18/04/2026
GIDAN UNCLE
PAGE 11
DAGA HAUSA NOVEL TV
A saluɓe yake kallon Hajiya, lallai ta ɗauki lamarin nan da zafi. Saboda tunda yake da ita, ko baƙar magana ba zai iya tuna ranar da ta faɗa masa ba. Amma yau gashi tana neman tsine masa. Cikin rashin ƙarfin gwiwa ya matsa jikin gadon Umaimah ya ce:
“Sannu babyn Uncle, ya jikin yanzu? Ina ne yake miki ciwo?”
Ya faɗa yana ɗora hannunsa a saman kanta. Ajiyar zuciya s**a yi a tare. Cikin sanyin muryarta ta ce:
“Da sauƙi.”
Murmushi ya yi ya ce:
“Ok, ku zo mu tafi, kada ku dame Aunty. Kun ga ba ta da lafiya ko?”
Nihal ce ta ce:
“Mu dai a nan za mu zauna wurin Aunty. Da safe ta dafa mana tea, ta yi mana wanka.”
Maliha kam kuka ta sa wai a dole ba za ta koma wurin uwarta ba. Da ƙyar ya shawo kan yaran, suna kuka suna ƙorafi. Ya ja su s**a fice daga ɗakin. Ita ma Umaimah ƙwallayenta ta share. Ba ta son ko kaɗan ta ji yaran suna kuka, jin shi take har cikin ƙirjinta.
Hajiya kam haushi ne ya kusa kashe ta, ita a tunaninta maganar da ta faɗawa Hameed ɗin ce ta sa Umaimah kuka. Kwanansu ɗaya a asibitin, ya zo da safe da zai tafi aiki ya duba ta, ya jima sannan ya tafi. Office a CBN Kano yake aiki.
Bayan tafiyarsa, babu jimawa Dr Saleem ya ba su sallama, s**a tafi gida. Yayar Hameed, Aunty Zarah, ta zo gidan saboda Hajiya ta kira ta, ta zayyane mata komai. S**a haɗu a parlour s**a yi ta Allah-wadai da abinda Hameed ya yi wa Umaimah.
Abin takaici, har da Daddy shi ma ya biye musu, ya ce:
“Wlh ba don Hameed ɗana ba ne, babu yadda zan yi da shi. Da sai na yi ƙararsa an fiɗɗa wa marainiyar Allah haƙƙinta. Jiya fa, tsabar ya raina mini hankali, na kira shi ina yi masa faɗan kuskuren da ya yi, sai ce mini ya yi shi fa bai yi wani laifi ba. Umaimah matarsa ce. Laifinsa ɗaya, ya ɓoye mana gaskiya. Da na ji rainin hankalin nasa ya yi yawa, sai na ce ya tashi ya ba ni guri kawai. Sai ya fashe mini da kuka, wai shi ba mazinaci ba ne. Idan ba mu yarda da abinda ya faɗa mana ba, mu ba shi dama ya gabatar da wasu daga cikin shaidun da s**a shaida ɗaurin aurensa da Umaimah. Faɗa na haushi da shi k**ar zan cinye shi, amma bai fasa faɗa mini ba. Shi fa matarsa ya yi mu’amala da ita, ba wata ba. Har yana neman yi mini rashin kunya, wai gobe ma idan yana buƙatarta zai neme ta ya yi duk abinda ya ga dama da ita tunda shi ya san ba zina yake yi ba. Saboda haka, Hajiya, sai kin sa tsaro sosai akan yaron nan, saboda idan kika yi sake za a samu matsala. Tabbas shi ma maganarsa abar dubawa ce. Saboda haka, zan yi bincike sosai kuma na ce ya gabatar mini da shaidunsa nan da kwanaki uku. Idan ba haka ba, zan ɗauki matakin shari’a a kansa.”
Yana faɗin haka, ya tashi ya nufi sama. Ita ma Umaimah miƙewa ta yi daga jikin Hajiya ta shige ɗakin da idan ta zo take zama a ciki. Ta kwanta. Ita dai zuciyarta babu daɗi kwata-kwata. Ba ta jin daɗin yadda suke aibata Uncle ɗinta. Saboda ko ba komai, ya yi mata abubuwa da yawa da ba za ta iya mantawa da shi ba.
Tana wannan tunani, wayarta ta yi ƙara. Ta ɗauka da sauri, ta ga ƙawarta ce Sa’ud. Da sauri ta ƙara a kunnenta ta ce:
“Hello Sa’ud, ki zo gidan Hajiyata don Allah yanzu. Ina son ganinki.”
