20/08/2022
Shehu ABG: Mafarauta Sun Yi Sake..
Daga Bello Ahmadu Alkammawa
Zancen da yafi daukar hankalin ‘yansiyasar Najeriya shi ne yadda hadarin siyasar Gidan Arewa watau Jihar Kaduna ya canza kwana nan sak**akon yadda wasu masu fada aji a cikin Jam’iyyun dake da gatar kasancewa sahun gaba a cikin lamuran siyasar jihar s**a sauya sheka zuwa sabuwar Jam’iyyar NNPP da rana tsaka ido na ganin ido.
Cikin wadanda s**a canza sheka zuwa NNPP har da Dan Marayen Zaki, kuma madubin siyasar talakawan Najeriya, tun kafin sojojin su fara shirye shiryen komawa barikokin a daidai lokacin da ake nakudar haihuwar Jam’iyyun APP da PDP, Alhaji Usman Shehu Garba wanda aka fi sani da ABG, komawarsa wannan jam’iyya ya kawo rashin tabbas a Jam’iyyar PDP da ita kanta APC saboda tun daga lokacin da ya yi wannan namijin kokarin, magoya bayansa da kuma wasu da s**a gane ma’anar dalilin ficewarsa, su kansu sun jefar da kwallon mangwaro sun kuma huta da kudaje. Wannan lamari ne ya sanya masu kula da lamuran yau da kullum ke ganin zaben da zai fi daukar hankalin ‘yansiyasa a lokacin babban zabe na 2023 shi ne zaben wanda zai kasance Wakilin Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa a Majalisar Wakilai Ta Kasa. A yanzu dai dukkanin Jam’iyyun dake kasarnan musamman APC da PRP da PDP da NNPP ne ake ganin za su fafata domin kasancewa akan kujerar, hankalin mutane da dama na ganin takarar za a yi ta tsakanin NNPP da PDP, saboda yadda Jam’iyyar da ake yiwa lakabi da Mai Kayan Marmari ke dada samun karbuwa ga mutane, alherin da soyayyar da girmama mutane manya da kananna tare da tallafin ga marasa galihu da aka san ABG da su shi ne ake ganin ya sanya ‘yansiyasa a jihar su ke kwarara zuwa NNPP domin kaucewa mulkin k**a karya da aka dade ana yi masu a APC da kuma PDP, wadda wasu ke ganinta tamkar jam’iyyar da ba ta da alkibla, tun bayan fitowar wani faifan bidiyon da ya nuna wani madugunta yana tattaunawa da jigon Jam’iyyar APC kuma dantakarar mukamin gwamna.
Sunan Alhaji Usman Garba watau ABG ba boyayye ba ne, tun kafin ya shiga siyasa zuwa lokacin da yake cikin tafiyar Jam’iyyar CPC wadda itace tayi masa zagin zuwa Majalisar Wakilai ta Kasa a can baya, irin nagartattun ayyuka da namijin kokarinsa a bangarorin bunkasa rayuwar mutanen Najeriya, ya sanya shi kasancewa bangon da talakawa ke jingina domin bunkasa rayuwar su saboda haka bayan CPC ta zama tarihi, amalin ya shiga Jam’iyyar PDP domin ganin ko ba domin ya yi takara ba, ya ci gaba da aiwatar da ayyukan jikai ga mutane ganin irin wannan ayyuka ne ya samu ana yi a gidan su, saboda haka yake kokarin ganin ya ci gaba da aiwatar da su domin ganin yana tafiya tare da kyakkyawan tarihin ci gaban al’umma. Tunda Malam Bahaushe ya ce ‘Barewa Ba Ta Yin Gudu ‘Ya’Yanta Su Yi Rarrafe.’
Tsakanin shekarar 2011-2015 lokacin da yake a zauren Majalisar Wakilai ya taka muhimmiyar rawa da ta sanya ‘Yan Najeriya da dama ke son ya koma majalisar domin ci gaba da ayyukan alheri da s**a taimaka kwarai wajen bunkasa rayuwar mutanen kasar da ita kanta kasar ta hanyar gabatar da kudurori da shiga aikin ginin kasa.
