27/08/2025
Cikin hukuncin Ubangiji da Amincewarsa a Lahadin data gabata Shugabannin kungiyar Kwankwasiyya Social Media Kumbotso Karkashin Jagorancin Hon. Hamza Ahmad Telan mata, tare da sauran shugabanni ta gudanar da taro na musamman domin karawa Juna sani da kuma kara gabatar da kwaskwarimar a kunshin Shugabanci don karawa tafiyar tagomashi da zai kawo mata nasara..
Tun daga kan Karamar Hukumar har zuwa mazaba don ci gaba da tallata tsarin siyasar Jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da mai girma Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, sannan kuma Shugabanin Karamar Hukumar Kumbotso a matakin Majalisar Jiha da tarayya da kuma Karamar Hukuma tare da fito da manufofi Kyawawa dan kara Inganta tafiyar cikin lafazi mai kyau da mutunci da mutuntawa.
Taron ya samu halartar โyan uwa โYan Gwagwarmayar Siyasa shugabanin Social Media dake Kumbotso wadan da s**a kasance โYan Siyasa ne kuma โYan Social Media tun daga matakin mazaba zuwa Karamar Hukuma Da Jaha .
Muna kara tunasar da shugabannin wannan Kungiya da Membobinta a tallata tare da bijiro da sababbin manufofi babu muzantawa bare cin mutunci.
Muna adduโar Allah ubangiji ya bamu nasara Kyakkyawa a kara taimakon tsarinmu na Kwankwasiyya a kowanna mataki, wadan da kuma s**a kara samun kan su cikin shuganaci muna taya su murna Allah ya bada ikon kwatanta dai dai tare da gabatar da ayyuka cikin ladabi da biyayya.
Comr. Ahmad Lawan Garba
Secretary: Kwankwasiyya Social Media Kumbotso.