20/04/2023
Kafin Kayi aure a wannan loƙaci Ya k**ata kasan da wannan ..
Kwanon Shinkafa ƴar Hausa Naira 1800 Ne Gwangwani Man gyaɗa 250 Maggi ɗaya Naira 10 Biredi Wanda Mutum biyu zasu iya Ci Naira 250 Taliya 450 ..
Sabulun Wanka 200 Na Wanki 200 Kuɗin Ruwa Jarka ɗaya naira 50 a ƙalla ka sayi jarka biyu kullum naira ɗari..
Sai Ka Buga a sati ɗaya Kai da amarya da ƴan ƙannen amarya masu kawo ziyara zaku iya lashe Kwano Huɗu na shinkafa Kuɗinta Zai K**a naira 1850 ×4 Zai k**a Naira 7400..
Biredi 250 a ƙalla ku siya sau biyar a sati Kuɗinka Zai K**a 1250..
Taliya a ƙalla ka sayi Guda Uku a satinnan kuɗinka zai k**a 1350..
Kuɗin Ruwan sha na wanki dana wanka a ƙalla jarka biyu a rana naira ɗari sau 7 ya k**a ɗari bakwai a sati..
Sabulun wanka da na wanki ,Maggi , Kayan Miya, Gas ko gawayi , Man girki Kuɗinsu zai K**a Naira 6000 A sati..
Shinkafar Sati Ɗaya - 7400
Biredi na Sati Ɗaya- 1250
Taliyar Sati Ɗaya-1350
Kuɗin Ruwa-700
Su kayan miya da sabulun wanka da wanki, gawayi ko Gas , Man girki -6000
Total ɗin Sati ɗaya duka- 16,700
Total ɗin wata ɗaya-66,800
Wannan lissafi kada ka manta ba'a saka wasu abubuwa ba da yawa k**ar kuɗin magani na rashin lafiya, kuɗin kayan kwalliya, auduga ta mata yayin Al'ada, Kuɗin taransifot na zuwa wajen aiki ko kasuwa na maigida, Ƴar madara ta watsawa a shayi, ɗan naman miya, gasu nan dai birjik..
Shi yasa Muke gayawa samari da babbar Murya idan baka samun a ƙalla dubu hamsin a wata ka haƙura da aure kaga dai lissafin dubu sittin ma tayi kaɗan, wannan kuma shine ƙarshen lissafi wanda ba kowacce mace ce zata iya yadda ta zauna a haka ba...
Nayi Nan 🚶🚶
Adam Husaini Abubakar