09/06/2025
Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin tarayya ta biya ta diyya bayan da aka soke Hawan Sallah na tsawon shekaru biyu a jere.
Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Tajo Uthman ne ya yi wannan kiran a ranar Lahadi yayin da Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya kai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ziyara a gidan gwamnati.
Uthman ya ce jihar Kano ta tafka asara mai tarin yawa sakamakon soke hawan na al’ada wanda ake gudanarwa shekara-shekara da ya ke jawo hankalin masu yawon buɗe ido na cikin gida da waje.
Kwamishinan Ya yi nuni da cewa, tasirin soke Hawan ya shafi tattalin arzikin kano wanda zai yi tasiri a kasafin kudin shekara mai zuwa na jihar.
Ya kuma ce dole ne gwamnatin tarayya ta ɗauki alhakin wannan asarar da ta jawowa jihar kano sakamakon soke Hawan don dale ne biya jihar diyya.
Menene ra'ayinku?