05/02/2025
A Madadin 'Ya'yan wannan kungiya mai suna a sama da Alummar wannan gari namu mai Albarka.
Muna taya mutane uku na garin Jikamshi murnar samun aikin Fire service a Federal government a karkashin jagorancin Mai girma Dan majalissar tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed Musawa Dujiman katsina.
1- Muhammad Ibrahim Jikamshi
2- Zaidu Garba Tela Jikamshi
3- Nura Yusuf Jikamshi
Muna tayasu Addu'ar Allah ubangiji ya basu ikon sauke wannan nauhi lafiya Allah ya basu ikon ciyar da Alumma gaba da taimakon musulunci da musulmai.
Daga karshe muna Masu fatan alkhairi da fatan zasu rike Aikin su cikin gaskiya da rikon Amana da jajircewa wajan yin aiki ta kuru domin tabbatar da cigaban gari da karamar Hukumar mu da jaharmu da kasa baki daya.
Mai girma DUJIMAN KATSINA irin wannan Aikin alherin ba yau kasoma ba mun Saba ganinshi, muna maka Addu'ar Allah ubangiji ya cigaba da Baka dama da ikon cigaba da taimakon Alumma kamar yadda kasaba.
Allah ya shiga lamuranka ya iya maka duk abunda baka iyawa alfarmar Annabi da Alqura'ni Amin 🤲
✍️
05/02/2025