25/09/2026
SARAKUNAN MALLAWAN ZAZZAU
Gidan Mallawa gida ne na sarauta a masarautar Zazzau, Kuma shine gidan da Sarkin zazzau na yanzu Mai martaba sarkin zazzau Amb Ahmad Nuhu Bamalli ya fito. zama sarkin Zazzau na farko biyo bayan shekaru 100 da sarauta tayi kaura daga gidan na Mallawa.
Tun farko daga Malam Musa Bamalli wanda shine wanda ya kafa gidan Mallawa, kuma shi ne sarkin Zazzau na farko cikin sarakunan Fulani wanda shehu usmanu Dan fodiyo ya bawa tutar jihadi.
Sarakunan Gidan Mallawa:
Mai martaba Sarkin zazzau Malam Musa Bamalli: Shi ne sarkin farko daga gidan Mallawa kuma sarkin Zazzau na farko daga Fulani, wanda yayi sarauta cikin shekarun (1804β1821)
Sai kuma sarki na biyu cikin gidan na mallawa wato Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Sidi Abdulkadir, wanda yayi sarautar Zazzau a shekarar (1853).
Mai Martaba Sarkin Zazzau Mallam Malam Abubakar, shine Sarki na uku cikin a cikin jerin sarakunan gidan Mallawa. Wanda yayi Zamaninsa na sarauta a cikin shekarun (1871β1874).
Sarkin zazzau na hudu a cikin jerin sarakunan mallawan shine Mai martaba Sarkin zazzau Malam Aliyu Ζan Sidi, yayi Sarauta cikin shekarun (1902β1920). Shi ne sarkin farko da gwamnatin Turawan mulkin mallaka ta Birtaniya ta naΙa sarauta a Birnin Zazzau.
Tun bayan da Sarkin zazau Aliyu Dan Sidi ya bar Sarautar zazzau a shekarar 1920, ba a kuma samun Sarkin da ya fito daga wannan gidan na Mallawa ba sai cikin shekarar 2020, inda aka nada Mai martaba Sarkin Zazzau Amb Ahmed Nuhu Bamalli wato Sarkin zazzau na yanzu kenan. Bayan shekaru Dari (100) sai kuma sarauta ta dawo gidan Mallawa.
Allah yaji kansu ya gafarta musu da dukkan iyayenmu baki daya AMIN.