27/03/2026
Yau muke cika kwanaki bakwai na Sallah. Muna Godiya ga Allah ﷻ da ya rayamu cikin ƙoshin lafiya.
Sallah ya wuce, Allah ya maimaita mana, Ameen.
MATASA - idan kun samu dama kuyi Aure, lallai ku sani akwai alkhairi mai ɗumbin yawa a cikin Aure.
Wato duk yadda za'ayi maka bayanin alkhairin dake cikin Aure, ba za ka fahimta ba, sai kayi Auran. Sai dai ayi don Allah, kada ayi don magance sha'awa ko dan neman tara abin duniya ga masu Auran Jari kenan, domin akwai da yawa waɗanda suke Aure ba don Allah ba, ba domin sun yarda suyi Auran don Ibada ne ba. Lallai ka sani, ki sani, idan har za kuyi Aure ba don Allah ba, to babu shakka ba za kuga alkhairin dake tattare da Auran ba, kuma daɗin da za kuji na ɗan lokaci ne, takaici zai biyo baya. Sai dai kuma ku sani, akwai jarabawa da ƙalubale a cikin Aure, amma idan akai haƙuri aka jure, tabbas za aga sakamako na alkhairi mai tarin yawa.
Ina amfani da wannan dama in sake gode wa dukkan waɗanda s**a taka rawar gani wajen ganin Auran mu ya kasance. Tun daga ɓangaren Iyaye da Ƴan'uwa da Abokai da Iyayen gida na Siyasa. Allah ta'alah ya saka ma kowa da alkhairi. Nagode!
Matata JAMILA - Allah yai miki Albarka, Allah ya ƙara mana zaman lafiya da haƙuri da fahimtar juna, Allah ya barmu tare ya bamu zuri'a masu Albarka, alfarmar Shugaba ﷺ Ameen thumma Ameen.