Radio Nigeria Kaduna

Radio Nigeria Kaduna Wannan kafa ce da aka buɗe domin yaɗa labarai da wayar da kan jama'a a kan abubuwan da suke faruwa a Nig.
(2)

04/09/2026
Hukumar Alhazan Jihar Jigawa Ta Nemi Hadin Kan Rundunar 'Yan SandaDaga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta...
04/09/2026

Hukumar Alhazan Jihar Jigawa Ta Nemi Hadin Kan Rundunar 'Yan Sanda

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta nemi ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya domin inganta tsaro da tabbatar da lafiyar Alhazai a lokacin aikin Hajji.

Shugaban Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci tawaga zuwa ziyarar ban-girma ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa a Dutse.

Labbo ya ce ziyarar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumar da ’yan sanda, musamman wajen tsara tsaro, sadarwa, musayar bayanai da haɗin gwiwa tsakanin hukumomi.

Ya jaddada muhimmancin samar da ingantaccen tsaro domin kare alhazai, jami’an hukumar da sauran masu ruwa da tsaki a duk tsawon aikin Hajjin.

Daraktan Janar ya kuma gode wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Tijjani Murtala, bisa karɓar tawagar da kuma irin goyon bayan da rundunar ke bai wa hukumar a kai a kai.

A nasa jawabin, CP Tijjani Murtala ya yaba wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai bisa rawar da take takawa wajen kula da jin daɗin alhazai da gudanar da ayyukan ibadarsu.

Ya tabbatar wa tawagar cewa rundunar za ta ci gaba da haɗa kai da hukumar da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da tsaro da lafiyar alhazai da jami’an da ke tare da su.

Kwamishinan ya ce rundunar ’yan sanda ta himmatu wajen samar da ingantaccen tsaro cikin ƙwarewa, saurin amsa buƙata da kuma amfani da bayanan sirri.

Ya kuma jaddada muhimmancin fara shirye-shiryen tsaro tun da wuri, musayar bayanai cikin lokaci da kuma haɗa kai tsakanin hukumomin da abin ya shafa domin samun aikin Hajji mai sauƙi, aminci da nasara.

TUC Passes Vote Of Confidence In Uba Sani, Appeals For Reinstatement Of 83 Sacked Workers
04/09/2026

TUC Passes Vote Of Confidence In Uba Sani, Appeals For Reinstatement Of 83 Sacked Workers

  By Adamu Yusuf The Trade Union Congress of Nigeria (TUC), Kaduna…

Thanks for being a top engager and making it on to our weekly engagement list! 🎉 Yohanna James, Tajuddeen Shu'aib, Ahmed...
04/09/2026

Thanks for being a top engager and making it on to our weekly engagement list! 🎉 Yohanna James, Tajuddeen Shu'aib, Ahmed Jamil, Ada'Ila M Salisu, Abubakar Idris Lamara, Shafiu Mai Iyali, Umar Nuhu, Abdulrahaman Garba, Usman Aliyu, Anas Ahmad, Shehu Bako Abdullahi, Yasir Salisu Yasir Salisu, Usama Auwalu, Abubakar Ahmad Nayaya, Ibrahim Sunusi, Shamsuddeen Abdulmaleek, Umar Mukhtar, Auwalu Salisu, Sufi Dalhatu, Naziru Alhasan, Mohammed Maaruf, Abokin Masoya Adam, Muntari Aliyu Rogo, Kentafiya Dawowa, Kabiru Malami, Muhammad Ibrahim Machudo, Umar Aliyu, GwaNi Jnr, Suraja Musa Idris, Shamsuddeen Mannir Atiku, Abba Sidi, A Jalal Yakubu, Alhassan Ismail Ibrahim, Kasimu Gitta, Kabiru Ahmad Sufi, Salihu Adam Saminaka, Abas Abba, Abbas Muhammad Zaria, Idrismd Idris, Abdulhakeem Musa, Zanna Maiyeri, Abba Zakariyya Muhammad, Labaran Karkara Da Burane, Bello Ahmad Adamu, Danmadamin Kauran Katsina Danmadami, Baban Hajiya, Buhari Ummar Abbas, Ismaila Yusuf Abdalla, Surajo Tijjani, Ibrahim Umar Kangiwa Ibrahim

