03/03/2025
KUSKUREN MAI AZUMI (03)
"Yana daga cikin kuskuren mai azumi, shine yawan kalle-kallen film da waƙe-waƙe"
-
"Yana daga cikin babban kuskuren da mai azumi zai yi musamman a lokacin da yake tsaka-da azumin nasa, yace zai kasance yana ɓata lokacinsa wajen kallon fina-finai a maimakon karatun alƙur'ani da duk wani aikin ladan da zai inganta azuminsa"
-
"Sau da yawa zaka riski masu azumi sun duƙufa wajen kallon shirye-shiryen fina-finai wai da sunan rage lokaci, wanda kuma hakan ba ƙaramar asara bane ga mai azumi, domin ya shagaltu daga ambatõn ubangijinsa ya biyewa tafarkin shaiɗan