11/09/2025
SANARWA GA MANEMA LABARAI
Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓe ta Hon. Esther Ashivelli Dawaki ta yi tir da ƙarfi, game da wulakanci, tsoratarwa da kuma k**a ba bisa ƙa’ida ba da aka yi wa ‘yar takarmu, Hon. Esther Ashivelli Dawaki, tare da Daraktan Janar ɗin Yaƙin Neman Zaɓenta, Hon. Fatange, a yayin zaɓen cike gurbi na Chikun/Kajuru Federal Constituency da aka kammala kwanan nan.
Abin da ya faru ba komai ba ne face aikin mugunta da aka tsara tun daga farko—ƙoƙarin kwace musu mutunci, rage su a matsayin ɗan adam, da kuma ƙoƙarin dakile jarumtarsu. Tilasta mace mai daraja da kuma DG ɗinta su riƙe allon EFCC ta hanyar tilastawa don wulakantarsu a bainar jama’a, ba wai kawai cin mutunci bane, illa kuma wata alama ce ta rashin imani da zaluncin siyasa. Wannan wulakantacciyar dabi’a ita ce ainihin ma’anar mugunta, wadda aka aiwatar don karya ƙarfin zuciya da kuma rage musu sha’awar yi wa al’umma hidima.
Ba za mu iya yin shiru ba kan mummunan sakon da wannan abu ya ƙunsa. Wannan zalunci da aka yi wa Hon. Esther Ashivelli Dawaki da Hon. Fatange ba wai kai tsaye ne ga mutum biyu kawai ba, illa kuwa hari ne kan mata, kan shugabanci da kuma kan dimokuraɗiyya baki ɗaya. Wani saƙo ne mai bayyana cewa wannan gwamnati (daga tarayya wajen Natasha, zuwa jiha a Kaduna) gwamnati ce ta masu ƙin ganin mata suna tasowa a matsayin shugabanni masu ƙarfin murya. Ta hanyar tattake musu mutunci, wannan gwamnati ta sake bayyana tsantsar raini da rashin mutuntawa ga duk wata mace da ta ƙuduri aniyar tsayawa kai da fata wajen faɗar gaskiya da kalubalantar tsarin zalunci.
Mun samu tabbaci kai tsaye daga wani babban jami’in EFCC cewa wallafa wannan hoton wulakanci ba shi ne manufar hukumar tun farko ba. A zahiri, jami’ai da dama a cikin EFCC sun nuna ɓacin rai da nadama kan irin wannan kunyar da aka jefa mata.
Yanzu dai ya bayyana a fili cewa wannan aiki ne na wasu mutane masu son zuciya, waɗanda s**a shirya wannan aikin shaidanci da zalunci domin bata mata suna da kuma tilastawa wasu su shiga cikin ƙarya. Wannan aiki nasu ba komai ba ne face alamar tsananin tsoro da rashin imani a siyasa.
Saboda haka, muna aikawa da ƙarfi tir da Allah wadai ga gwamnatin APC a Jihar Kaduna ƙarƙashin Gwamna Uba Sani, saboda amfani da hukumomin tsaro (DSS, ‘Yan Sanda da EFCC)—waɗanda aka kafa domin kare jama’a—a matsayin kayan aiki na tsoratarwa da k**a ba bisa ƙa’ida ba. Wannan wulakantaccen amfani da iko domin cin zarafi da zaluntar abokan hamayya na siyasa shi ne ainihin alamar mulkin k**a karya. Ku sani, duk yadda s**a yi nisa wajen aikata mugunta, iko na da iyaka. Wadanda s**a yi amfani da shi ba da gaskiya ba, wata rana lallai za su bada hisabi.
Muna kira ga jama’ar Kaduna State, musamman mazauna Chikun/Kajuru Federal Constituency: ku taso ku yi magana. Dimokuraɗiyya tana mutuwa a cikin shiru, kuma ba za mu iya yi wa wannan mugunta shiru ba. Sauyin gwamnati zuwa mulkin k**a karya dole ne mu ƙi shi da baki ɗaya, domin ciwon ɗaya ya zama ciwon kowa. Kada ku ji tsoro—mur’yarku ita ce ƙarfin ku, kuma jarumtakun ku shi ne garkuwar mu.
Ku tabbatar da wannan: komai tsawon dare, wayewar gari lallai zata zo. Mun riga mun shaida irin waɗannan lokuta a tarihinmu—lokutan da gwamnati ta yi tunanin za ta iya murƙushe murya da ƙarfin jama’a. Duk sun wuce, jama’a kuma sun yi nasara. Wannan lokacin zalunci ma zai wuce, mu kuma za mu fito da ƙarfi, da haɗin kai, da ƙarfin zuciya.
An sanya hannu,
Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaɓe ta Hon. Esther Ashivelli Dawaki
Ɗan takarar PDP, Chikun/Kajuru Federal Constituency Bye-election
Ezekiel Jagaba Tanuna Stainless Timothy Shekoduza Dalhatu Waziri Idris Ibrahim Sadiq S Madaki Aliyu Ismail Bwans Omoh Abdulla Zulaihat Alberah Catoh Sen Lawal Adamu Usman