Jama atu,ahbabu tijjaniyya wadda awa.

Jama atu,ahbabu tijjaniyya wadda awa. this page has been founded purposely to promote islamic philosophy.and to educate people more about tijjaniyya discipline and
ideology.

Bude babban Masallacin da National chief Imam Ghana Sheik Nuhu Usman Sharubutu ya gina daga Kasar Ghana Tare Da Imam Abu...
05/09/2026

Bude babban Masallacin da National chief Imam Ghana Sheik Nuhu Usman Sharubutu ya gina daga Kasar Ghana Tare Da Imam Abulfathi Sani Attijjany

Ya Kamata Sunan Manzon Allah ﷺ Ya Kasance Mafi Soyuwa Ga Zukatanmu, Kuma Sunnarsa Ta Kasance Jagorar Rayuwarmu.Ya kamata...
04/09/2026

Ya Kamata Sunan Manzon Allah ﷺ Ya Kasance Mafi Soyuwa Ga Zukatanmu, Kuma Sunnarsa Ta Kasance Jagorar Rayuwarmu.

Ya kamata ƙaunar Manzon Allah ﷺ ta kasance mai girma a cikin zukatanmu, domin shi ne wanda Allah Ya aiko mana da shiriya, ya koyar da mu gaskiya, kyawawan ɗabi’u da hanyar samun yardar Allah.

Ƙaunar Manzon Allah ﷺ ba ta tsaya ga ambaton sunansa da baki kawai ba; tana bayyana ne ta hanyar girmama shi, koyi da halayensa da bin Sunnarsa a cikin rayuwarmu.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ

“Haƙiƙa, kuna da kyakkyawan abin koyi cikin Manzon Allah ﷺ.”
(Suratul Ahzab: 33:21)

Saboda haka, mu sanya Sunnarsa ﷺ ta zama jagorar mu’amalarmu, tarbiyyarmu, maganganunmu da ayyukanmu. Mu kuma koya wa ’ya’yanmu tarihin rayuwarsa da kyawawan ɗabi’unsa tun suna ƙanana.

Allah Ya cika zukatanmu da ƙaunar Manzon Allah ﷺ, Ya sa mu kasance cikin waɗanda suke bin Sunnarsa da gaskiya, kuma Ya haɗa mu da shi a Aljanna. 🤲❤️

04/09/2026
DA DUMI-DUMI: SHEIKH ABBAS SADAUKI YA KAMMALA DIGIRIN MASTERS A HARSHEN LARABCIƊaya daga cikin matasan malaman Ɗariqar T...
04/09/2026

DA DUMI-DUMI: SHEIKH ABBAS SADAUKI YA KAMMALA DIGIRIN MASTERS A HARSHEN LARABCI

Ɗaya daga cikin matasan malaman Ɗariqar Tijjaniyya, Sheikh Abbas Sadauki, ya kammala karatun Masters Degree a fannin Harshen Larabci a Northwest University, Kano.

Kammala wannan babban mataki na karatu na ƙara fito da irin ƙoƙarin matasan malamai wajen haɗa ilimin addini da na zamani, musamman a fannin harshen Larabci wanda ke da muhimmiyar rawa wajen fahimtar manyan littattafan Musulunci.

Muna taya Sheikh Abbas Sadauki murnar wannan gagarumar nasara ta ilimi, tare da roƙon Allah Ya ƙara masa ilimi mai amfani, hikima da ikon amfani da iliminsa wajen hidimtawa addini da al’umma.

Allah Ya ƙara ɗaukaka da albarka. Amin.

ABUN BURGEWA: DALIBAN JIHAR KANO DA KE KARATU A SHARDA UNIVERSITY, INDIA, SUN GABATAR DA MAULUDIN ANNABI ﷺGreater Noida,...
03/09/2026

ABUN BURGEWA: DALIBAN JIHAR KANO DA KE KARATU A SHARDA UNIVERSITY, INDIA, SUN GABATAR DA MAULUDIN ANNABI ﷺ

Greater Noida, India: Daliban Jihar Kano da ke karatu a Sharda University, India, sun gudanar da wani babban taron Maulidin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ﷺ a Babban Dakin Taro na Nalanda Premium Hostel, Knowledge Park III, Greater Noida, India.

An fara taron da addu’a da karatun Alƙur’ani Mai Girma, sannan aka gabatar da karatuttuka daban-daban da s**a shafi rayuwa, Sīra da kyawawan ɗabi’un Manzon Allah ﷺ daga bakin malamai da dama.

Daga cikin malaman da s**a gabatar da karatuttuka akwai Sheikh Malam Ibrahim Shira, Sheikh Malam Alawee, Gwani Malam Amir Adnan, da sauran malamai.

Haka kuma, an gabatar da Ta’aliki daga bakin Malam Suhaibu, Gwani Muhammad M. Said, M. Hassan Na Manzon Allah ﷺ, da sauran malamai na gida da na waje.

Karatun Tahni’a da Kasidar Manzon Allah ﷺ

An gabatar da Karatun Tahni’a daga bakin Malam Mannir Bello Dawakin Kudu, sannan aka gabatar da kasidar Manzon Allah ﷺ daga bakin Malam Zahraddin Umar Danbatta (Dagaci).

Taron ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Hausawan Sharda University, Cmrd. Sani Ahmad Sa’id, tare da ɗaukacin daliban Jihar Kano da sauran al’ummar Musulmi daga yankin Greater Noida, India.

A ƙarshe, an gudanar da addu’o’in neman nasara da fatan alheri ga ɗaukacin al’ummar Musulmi, tare da addu’ar samun zaman lafiya a Jihar Kano, Najeriya da kuma sauran al’ummar Musulmi a faɗin duniya.

