01/06/2026
Sakon Ta’aziyya
Ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalan Ahmed Laushi bisa rasuwar mahaifinsu, wani jigo kuma mai taimakon al’umma. Wannan rashi ba na iyalansa kaɗai ba ne, rashi ne ga Arewacin Najeriya baki ɗaya saboda irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban jama’a.
Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa da al’ummar da ya bari haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.
– Hon. Ahmed Tijjani Nakande