Tana faɗin haka ta kashe wayar. Tana nan kwance, ba a fi mintuna ashirin ba, ta ji muryar Sa’ud ɗin suna gaisawa da Hajiya. Shigowa ta yi tare da mayar da ƙofar ta rufe. Ta zuba wa Umaimah ido tare da cewa:
“Na shiga uku Umaimah! Meyeye ya same ki haka kika rame?”
Kuna sauraron littafin: GIDAN UNCLE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Lumshe idonta ta yi tare da miƙewa zaune ta ce:
“Meye ma bai same ni ba Sa’ud, bari na yi na cikin Uncle.”
Nan ta kwashe su komai ta faɗa mata, ta ce:
“Sa’ud, ni fa ina tunani abinda Uncle yake faɗa gaskiya ne, saboda shekara ɗaya baya mun je Maiduguri. Lokacin da gani sai shi sai yaran Aunty Sadiya, ƙin zuwa ta yi, ta ce a’a ba taron family ɗinsu ba ne.
Ina kwance na yi matashin kai da cinyar Kaka. Ya shigo parlour-n, tunda ya shigo na ga yana min kallon ƙurullah, hankalinsa gaba ɗaya yana kan ƙirjina, saboda rigar jikina ba wata ta ƙirƙi ba ce, kuma ko bra ban sa ba. Ashe ita ma Kaka ta lura. Kawai sai na ji ta ce:
“Ko kana so ne?”
Sosa kansa ya yi ya ce:
“Wlh Kaka, akwai matsala, ina buƙatar matata sosai.”
Dariya ta yi ta ce:
“Kai da kayanka Hameed, ni ma na matsu a wuce wurin nan. Na matsu na ga irin taku baiwar, na matsu na ga yayanka da baby kafin ƙasa ta rufe idona. Hameed, ka fito ka bayyanawa duniya matarka ce ita, ko kai ma ka samu sauƙin wannan banzan rayuwa ta gidanka. Su kansu iyayenka suna son ba ka samun kulawar da ta dace wurin matarka, amma sun kasa nema maka mafita. Me ake da irin wannan auren da haƙƙin kwanciya ma ba za a sauke ba, b***e a kai ga na kulawar yau da kullum? Hameed, kullum gindinka a tsaye tun bayan aurenka, ban taɓa gani ka canza ba, ban taɓa gani wandonka ya zauna daidai ta gaba ba. To gaskiya, ka yi ƙoƙarin nemawa kanka mafita kafin mace ta kashe ka da lafiyarka da komai ka zama sorry.”
Duk cikin yarenmu na Shuwa take maganar. Wlh a lokacin ban fahimci me kalaman Kaka suke nufi ba, kawai dai mamakin rashin kunyarta nake yi. Sa’ud sai lokacin da Uncle ya ɓare ni ya ratsa ni, sannan kalaman Kaka s**a riƙa dawo mini.
Uncle Hameed jarababbe ne ajin farko. Tun ina gudun abinda yake mini har na saki jiki da shi, duk da wahalar da nake sha idan yana cinna, haka nake jurewa. Wlh sai da ya kasance idan ba ya tare da ni ba na jin daɗi. A zahiri ban son mu’amalarmu, amma a baɗini ina so. A cikin sati biyun nan na ji jiki sosai a hannunsa, saboda babu raga ya ko ta kwabo tsakanina da shi. A dare sai ya neme ni sau uku. Tun a lokacin na fara jin jikina wani iri, ashe ciki ya ɗirka min.
Bayan dawowar Aunty Sadiya sai na yanke duk wata alaƙa tsakanina da shi, ba don ina so ba, sai don tsoron ranar da asiri zai tonu. Ashe na baro ƙari tun ran tubani. Kwana uku baya ya ɗauke ni da zummar Daddy yana nema na. Kawai ya kai ni wani hotel, tunda muka je nake amai. A haka ya yi abinda yake so ya yi da ni.”
Nan ta zayyane mata komai, ta kuma ce:
“Tunda abin ya faru, kowa laifin Uncle yake gani. Su Hajiya sai aibata shi suke yi. Ni kuma ba na son hakan, Sa’ud. Ina son ganinsa yau amma sun hana mu ganin juna. Ina jin shi yana roƙon Hajiya yana son magana da ni, ta zage shi tass, dole ya ba ta haƙuri ya fice.”
