03/05/2022
Assalamu Alaikum!
Da farko Ina mai godiya ga ALLAH da yasa mukayi sallah lafiya, muna fatan ALLAH ya maimaita mana. kuma inaso nayi amfani da wannan dama domin yin godiya bisa irin gudunmawar da ake bamu.
Bayan dogon lokaci da muka ɗauka muna nazari tare da tuntunɓar mashawaranta da magoya bayanmu, mun samu dama mun kai matsaya game da takarar da muke nema ta majalissar jiha. cikin hukuncin ALLAH mun zaɓi Jamiyar PRP NASARA Domin irin gudunmawar da take bawa matasa a harkokin siyasa.
A bisa hakane, Abokina kuma Amini na sa'annar Mai kula da harkokin takarata Adamu Ahmad Ibrahiim ya cire kudinsa ya siyamin fom ɗin tsayawa takara a ƙarƙashin wannan jamiya tamu ta PRP NASARA. Allah yasaka masa da Alkhairi.
Inaso na sanar daku cewa munfito siyasa ne domin muna ganin akwai gudunmawar da zamu bawa Alumma domin cigaba. Ba mun fito siyasa ne mu ci mutuncin kowa ba, ba munfito muyi mummunar adawa ba, muna zaune lafiya da kowa kuma INSHA ALLAHU zamu ci gaba ta kulla alaqa cikin girmama mutane da kawaici.
Daga Karshe Muna neman adduarku na zaɓin Alkhairi, Idan takararmu Alkhairi ce ga Al'ummar Haɗejia Allah ya tabbatar, Idan kuma ba Alkhairi bane muna fata Allah yayi mana zaɓi na Alkhairi Domin dashi ne muka dogara.
BISSALAM,
NAKU ABBA JAGA
DAN TAKARAR MAJALISSAR JIHA MAI WAKILTAR HAƊEJIA A ZAUREN MAJALISSAR DOKOKIN JIHAR JIGAWA.