10/06/2024
*AYYANA DOKAR TA BACI KAN ILIMI A JIHAR KANO*
ABINDA AYYANA DOKAR TA BACI KAN ILIMI A JIHAR KANO TA KUNSA:
- Kaddamar da fara gyaran gaba daya makarantun firamare da sakandire a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar
- Gina ajujuwa guda 1,000 a fadin kananan hukumomi 44 (LGAs).
- Fara gyaran dakunan gwaje-gwaje guda 300 tare da gina karin 300 a makarantu 200 a fadin kananan hukumomi 44.
- Jimillar ajujuwa 28,264 za a gina nan da shekaru 3 masu zuwa a fadin jihar.
- Gwamnatin jihar Kano zata dauki ma'aikata akalla 1,000 a makarantun gaba da sakandire a jihar.
- Daukar karin malamai 10,000.
- Daukar malaman BESDA sama da 5,632 aiki na dindindin a jihar.
- Sake bude dukkanin makarantun kwana da gwamnatin baya ta rufe.
- Raba abinci sau daya a rana ga kowane dalibi a dukkanin makarantun firamare na jihar.
- Sake dawo da shirin raba kayan sawa na makaranta kyauta ga duk daliban firamare 1.
- Raba rancen Naira miliyan 300 ga malaman firamare.
- Amfani da manyan bas guda 70 domin kai kawon dalibai mata daga gida zuwa makarantunsu.
- Karasa biyan ragowar kudaden makaranta na wadanda s**a ci gajiyar tallafin karatu a makarantu daban daban tare da basu satifiket
- Biyan kudin rajistar NECO da NBAIS ga dukkannin daliban da s**a cancanta.
- Gyarawa da haΙaka makarantun koyar da harsuna mallakin gwamnatin jihar.
- Sake dawo da shirin KONA ga malaman makarantun firamare da sakandare a jihar.
- Amincewa da gaggawar gyara makarantun da aka samu annobar gobara a kananan hukumomi daban-daban.
- Kammala da kuma amfani da makarantun Islamiyya 44 da kwalejojin fasaha guda 44 da gwamnatin Sanata Rabiu Kwankwaso ta kaddamar.
Makasudin ayyana dokar ta-baci kan ilimi a jihar Kano:
- Kowace Makaranta, makaranta mai kyau.
- Kowane Yaro, Dalibi.
- Kowane Dalibi, mai koyo mai himma.
- Kowane Malami, malami mai kulawa.
- Kowane uba, abokin tarayya mai taimako.
- Gwamnatin ku, mai himma wajen samar da ilimi da kuma cigaban βyan jihar