06/12/2023
...shiyasa Harkar aikin lafiya ya banbanta da sauran ayyuka
Tun farkon fara tsunduma cikin sha'anin koyon kiwon lafiya, dalibai s**an fuskanci horo na musamman domin cewa sun kusa fara mu'amula da dan Adam wanda yake da rai guda daya kawai. Asaboda hakane ma koyon aikin ya ke farawa da gwaje-gwaje akan gawarwaki wani lokacin ma ake hadawa da dabbobi saboda dai taka tsan-tsan wajen kula rayukan mutane. Wannan yakan dauki lokaci mai tsawo (Rabin lokacin gabatar da karatun baki daya).
Hatta kalar jarrabawar da ake yi ma irin wannan daliban tasha ban-ban da sauran dalibai. Misali: bayan shafe dogon zangon karatu ta hanyar kwankwadar zallar karatu da (practicals) sai a shirya musu jarrabawa kusan kala uku; ta rubutun zube; ta gwaje-gwaje (practical) sai kuma ta baki (wanda manyan professors zasu zo daga jami'oin da muke dasu a wannan kasa.....(bari mu bar wannan maudu'in mukoma kan dalilin wannan rubutu nawa).
Saboda dai a Kara tabbatar da cewa lafiya da kuma rai sune abin dubawa farko, wannan daliban akan yi musu hukuncin yin karya yayin amsa tambaya a lokacin jarrabawa ta hanyar rage musu maki (maimakon abarmusu sufuri) ga duk amsar da ta kasance ba dai-dai ba: ma'ana dai dalibi idan bai san amsaba yafi kyau ya bar wurin bai sani ba akan yayi canki-canki duk dai domin ladabtar da su sugane cewa ba ayin canki-canki akan lafiyar mutum ko kuma dungurungum rai. Wato dai idan ka samu kanka/ki a halin duba mara lafiya yafi kyau kayi abinda ka sani akan mara lafiya abinda baka sani ba kar ka gwada (canki-canki) akan mara lafiya maimakon haka anfiso ka tura mara lafiya gurin kwararre wanda yafika/ki.
Daga lokacin da wadannan dalibai s**a doshi kusantar mutane masu rai wani sabin horone na musamman wanda zasu dinga karba wajen manyansu lokaci zuwa lokaci. Tare da tilasta musu akan ko da wasa kar su soma duba marasa lafiya akaran kansu. Acikin irin wannan horo ne dalibi zai taka tsan-tsan akan tabbatar da gaskiyarsa a duk lokacin da aka tambayeshi wata tambaya.
Ina tuna wani abokin karatu wanda irin wannan ya taba faruwa akansa bayan an umarce shi da ya duba mara lafiya sai aka samu akasi baiyi wani abu ba acikin abinda yakamata ace yayi. Koda aka tambayeshi kuwa sai yace yayi. Da aka tambayi mara lafiya kuwa sai aka gano baiyi ba wannan ne yasanya shi maimaita wannan shekarar karatun baki daya.
Akodayaushe malaman suna tsoratar/ladabtar da Daliban ta hanyar yi musu tajdidin kalmar nan da aka gada daga wajen magabatan kiwon lafiya a yaren latin ''primum non nocere'' wato dai ''farko kada ku cutar".
Har ila yau yana daga cikin wajibi, sanya tsarin tanadin shari'ah abisa sakacin aiki domin dai tabbatar da nagartar aiki bayan an kammala karatu wanda malamai masana shari'ah zasu dinga bada lacca lokaci zuwa lokaci ga wadannan dalibai.
Bayan samun damar fara aiki a matsayin ma'aikacin lafiya, babu wani kuskure a wannan lokacin idan kasani kawai kasani kayi abinda ya dace(bada magani) idan baka sani ba baka sani ba kawai shima kayi abinda ya dace( tura mara lafiya wurin kwararren ma'aikaci). Akasi akan yin daya daga cikin wannan tou wannan kuskurene kuma a wannan fuskar ana kiranshi ganganci wanda ya kan iya jawo rasa lasisin aiki baki daya.
Na tabbata hukuma tana matukar kulawa da wannan dokokin da aka kafawa ma'aikatan lafiya. don haka yana da kyau hukuma kar su tsaya iyakar wani sashe na ma'aikata su kyale wani sashe su ci karansu babu babbaka.
Allah Ya sa mu dace.