PAMA_Political Awareness Movement & Advocacy

PAMA_Political Awareness Movement & Advocacy A Doctrine To Liberalism In Politics

Murnar mu na neman komawa ciki!Kwanakin baya farashin kayan abinci ya sauka matuƙa, amma zuwa yanzu lamarin sai addu'a, ...
07/11/2024

Murnar mu na neman komawa ciki!

Kwanakin baya farashin kayan abinci ya sauka matuƙa, amma zuwa yanzu lamarin sai addu'a, farashin sai hawa yake k**ar wutar shuci.

Ba komai ya haddasa haka ba illa rashin kishi irin na mu na talakawa da muke karyar da kayan amfanin mu da mu ka noma wata da watanni ga ƴan jari hujja, waɗanda su ke bin mu har gona su na sayewa araha domin niƙawa a kamfanunuwan su na shinkafa.

Na biyu rashin imani na ƴan jari hujja, masu mai da talaka bayi domin buƙatun su na wofi.

Allah Ya gyara Ƙasar nan.

06/11/2024

Na tausayawa Madakin Rushi. Yanzu fa shikenan ya kwanta dama a siyasance. Guzumomin Butulayen da su kai ashara sun isa misali!

04/11/2024

Buy new Airtel SIM card, get it registered instantly Biz Link.

Pay ₦800 Only.

03/11/2024

Belin Emefiele da ya sace Biliyoyin Naira, Miliyan 20.. Belin Manyan ɓarayi dubu 50 zuwa 100. Belin masu yi wa dokar zaɓe karan 500,000. Amma Belin ƙananan yaran mu Ƴan'arewa Musulmi, marasa laifi Miliyan 10.

Arewa mu farka!

Waɗannan sune ƙananan ƴara 148 da Gwamnatin tarayya ta k**a a zanga-zangar neman sauƙin rayuwa da aka yi a Nijeriya, (74...
02/11/2024

Waɗannan sune ƙananan ƴara 148 da Gwamnatin tarayya ta k**a a zanga-zangar neman sauƙin rayuwa da aka yi a Nijeriya, (74 daga Kano, 44 daga Kaduna).

Sannan wai sai an biya kuɗin beli Naira Miliyan Goma (₦10,000,000) da kuma samun Mai matakin albashi na 15 da ke aiki a Abuja ya tsaya musu, sannan za'a bayar da belin su.

Idan kun lura dukkanin su a rame suke cikin yunwa da rashin lafiya da tozartawa.

Akwai babar ɗaya daga cikin su, da sai da ta ci bshi sannan ta je wurin Shari'ar, kuma a masallaci ta kwana, baban yaro kuma ba shi da lafiya, sannan yaron na ta shekarar sa 14, kuma sayen magani ya fito a ka k**a shi.

Muna kira ga Lauyoyin mu na Arewa, da Ƴan kasuwa da Gwamnoni, da masu faɗa aji, da kowa da kowa da mu fito mu nemar yaran nan ƴancin su.

Wannan fa cin kashin ana yi mana kawai domin mu Ƴan Arewa ne kuma Musulmi,.

✓An jefa mana rashin zaman lafiya
✓An jefa mana talauci
✓An hana mu wutar lantarki
✓An kashe mana ilmi
✓An ƙi gyara Dam na Jihar Barno har ambaliyar ruwa ta riske su
✓Da suaran su.

Amma duk abin da ya sami Shamuwa watan bakwai ne ya jawo mata, duk sharrin manyan arewa ne

Allah kai mana maganin waɗannan musibu.

01/11/2024

Kafin Ka Wala, dole sai Ka Wahala.
Da Dattin Zuci, gwanda Dattin Jiki 👌

01/11/2024

Yau Juma'a. 📿
Allah Ka sada mu da albarkar ranar Juma'a.

Jumu'at Mubarakah
❤️

30/10/2024

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ₦71,000 a matsayin ma fi ƙarancin albashi!

09/10/2024

Allah Ya ji ƙan Hon. Inusa Harina Imawa. Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Dawaki/Warawa.
Allah Ya sa mu cika da imani.
🙏

08/10/2024

Kuna raina Barrister. Idan ku kai wasa shine Sipikan Gobe. Kuma sai ya ƙara ragargaje Tungar Garera!🤗

17/09/2024

Game da zaɓen Ƙananan Hukumomi na Jihar Kano. Ya k**ata Ƴan Tungar Garera su gane cewa, babu yadda za'a yi Mai Mageduwa ya mulki masu yatsu. Sai dai ya mulki kutare! 😀

15/09/2024

Alhamdulillah!
Masara kwano ɗaya ₦1,600.
Muna sa rai ta dawo ƙasa da ₦1,000.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when PAMA_Political Awareness Movement & Advocacy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share