16/11/2025
Assalamu Alaikum,
Zuwa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano,
H.E. Engr. Abba Kabir Yusuf.
Halin da makarantar Muhammad Vice Adamu Senior Secondary School Kano, Fagge (MVA Kuka) take ciki:-
1 - Amincewa da karbar gayyatar masu yin cacar karta da shan sigari (cigarette) wadanda zasuyi bikin shekara a cikin makaranta a duk ranakun asabar da lahadi, kuma duk ranar Monday dalibai idan sunzo sai sun share filter taba sigari (cigarette) mai tarin yawa a cikin classes nasu, inama ace quiz competitions akeyi ko musabaka Qur'ani mai girma.
2 - Cin zarafin malamai a gaban dalibai idan sun samu sabani a tsakaninsu da shugaban makaranta.
3 - Kin gyara duk wani abun amfani da ya lalace a makaranta, kin samar da abubuwan rubutu kamar Chalk ko marker ta rubutu duk da ana karbar P.T.A dues awajan dalibai, yanzu haka malamai ne suke hada kudin chalk da marker suke siya.
4 - Maida filin makaranta wajan yin loading motoci ana karbar kudi,
5 - Sawa a dauke duk wani malami dan asalin fagge idan yaga zai kawo masa cikas akan abinda yake son yi, anyi hakan Kashi daban - daban lokaci daya an dauke malamai 11, malamai 4, kwana nan ankara dauke malamai 6 ba tare da an maida gurbinsu ba. Saboda idan kai kace adauke maka malami baza'a yimaka replacement ba ko shi kadai ne a department din.
6 - Yunkurin batar da computers guda 3 da fakewar headquarter ne s**a ara, kuma malamai sunyi magana da H.o.d computer ya tabbatar andawo dasu. Kuma ya hana yin computer practical da sauran courses masu practical Saboda za'a kashe kudi.
7- Yanke wayar wuta aluminum cable mai hawa hudu daga pole zuwa office na principal .
Wannan kadan daga cikin matsalolin Wannan principal na Muhammad vice Adamu senior secondary school kuka fagge don haka akwai bukatar mahukunta su shigo su bincika wannan lamari domin a gyara.
Allah ya ba da ikon gyarawa,
Mun gode.