10/10/2026
ADC TA KADDAMAR DA KWAMITIN YAKIN NEMAN ZABEN SHUGABAN KASA DON 2027: SABUWAR SAFIYA TA KETO
Abuja, 9 ga Oktoba, 2026 – Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na 2027 a jiya Juma'a a dakin taro na Shehu Musa Yar'Adua Centre, Abuja.
Taron ya gudana karkashin jagorancin Shugaban Jam'iyyar na kasa, SENATOR DAVID MARK, tare da Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zabe, ALHAJI KASHIM IBRAHIM-IMAN, da Daraktan Yakin Neman Zabe, SENATOR AUSTIN AKOBUNDU.
Dan takarar Shugaban Kasa na jam'iyyar, ALHAJI ATIKU ABUBAKAR, shi ne ya dauki hankalin kowa da jawabin da yayi akan halin da kasar ke ciki.
Atiku ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ta gaza.
"Tinubu ya samu shekaru uku da rabi domin ya inganta rayuwarmu. Me ya bamu? Buhun abinci da kullum farashinsa ke karuwa a kasuwa. Kudin mota zuwa aiki da ke cinye albashi. Sana'a ko Gona da muke tsoron zuwa saboda tsaro. Wannan shine mummunan tarihin da yake so 'yan Najeriya su tafa masa,” in ji Atiku.
Ya kara da cewa rangwamen kudin fetur na kwana 30 da gwamnati ta sanar, wulakanci ne ga 'yan Najeriya. Ya ce,
“Rangwamen fetur na kwana 30 ba zai goge wahalar shekaru uku da rabi ba. Tinubu ne ya sa rayuwa tayi tsada, ni kuma zan mayar da ita mai sauki.”
Daraktan Yakin Neman Zabe, Sanata Akobundu, ya bayyana shirin ADC na ceto kasa, wanda ya hada da rage kudin hada fetur a cikin gida domin farashin mai ya fadi, gyara wutar lantarki, ilimi, lafiya da noma, da kuma duba bashin dalibai na NELFUND.
Shugaban Kwamitin, Kashim Ibrahim-Imam, ya kalubalanci magoya baya da su shirya tsare kuri'unsu, yana mai cewa,
“Dole ne Tinubu ya tafi! Ku fita da sassafe, ku tsare kuri'unku da idanunku, ba da hannuwanku ba. Taron jama'a miliyoyin da suke cikin lumana, ba a iya musu magudi ba.”