Kuna sauraron littafin: GIDAN UNCLE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Ajiyar zuciya Sa’ud ta yi ta ce:
“Tabdi! Lallai Uncle yana cikin bala’i. Yanzu gidan sa na fara zuwa. Ina shiga na tabbatar da ba lafiya ba. Kayanki da duk wani abu da yake mallakinki an yi watsi da su a harabar gidan. Gabana na faɗuwa, na shiga parlour-n. Na ɗauka kina ciki, a nan na tarar da wani tashin hankali.
Sababbin kayan furniture da ya zuba miki an ɓalle su ɓallar wulaƙanci waɗanda ba za su moru ba. Ita da wata ƙawarta da wani saurayi — ina tunani ƙaninta ne — suna ta zazzaga bala’i tare da sake famfata akan kada ta kuskura ta yarda da wannan cin amanar.
Ta ɗaga masa hankali har sai ya sake ki. Wai asiri kika yi masa kika ba shi ya ci a abinci, shi ya sa idonsa ya rufe har yake faɗa mata maganganu akan ki. Wai banda ma jarabarsa me zai yi da ke, yarinyar da ya ci kashinta da fitsarinta.
Wlh aiki ne babba a gabanki. Idan har kin tabbatar mijinki ne, cire kunya za ki yi ki lailaye abinki, ki ba shi komai, ki yi masa komai. Ki ƙyale shegiya da haukanta. Ba na son cikin nan ya zube ba Umaimah, na so a ce yana jikinki har yanzu, da ko ba aure tsakaninku na san sai an ɗaura shi. Yanzu dai ba wannan ba, wane shiri k**e yi na tarar angonki?”
Kallon Sa’ud ta yi, idanunta taf da ƙwalla, ta ce:
“Ina jin tsoro Sa’ud, na san wace Aunty Sadiya, na san haukan kishinta. Wlh duk kishinmu Shuwa da ake faɗa, Sadiya ta fi mu, ita da take ma Bahaushiya. Na san za ta iya kashe ni k**ar yadda take faɗa.”
Kallon banza Sa’ud ta watsa mata, ta ce:
“Kaji banza. Ke kuma tsayawa za ki yi har ta kashe ki kina zaune? Ai wannan mulkin mallakar ya wuce, dole ki zage ki je mata da duk yadda ta zo miki. Idan ta ce ku zauna lafiya, ku zauna. Idan ta ce haukan za a yi, ki nunawa shegiya kin fita iyawa, ki ci uwar ubanta a hauka. Ki nuna mata naki na jini ne na gado ne, ke da k**e Shuwa-Arab har a faɗa miki kishi? Allah ya tsinewa uwar wanda ya ji tsoro ya fasa. Wlh yarinya, zagewa za ki yi, ki cire tsoro ki k**a ɗan’uwanki mijinki a hannu. Kin ji dai na faɗa miki.”
Tunda Sa’ud ta fara maganar, take kallonta har ta gama, sannan ta ce:
“Amma dai Sa’ud, kin san da ciwo abinda ka raini yarinya kuma ta zo ta zama kishiyarka. Gaskiya babu adalci a cikin lamarin.”
Tsaki Sa’ud ta yi, ta ce:
“Kuma fa kin fara ba ni haushi Umaimah da k**e wannan maganar. Ke kika ce kada ta tsaya ta kula da mijinta ko ke kika hana ta k**a mijinta? Ai dama ta san haka za ta faru, tunda ita ce ta ba da ƙofar hakan. Inda tana sauke masa haƙƙinsa, tana ririta shi k**ar jariri, da bai yi sha’awar wata macen ba.
Ke bari ki ji, wlh mazan zamanin nan, ko kana kula da su ma sai ka haɗa musu da Lahaula da Yasin, har da Suratul Shifa don neman musu lafiya. Ke ina son samu ne har da Suratul Jinn duk ki riƙa tofa musu, don wani lokaci k**ar masu shafar aljanu haka suke. B***e ka sake shi, sai ka saki k**ar makahon raƙumi, duk inda ya ga dama ya cilla ƙafarsa.
Ai ta ma gode wa Allah da abin ya tsaya mata iyanan. Inda wani ne ma yadda yake da lafiyar nan, in ya riƙa neman mata, har sai ya kwaso mata ƙanjamau, ya zo ya gwagwada mata, su shiga uku. Sakaryar banza da ita, ke ma idan kika zama lusara irinta, wlh kuna ji kuna gani mijinku zai fi ƙarfinku. Kuma Billahillazi, kin ji na rantse, ko ni ya ce yana so, ba daka zan yi ba, bori ya hau don samun miji irin Uncle Hameed a zamanin nan ba duk mace mai sa'a ba.”
