11/07/2024
MATSAYIN ZANGA-ZANGA A MUSULMI..(01)
Duk wanda ya kalli zanga-zanga da bore ga mahukunta da idon basira da hangen nesa, zai iya fahimtar cewa ababe ne waɗanda suke ƙunshe da saɓawa shari'a ta fuskoki da dama.
Zan tsakura maka kaɗan daga cikin waɗannan fuskoki ga abinda ya bayyana a gare ni
1️⃣ Waɗannan abubuwa ba su da tushe a cikin Alkur’ani, ko Sunnah, ko aikin magabata, haka kuma maganganun manyan malamai kafaffu a ilimi, saidai ma sun bayar da fatawa ta haramci ga zanga-zanga da duk wani nau'i na taratsi da bore ga mahukunta.
Kada ka manta mai karatu, malamai nace gogaggu kafaffu a ilimi ❗
2️⃣ Zanga-zanga ta saɓawa nassoshi waɗanda s**a zo game da umarni wajen hakuri da zaluncin mahukunta, da addu’a da maida lamari zuwa ga Allah.
3️⃣ Zanga-zanga ta saɓawa tsarin shari’a game da nasiha ga masu mulki, kamar yadda duk masu karatu s**a sani.
4️⃣ Abune sananne cewa a mafi yawan a mafi yawan lokuta zanga-zanga tana ƙunshe da la'antar masu mulki da keta alfarmarsu, kuma wannan ba ya taɓa zama hanyar canza ɓarna, da ma kuma akwai nassoshin shari'a masu yawa cikin haramci game da hakan.
5️⃣ Zanga-zanga kafa ce dake ɓullewa zuwa ga aikata zunubai masu yawa, kamar : bayyana tsiraici, cakuɗuwar maza da mata, iface-iface, fashe-fashe, ƙone-ƙone da sauransu, waɗanda basu daga cikin tarbiyyar musulunci da al'ummar musulmi.
6️⃣ Wani lokaci zanga-zanga tana sabbaba daidaito tsakanin Musulunci da kafirci, ta fuskar cakuɗewa da tarayya a cikin aiki ɗaya tsakanin musulmai da sauran maz'habobin ƙarya masu da'awar musulunci, dama sauran addinai mabanbanta.
Irin wannan tarayya bata daga cikin tarbiyyar da musulunci ya lamuncewa musulmi ya haɗa kai da kafirai wajen samar da ita ❗
7️⃣ Zanga-zanga ta kan haifar da munanan ayyuka, kamar : zubar da jini, almubazzaranci da kuɗi, yaɗa hargitsi, da dai sauransu; ga kuma rashin cimma abubuwan da ake buƙata a mafi yawan lokuta.
8️⃣ Zanga-zanga da bore ga mahukunta su ne mafara na amfani da makami ga masu mulki, wanda nassoshi s**a yawaita cikin hani game da hakan.
Babu shakka zanga-zanga hanya ce da ke kaiwa zuwa ga khawarijanci(boko haram), domin mutane sunada mabanbantan manufofi a cikin zukatansu, sai kuma zanga-zanga ta share masu fage na bayyana manufofinsu❗
9️⃣ Idan zanga-zanga ta yamutsa lamari ta kuma tsananta, sai ta kai ga shigowar kafircin kasashen waje a kasashen musulmi.
Wannan kuma abu ne da duk mai madaidaici hankali zai iya fahimta, ballantana mai zurfin nazari ko kuma masani a fagen ilimin rayuwa da addini ❗
🔟 Abin takaici ma shine: zanga-zanga asali ne tabbatacce a cikin mulkin demokradiyya, wanda ya samar da dama ga duk wani ɗan ƙasa ya faɗi albarkacin bakinsa, kuma yayi tutsu da zanga-zanga game da abinda yake ganin bai masa ba❗
Ko shakka babu wannan dabi’a ba ta dace da Musulunci ba, kuma wannan ƙa’idar ta saɓawa ƙa’idojin Musulunci, don haka babu wani hukunci sai abinda shari'a ta yanke, kuma baya halatta ga wani ya shar'anta wanin ta, don haka duk wanda ya yi da'awar cewa zai iya saɓawa hakan, ko kuma yana ganin hukuncinta bai tabbata ba, ko kuma bai dace da zamani ba; wannan kuma babu shakka ya afka kan tafarkin halaka.
Allah Ya tsaremu Ya tsare mana imaninmu da addininmu🤲🏻
Abul-Mustapha Al-athary
08037894111
5/1/1446🔁11/7/2024