Jigawa Pilgrims Board Seeks Police Collaboration For Hajj Security
04/09/2026

Jigawa Pilgrims Board Seeks Police Collaboration For Hajj Security

By Usman Muhammed Zaria Jigawa State Pilgrims Welfare Board has sought stronger…

Jigawa Govt Mourns Emir of Gumel, Ahmed Muhammad Sani
04/09/2026

Jigawa Govt Mourns Emir of Gumel, Ahmed Muhammad Sani

By Usman Muhammed Zaria Jigawa State Government has expressed regret over the…

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Sarkin GumelDaga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana alhinin r...
03/09/2026

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Sarkin Gumel

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana alhinin rasuwar Sarkin Gumel, Mai Martaba Alhaji Ahmed Muhammad Sani, wanda ya rasu yana da shekaru 84 a birnin Alkahira na ƙasar Masar, bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai. Ya ce marigayi Sarkin ya hau karagar mulki a shekarar 1980, inda ya shafe shekaru 46 yana yi wa al’ummarsa hidima.

Malam Bala ya bayyana Sarkin Gumel na 16 a matsayin sarki mai hikima da hangen nesa, wanda ya bayar da gudunmawa wajen inganta harkokin lafiya, ƙara yawan yara masu zuwa makaranta, da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Gwamnatin jihar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, al’ummar Masarautar Gumel, Majalisar Sarakunan Jihar da daukacin al’ummar Jigawa, tana mai cewa za a yi matuƙar kewar gudunmawar da ya bayar ga ci gaban al’umma.

Masarautar ta Gumel za ta sanar da lokacin jana’izar Marigayin kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.

Ta kuma roƙi Allah SWT Ya gafarta wa marigayin, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya kuma sa Aljannatul Firdaus ce makomarsa.

Nigerian Navy Inaugurates Solar Powered  Borehole at Gombe Cottage Hospital
03/09/2026

Nigerian Navy Inaugurates Solar Powered Borehole at Gombe Cottage Hospital

By Hudu Shehu.     The Nigerian Navy has inaugurated a newly…

Gwamnatin Jigawa Ta Dakatar Da Shugaban Babbar Makarantar Sakandare Da Ke DutseDaga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar...
03/09/2026

Gwamnatin Jigawa Ta Dakatar Da Shugaban Babbar Makarantar Sakandare Da Ke Dutse

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta dakatar da Daraktan Babbar Makarantar Sakandare da ke Dutse, Malam Abdullahi Shehu, saboda zargin sakaci da aiki.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi, Kimiyya da Fasaha, Abdullahi Yakubu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse.

Ya ce an dakatar da daraktan ne bayan wata ziyarar ba-zata da ma’aikatar ta kai makarantar domin duba yadda ake gudanar da harkokin makarantar.

A cewarsa, matakin ya biyo bayan sakacin da aka gano wajen gudanar da ayyukan makarantar, lamarin da ma’aikatar ta ce abin takaici ne, musamman ganin irin tallafin da gwamnati ke bai wa bangaren ilimi.

Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi, Kimiyya da Fasaha, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ya nuna damuwa kan yadda shugabancin makarantar ba ya gudana yadda ya kamata. Ya kuma umarci Daraktan Kula da Ayyukan Makarantu, Mustapha Abdullahi Ringim, da ya binciki batun rashin halartar malamai domin daukar matakin da ya dace.

Kwamishinan ya kuma duba ayyukan gyaran ajujuwa da dakunan kwanan dalibai a Makarantar Dutse Model International, da kuma aikin gina wurin koyar da sana'o'i.

Daga nan ya ziyarci Makarantar Larabci da Ilimin Addinin Musulunci ta Fatara da ke Dutse, inda ya duba ayyukan gyaran makarantar tare da umartar shugabanta da ya inganta ayyukan makarantar domin samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa.

Kaduna Government Inaugurates Four Agency Boards, Tasks Members On Reforms, Transparency
03/09/2026

Kaduna Government Inaugurates Four Agency Boards, Tasks Members On Reforms, Transparency

  By Adamu Yusuf   The Kaduna State Government has inaugurated the…

Address

No. 7 Yakubu Gowon Way
Kaduna
800238

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Radio Nigeria Kaduna posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Radio Nigeria Kaduna:

Shortcuts

Share