Taron ya kasance wata dama ta ƙara tunawa da rayuwar Manzon Allah ﷺ, ƙaunarsa da kyawawan koyarwarsa, tare da ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin ɗalibai da al’ummar Musulmi.

Majiyar Rahoto: Mannir Bello Dawaki

03/09/2026

saoyyar annabi itace muslunci

WAHABIYA YA KAMATA KU SANI. Cewa Wai Annabi S A W Bai Ce A Yi Maulidi Ba. To Ku Sani Cewa Hatta Sahabbai Bai Taɓa Umarta...
03/09/2026

WAHABIYA YA KAMATA KU SANI.

Cewa Wai Annabi S A W Bai Ce A Yi Maulidi Ba. To Ku Sani Cewa Hatta Sahabbai Bai Taɓa Umartassu Kai-tsaye Da Wani Abu Na Su Girmama Shi Su Nemi Tabarruki Daga Gare Shi Ba Sai Bayan Sun Yi Yake Tabbatar Da Wannan Abin Da S**a Yi Na Girmamawa.

Saboda Haka Duk Wani Abu Na Tabbarruki Da Girmamawa Ga Annabi S A W Ba Ya Buƙatar Umarnin Annabi S A W Kai-tsaye. Kamar Yadda Sahabbai S**a Yi.

Su Kuma Masu Maulidi Suna Yi Dan Girmama Annabi S A W Da Neman Tabbarukin Sa Suke Yi.

Dan Allah A Duba Ma'anar Wannan Hadisin Da Idanun Fahimta.

Ba Annabi S A W Ya Umar Ce Su Yi Ba. Amma Da Yake Sun Yi Dan Allah Da Kuma Girmama Annabin Sa Sai Allah Ya Tabbatar Musu Tare Da Basu Matsayi Na Musamman.
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
- أنَّ رسولَ اللَّهِ صلَّى اللَّهُ عليْهِ وسلَّمَ خرجَ على حَلْقةٍ يعني من أصحابِهِ فقالَ ما أجلسَكم قالوا : جلَسنا ندعوا اللَّهَ ونحمَدُهُ ، على ما هدانا لدينِهِ ومنَّ علينا بِكَ قالَ آللَّهُ ما أجلسَكم إلَّا ذلِكَ قالوا آللَّهُ ما أجلسنا إلَّا ذلِكَ قالَ أما إنِّي لَم أستحلِفْكم تُهمةً لَكم وإنَّما أتاني جبريلُ عليْهِ السَّلامُ فأخبرَني أنَّ اللَّهَ عزَّ وجلَّ يُباهي بِكمُ الملائِكةَ
خلاصة حكم المحدث : صحيح
الراوي : معاوية بن أبي سفيان | المحدث : الألباني | المصدر : صحيح النسائي | الصفحة أو الرقم : 5441
| التخريج : أخرجه النسائي (5426) واللفظ له، ومسلم (2701)، والترمذي (3379) بنحوه.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇
لم يأمر النبي ﷺ الصحابة ابتداءً بالتمرّغ أو التبرك بذاته أو أثاره كأمرٍ تعبدي واجب، بل وقع ذلك منهم إجلالاً ومحبةً وأقرّهم النبي ﷺ عليه ولم ينههم عنه في حياته.

👇👇👇👇👇👇👇👇
مظاهر إجلال الصحابة وتبركهم بآثاره ﷺ
ماء الوضوء والعرق: كان الصحابة يقتتلون أو يكدحون على بقايا وضوئه ﷺ يتبركون به، كما ثبت في قصة عروة بن مسعود في صلح الحديبية.
النخامة والريق: ورد في صحيح البخاري أن النبي ﷺ ما تنخم نخامة إلا وقعت في كف رجل منهم فدلك بها وجهه وجلده.
الشعر والأظفار: قسم النبي ﷺ شعره وأظفاره بين الصحابة في حجة الوداع فأخذوها وحفظوها للتبرك.
الثياب والآنية: تبركوا بما مس جسده الشريف من ملابس وآداب وأقداح.

02/09/2026

محمد رسول الله صلى الله عليه وسلم تسليما كثيرا

Allah ya karbi addua,ar sheikh Jafar.Addu'ar Ja'Ja'afar Adam Ya ce :    "Ya ubangiji da mu da muke kira zuwa ga tafarkin...
02/09/2026

Allah ya karbi addua,ar sheikh Jafar.
Addu'ar Ja'Ja'afar Adam Ya ce :

"Ya ubangiji da mu da muke kira zuwa ga tafarkin Annabinka muke kira zuwa ga sunnar Annabinka, muke kira zuwa ga koyarwarsa, kar a ƙara kar a rage, da waɗanda suke ganin za a iya yin biye-biye kuma a tsira, abi wancen, abu wancen kuma a tsira, da mu da muka ce waɗancen al'amura (Maulidi) bidi'a ne ba koyarwar Annabi ﷺ bane, da su da s**a ce (Maulidi) son Annabi ne ﷺ gaske ne, ba bidi'a bane ba, Ya Ubangiji duk wanda yake kan dai-dai Allah ka taimake shi, Ya Ubangiji duk wanda yake kan dai-dai Allah ka sa Albarka a cikin Rayuwarsa, Ya Ubangiji duk wanda yake kan ƙarya kuma ya san ƙarya ce, Allah ka karya shi, ya Ubangiji ka fallasa shi, ya Ubangiji ka rusa gidansa, Idan sun isa su ƴan halal ne su faɗi wannan a masallatan su juma'a mai zuwa"

Address

Kaduna North
Kaduna

Telephone

+2348022325000

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jama atu,ahbabu tijjaniyya wadda awa. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share