07/06/2026
Yau na sake tabbatar da cewa irin su Datti Assalafiy babu komai a zuciya su sai kiyayya da burin yaɗa farfaganda. Naga yayi posting wani ID card yana maganar wai wannan ne ID card din da Peter Obi yayi wa yan Arewa lokacin da yake kan mulki.
To abun tambaya ina tsohon ID din da kuma kuka rinka posting a lokacin baya a wana ƙungiyar yan Arewa mazauna kudu.
To wannan ID card an samar da shi ne lokacin Peter Obi yana Gwamnan a Anambra ga dukkanin wani dalibi da yake karatu a jami'o'in garin Anambra domin samun damar kulawar lafiya kyauta ba tare da sun biya ko sisi ba.
A wannan lokacin Indai kai dalibi ne kaje ko wane asibiti a Anambra da wannan ID card din za'a duba ka ayi maka abun daya dace a kyauta ba tare da ka biya ko sisi ba.
Ana masa laƙabi da ANIDS (Anambra Integrated Development Strategy).