27/02/2026
Gwamna Abba ka fi ƙarfin mota
Maigirma gwamna Abba K. Yusuf, duk wanda Allah Ya ba wa shugabanci sai ya haɗa da hakuri da jama’a. Babba juji ne, inji masu iya magana. Shi kuwa William Shakespeare cewa ya yi “Uneasy lies the head that wears a crown". Bima’ana, duk wata matsala ta tattara akan wanda ya hau kujerar shugabanci.
Duk wanda Allah ya zaɓa cikin miliyoyin mutane ya ba wa ragamar shugabanci, to kuwa sai ya haɗa da haƙuri da miliyoyin jama’a. Dole sai ya gani, ya nuna bai gani ba, kuma ya ji, ya nuna bai ji ba.
Akwai ɗaya cikin tsoffin kwamishinanka da ya nemi shawarata kimanin sati biyu da s**a gabata, kan batun motocin da aka siya musu. Shawarar da na ba shi ita ce: in dai za ka iya ajiye kujerar kwamishina, mece ce kuma mota da ba za ka iya ajiyewa ba? Haka dai muka rabu, bai gamsu da shawarar da na ba shi ba na ya mayar da motar salin-alin.
Duk da cewa a fahimtata ka fi kwamishinonin nan gaskiya akan wannan lamari, amma tunda kai babba ne, bai kamata mota ta janyo cece-ku-ce tsakaninka da tsofaffin kwamishinoni ba, musanman dan albarkacin ɗan gidan Kwankwaso.
Duk wata ni’ima da alfarma ta ofis, gwamna ka samu a ƙarƙashin Kwankwaso – tun daga gida da mata da mota da kujerar hajji da uwa-uba kujerar gwamna, duk Allah Ya ba ka ta silar wannan bawan Allah. Akwai abin da ɗauke kai ya fi kawo maslaha akan cewa lallai sai an bi ƙa’ida.
Wannan hoton mushen motar ka ce Toyota Corolla (First Lady), wacce Kwankwaso ya siya maka tare da manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati a 1999, kuma ya sahale muku ku tafi da ita bayan an faɗi zaɓe.
Hausawa na cewa in dai loma ɗaya ta ishi maƙwalamci, to a tsoma a mai ba shi.