Kapmen Kano North

Kapmen Kano North Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kapmen Kano North, Political organisation, Kano.

  GOBE TA ALLAH CE!!!Ya Allah, ga bawanka, Mai Girma His Excellency Sanata Barau I. Jibrin, wanda babu abin da ke cikin ...
23/01/2026


GOBE TA ALLAH CE!!!

Ya Allah, ga bawanka, Mai Girma His Excellency Sanata Barau I. Jibrin, wanda babu abin da ke cikin zuciyarsa face kudirin alkhairi da ci gaban al’ummar Jihar Kano.

Ya Allah, Ka ƙara inganta shirye-shirye da manufofinsa, Ka cika masa dukkan burikansa na alkhairi, don alfarmar Manzon Allah (SAW).

Ya Allah Maɗaukakin Sarki, Ka tabbatar masa da mafi girman alkhairi a duniya da Lahira. Ka albarkaci rayuwarsa da dukkan al’amuransa, Ka sauƙaƙa masa lamurransa, Ka kuma biya masa dukkan bukatunsa na alkhairi.

Ameen, Ameen Ya Rabbal Alameen. 🤲🏽

Kano Za Ta Dawo Kan Turbar Ci Gaba Tare da Sanata Barau I. JibrinJihar Kano na da cikakken damar dawo wa kan hayyacinta ...
19/01/2026

Kano Za Ta Dawo Kan Turbar Ci Gaba Tare da Sanata Barau I. Jibrin

Jihar Kano na da cikakken damar dawo wa kan hayyacinta da matsayinta na jagora idan al’ummar jihar s**a haɗa kai s**a zaɓi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai ta Ƙasa, Sanata Dakta Barau I. Jibrin, a matsayin Gwamna.

Sanata Barau sanannen jagora ne da ya shahara wajen kyautata rayuwar al’umma, gina siyasa mai inganci da kuma jajircewa wajen ci gaban Kano. Tare da kwarewarsa a fagen shugabanci da zurfin gogewarsa a harkokin gwamnati, yana da dukkanin cancantar da za su tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, bunƙasar tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi, musamman ga matasa.

Haɗin kai da cikakken goyon baya daga al’ummar Kano zai samar da jagoranci nagari da zai kawo sauyi mai ɗorewa, ya farfaɗo da harkokin ilimi, lafiya, noma da kasuwanci, tare da ƙara wa jihar Kano daraja da kima a idon ƙasa da ma duniya baki ɗaya.

Yanzu ne lokacin da ya dace mu tashi tsaye mu haɗa hannu domin ganin Kano ta dawo matsayinta na jagora a Arewa da kuma cibiyar ci gaba a Najeriya.

Tare da Sanata Barau, Kano za ta dawo kan hayyacinta.

Kano ta mu ce, ta kuce — haɗin kanmu ne ginshiƙin gagarumar nasara.

Daga:
Auwal Wadata Sansan
Kano Progressive Media Network
(KAPMEN), Kano North

  DSP Senator Barau I. Jibrin Maliya, CFR, has approved the installation of 1,400 solar-powered streetlights in each Loc...
18/01/2026


DSP Senator Barau I. Jibrin Maliya, CFR, has approved the installation of 1,400 solar-powered streetlights in each Local Government Area within Kano North Senatorial District, bringing the total number of solar streetlights to 18,200 across the zone
By Auwal Wadata Sansan
KAPMEN, Kano North

Kungiyar Kano Progressive Media Network (KAPMEN) ta jaddada aniyarta ta ci gaba da tallata kyawawan manufofi da nasarori...
17/01/2026

Kungiyar Kano Progressive Media Network (KAPMEN) ta jaddada aniyarta ta ci gaba da tallata kyawawan manufofi da nasarorin da DSP Senator Barau I. Jibrin (Maliya) ya shimfiɗa, tare da haskaka ayyukan alherin da ya aiwatar a Kano ta Arewa, cikin ladabi, gaskiya da mutunta kowa.

Kungiyar ta bayyana cewa a siyasa, magana mai tsafta, hujja da gaskiya ita ce tubalin nasara, tare da nuna cikakken yakini cewa ayyukan da Sanata Barau ya aiwatar su ne ginshiƙan da ke haskaka tafiyarsa da karfafa amincewar al’umma a gare shi.

Sanata Barau ya yi fice wajen gudanar da ayyuka na zahiri da s**a shafi tallafa wa al’umma, samar da muhimman ayyukan more rayuwa, da kuma inganta jin dadin jama’a a dukkan yankunan da yake wakilta. Wadannan ayyuka su ne hujjoji karara da ke nuna jajircewarsa, hangen nesansa da kuma kishinsa ga cigaban Jihar Kano.

Kungiyar KAPMEN ta bayyana cikakkiyar gamsuwa da salon jagorancin Sanata Barau, tare da nuna kyakkyawan fata da yakini cewa, da ikon Allah, tafiyar siyasar shekarar 2027 za ta kasance ta nasara. Haka kuma, kungiyar ta jaddada cewa siyasa mai nutsuwa, gaskiya da tsabta na bai wa al’umma damar fahimtar nagarta da kuma zabar abin da ya fi dacewa da muradunsu.

A shekarar 2027, da yardar Allah, za a fuskanci zaɓe cikin kwanciyar hankali, haɗin kai da amincewa, bisa tabbacin cewa nagarta ba ta ɓoyuwa. Kungiyar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen wayar da kan al’umma kan ayyukan da Sanata Barau I. Jibrin ya aiwatar, domin bambance wanda ya yi aiki a zahiri da wanda ya tsaya kan alkawari kawai.

Allah Ya tabbatar da nasara, Ya kuma sa wannan buri ya cika cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Auwal Wadata Sansan
KAPMEN
Kano North

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kapmen Kano North posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share