar wannan yankin da kada ku bari abar ku a baya wajen zaɓen Jam'iyyar (P.R.P) Nasara.
#2027