Kuna sauraron littafin: GIDAN UNCLE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Ajiyar zuciya ta yi, daidai lokacin wayarta ta yi ring. Da sauri Sa’ud ta ɗauka, ta yi murmushi ta ce:
“Kin ga ɗan halak ko ɗan uwarki. Kashe murya ki k**a abinki, babu komai. Ko ba aure akwai ƙauna, b***e ma ni na daɗe da sanin mijinki ne, don Yaya Yusuf ya daɗe da faɗawa Farouq ɗin mu cewa ya fita daga harkarki, kada ya haɗu da fushin Hameed saboda ke ɗin matarsa ce.”
Katsewa wayar ta yi, ta ajiye, ta kamo hannun Umaimah, ta ce:
“Wlh Umaimah, ki ajiye gidadancin nan naki, ki mayar da kanki karuwa da gaske a wurin mijinki.”
Sake shigowa kiran ya yi, ta miƙa mata. Hannunta na rawa, ta ɗaga ta ce:
“He… Hello.”
Ajiyar zuciya ya sauke, ya ce:
“Babyn Uncle, ya jikinki?”
A sanyaye ta ce:
“Da sauƙi.”
Murmushi ya yi, ya ce:
“Ke ma fushin k**e yi da ni ko baby?”
Da sauri Sa’ud ta kaɗa mata kai, ta ce:
“A’a Uncle.”
Ajiyar zuciya ya yi, ya ce:
“Har na ji sanyi, babyn Uncle. Na san kowa fushi yake yi da ni akan abinda ya faru tsakanina da ke, wanda na san rashin sani ne ya sa suke ganin baƙina. Ina cikin tashin hankali a gida, babyn Uncle, wurin Sadiya. Ba sai na faɗa miki na ɓangaren Hajiya da Daddy ba, kin san komai. Amma duk ba su dame ni ba k**ar naki. Don Allah kada ki ba da damar da za a raba mu, Umaimah. Wlh akwai matsala cikin hakan, ba ƙarama ba. Ina son ki ba ni haɗin kai, babyn Uncle. Kin ji.”
Ajiyar zuciya ta yi ta kalli Sa’ud, ɗaga mata kai ta yi alamar to, ta ce:
“To Uncle.”
Numfashi ya sauke ya ce:
“Yauwa baby na, Allah ya yi miki albarka. Zan kira ki zuwa dare, amma jinin ya tsaya ko?”
“A’a,” ta faɗa.
Murmushi ya yi ya ce:
“Shikenan, shi ma na san zai tsaya kafin lokacin da zan ɗauke ki. Ki kwanta ki huta, sai mun yi waya anjima.”
Ajiye wayar ta yi tana haki k**ar wadda ta yi gudun fanfalaƙi. Dariya sosai Sa’ud ta yi ta ce:
“Kaji banza don Allah, wayar k**e wa wannan hakin. To, ya kika yi ranar farko da ya turmushe ki?”
Dariya ta yi ta ce:
“Wlh ban san komai da ya faru ba, tun dare sai ɗaya na rana na farka na ganni ɗaure da drip.”
Ƙara sheƙewa da dariya Sa’ud ta yi ta ce:
“Lallai Uncle ya ga matar wannan ragwanta haka.”
Dariyarta ta ƙara wa sauti, ta ce:
“Muguwa kuma a haka don rashin imani kika ba ni magani ya haukata ni da kaina, na riƙa roƙon Uncle ya gurgure ni. Aikuwa na ci na ci ubana ranar na ga yadda ake barin madara.”
Dariya ta kuma sheƙewa da ita, ta ce:
“Irin muguntar da aka yi mini, ni ma na yi miki haka. Zainab ta yi mini washegarin ranar da Yaya Auwal ya fara zungura ta. Ke ban faɗa miki wani abu ba, Zainab ta yi ciki. In faɗa miki, Abba yana ta bala’i wai mun cuce shi. Shi kuwa Yaya Auwal ya ce to Abba, mun faɗa maka aure muke so, ka ƙi yi mana. Yanzu ga irinta nan, shi ne ya ce ta turo Jabir ɗin a yi magana, shi ma Yaya Auwal za su yi magana a tsayar da lokacin bikin mu. Amma ni fa gaskiya ba na jin zan auri Yaya Auwal.”
Kallonta Umaimah ta yi da sauri ta ce:
“Me ya sa?”
