26/01/2026
BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KADUNA
VOL 1
Sanata Uba Sani, CON
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,
Mai Girma Gwamna, muna miƙa gaisuwa ta musamman tare da fatan alheri, zaman lafiya, da ƙara samun nasara a jagorancinka mai cike da hangen nesa, adalci, da kishin al’umma. Lallai shugabancinka ya kawo sabuwar fata da kwarin gwiwa ga al’ummar Jihar Kaduna, musamman ma yankunan karkara da aka dade ana kallon su a baya.
Mai Girma Gwamna, wannan rubutu na zuwa gare ka ne domin bayyana ra’ayi, fata, da kuma muradin al’ummar Ikara da Kubau Federal Constituency, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci na shirin siyasa. Rubutun na nufin bayyana gaskiya da adalci dangane da kujerrar Wakilin Tarayya (House of Representatives) ta Ikara/Kubau, wacce a fili take nuna cewa lokacin Ikara ne, kuma akwai mutum guda da ya fi kowa cancanta da ya dace a goya masa baya—Hon. Dr. Hamza Ibrahim Ikara.
IKARA DA KUBAU: TARIHI, ADALCI, DA JUYIN JUYA HALI
Mai Girma Gwamna, Ikara da Kubau ba sabbin yankuna ba ne a siyasar Jihar Kaduna da ta ƙasa baki ɗaya. Yankuna ne masu tarihi, mutunci, da rawar da s**a taka a siyasa, ilimi, kasuwanci, da zaman lafiya. Duk da haka, idan aka yi la’akari da tsarin raba dama da wakilci, Ikara ta dade tana haƙuri, tana jiran lokacinta cikin biyayya da biyayyar jam’iyya.
A siyasa, adalci shi ne ginshiƙi. Idan aka ce lokaci ya yi na wani yanki ya wakilci jama’a, hakan yana ƙarfafa haɗin kai, kwanciyar hankali, da amincewa da shugabanci. A yau, babu shakka cewa lokacin Ikara ya yi na riƙe wannan kujera domin a cika tsarin daidaito da gaskiya.
DALILIN DA YA SA IKARA TA CANCANTA A YANZU
1. Haƙuri da biyayya – Ikara ta nuna ladabi da biyayya ga jam’iyya da shugabanci a tsawon lokaci.
2. Gudummawa ga nasarar APC – A kowane zaɓe, Ikara na daga cikin yankunan da s**a tsaya tsayin daka wajen ba APC ƙuri’u