Wasu daga cikin ayyukan da ya aiwatar a cikin lokacin da yake a majalisar sun hada da samar da cibiyoyin bunkasa karatun akan ilimin kimiyyar duniyar gizo a Makarantar Sakandare Gwamnati dake Kabala da kuma Kwalejin Tunawa da Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello watau (SMC). Wannan aiki ya sanyawa dalibban azama tare da samun ilimin kimiyyar duniyar gizo cikin sauki domin su tafi tare da zamani, wannan kuma ya kara sanya su kasancewa a sahun gaba a kowanne mataki na karatu, musamman a wannan lokaci da komai yake ci gaba da kasancewa a duniyar gizon. Wani abu da yake kara jan hankalin mutane musamman talakawa gare shi, shi ne irin kokarinsa wajen ganin dimbin matasan da s**a k**ala karatu bas u kasance hadari ga al’umma ba, wannan ya sanya shi fitowa da cibiyoyin sana’o’in hannu iri da dama domin ganin matasan sun sami dogaro mai amfani a cikin al’umma, shirye-shiryen Noma da Kiwon Kaji da Kiwon Kifi ba karamar muhimmiyar rawa s**a sanya rayuwar matasan da s**a sami shiga shirin ya yi ba, ko baya ga samun dogaro, sun kasance abun kwarai a cikin al’ummomin da s**a fito a cikin su, hasalima ba su da lokacin shiga kowanne irin tsari na daukar doka a hannu, ko zama fitsararru a cikin al’ummar su. Jami’ar Jihar Kaduna wadda ake yiwa lakabi da (KASU) a Turance tana cikin makarantun gaba da sakandare da s**a samu kyautar Kwamfuta dari biyu domin bunkasa ilimin kimiyyar duniyar gizo. Haka kuma duka da a tsakanin shekaru, Alhaji ABG ya samar da ajujuwa a Makarantun Firamare dake Kabala da Badarawa da kuma Marafa, an kuma samar da fanfunan tuka tuka bilahadadin a cikin mazabar.
Bai taba tuya ya manta da albasa ba, saboda sanin ilar yin hakan, saboda haka a dukkanin jam’iyyun da ya kasance cikin su, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar rayuwar ‘yansiyasa a kowanne mataki wannan da wasu dalilai da dama ya sanya wadanda s**a sha romon dimokuradiyya ta hannunsa su ke ci gaba da canza sheka zuwa sabuwar Jam’iyyar NNPP, kuma tarihin siyasarsa da irin kokarinsa ya sanya madugun Jam’iyyar NNPP kuma Dantakarar Shugaban Kasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya karbe shi da kansa, ya kuma tabbatar masa takarar kujerar majalisar wakilai ta kasa a karkashin tutar jam’iyyar.
Sunansa ya kasance kumfan Zinare ne ta dalilin namijin kokarinsa wajen bunkasa kasuwancin sadarwa a lokacin da yajagorancin Kwamitin Sadarwa a Majalisar Wakilai ta Kasa, ko baya ga fitowa da hanyoyin bunkasa kasuwancin sadarwa, jagorancinsa kuma ya samar da kyakkyawan yanayin samun kudaden shiga ga Gwamnatin Tarayya tare da kiyayewa da dokokin da s**a yi hukumar, haka kuma ya yi amfani da matsayinsa wajen samarwa matasan dake da ilimin akan sadarwa daga yakin Arewa ayyuka a dukkanin rassan hukumar dake kasar. Bincike ya nuna cewa yana ci gaba da saduwa da mutane domin fadakar da su, dangane da dacewar zaben Jam’iyyar NNPP a zaben 2023 daga sama har kasa, wani abu da yake baiwa mutane sha’awa dashi shi ne, har yanzu bai canza ‘ya’yan dandalin yakin neman zabensa ba, har yanzu su ne yake tare da su domin ganin yadda s**a rike masa amanar ko wuya ko dadi, ba su taba barinsa ba, saboda haka shi kuma ba zai taba barin su ba, wannan zumunci na Takalmin Kaza dashi mutane ke auna amanarsa da kuma k**anta gaskiyarsa a cikin tafiyar siyasarsa. Mutane da dama sun shirya tsaf domin goyon bayansa da Jam’iyyarsa ta NNPP domin ganin ta lashe babban zabe dake zuwa, yak**ata dukkanin ‘yantakarar jam’iyyar da magoya bayanta su hada kawunan su domin ganin sun raba Jaki da Duma a badi.
Bello Ahmadu Alkammawa
Director New Media