Kuna sauraron littafin: GIDAN UNCLE
Daga: Hausa Novel Dot Com
Kada ku manta ku yi:
Follow
Like
Share
Mun gode.
Murmushi ta yi ta ce:
“Na samu wani guy ne, sunansa Anwar. Wlh ya fi Yaya kawo wuta, gashi da barin Naira, nishi nake so. Yanzu ma mun yi magana da shi, na ce ya turo gidan mu. Ya ce mini to, bari ma na kira shi mu ji.”
Ta ɗauki wayarta ta kira shi. Sai da ta kira kusan sau uku sannan ya ɗaga, yana wani irin nishi ya ce:
“Ahhhh baby, ina kan aiki yanzu za... za mu yi waya anjima. Na faɗawa Dad ma maganarki...”
Kit, ya kashe wayar. Mamaki ya cika Umaimah, ta ce:
“Kayy, wannan kuwa ƙalau yake?”
Ajiyar zuciya Sa’ud ta sauke ta ce:
“Ƙalau yake, sai iskanci. Yanzu haka yana tare da wata ne.”
Da sauri Umaimah ta dube ta ta ce:
“Da wata fa kika ce? Kuma a haka k**e tunanin auransa? A’a, indai kuwa haka ne, ba ki yi wa kanki zaɓi na ƙwarai ba.”
Kallon Umaimah ta yi ta ce:
“Ni ma na sani Umaimah, to amma ya zan yi? Allah ya jarabce ni da son sa. Wlh ba zan iya auren wani ba shi ba.”
Girgiza kai Umaimah ta yi ta ce:
“Gaskiya kada ki fara. Kada son zuciya ya sa ki tsallake. Tabbas ki k**a gaibu. Gaskiya ba zan goyi bayan ki yi wannan gangancin ba. Ki auri Yaya Auwal, ya fi dacewa da ke kuma sai ya fi ganinki da ƙima saboda ya san shi ne ya fara lalata ki.”
Murmushi ta yi ta ce:
“Duk na yi wannan tunanin Umaimah amma na kasa jurewa. Ki taya ni da addu’a kawai.”
Haka s**a ci gaba da hira sai dare, sannan ta raka ta bakin titin unguwarsu. Ta juyo ta dawo.
A hanyarta ta dawowa, ta ji ana danna mata horn. Da sauri ta juya, ajiyar zuciya ta yi. Ya buɗe mata motar ya ce:
“Meye ya fito da ke da daren nan? Wa ma kika faɗa za ki fito?”
Kawar da kai ta yi. Ya yi murmushi tare da jan motar, s**a ƙarasa gidan. Ya yi parking, ta buɗe za ta fita, ya yi saurin riƙo hannunta. Ta ɗago da sauri, ƙaraf idonta ya faɗa cikin nasa.
Ya matso sosai, tare da sauke kujerar da take kai ta yi baya, ta kwanta. Kafin ta tashi, ya bi ta ya danne tare da juyo da fuskarta, ya ɗora lips ɗinsa akan nata, yana sauke mata wani hot kiss.
Lumshe idonsu s**a yi a tare. Ta sanya hannunta biyu ta rungume shi, tana taya shi tsotsar baki. Hannunsa biyu ya sanya ya dafe hips ɗinta, yana jin wani irin feeling ɗinta na bijiro masa.
Zare bakinsa ya yi daga nata, ya sanya hannunsa ya janye mayafin jikinta, ya ɗora hannunsa saman b***s ɗinta, yana matsa su a hankali ta cikin riga. Tunda ta lumshe idonta, ba ta buɗe ba sai da ta ji bakinsa saman ni***es ɗinta, yana jan su a hankali yana sakin nishi mai shiga jiki. Sake ƙanƙame kansa ta yi, ta tura hannunta cikin sumarsa, tana faɗin:
“Washhhhh... Uncle.”
Daidai lokacin ta ji ana ƙwanƙwasa motar da ƙarfi. Da sauri ta fara ture shi, tare da kallon wurin. Hajiya ta ga tsaye a jikin motar...
________________________________________
Sai mun haɗu a next page.
Comment, Like da Share ɗin ku shi ke Sani. Jin karsashin yin saurin, suburbuɗo muku wani page ɗin!
📖 Kuna sauraro Littafin Gidan Uncle
Daga: Hausa Novel Dot Com
📌 Kada ku manta ku yi:
✅ Follow
👍 Like
🔁 Share
🙏 Mun gode
📍 Mu haɗu a Shafi na 12, in shaa Allah.