07/08/2022
SHUGABAN KUNGIYAR ATIKU ALKHAIRIYYA YA GANA DA SABBIN EXCOS NA MUTUM 25 NA SHIYYOYI 3 (KANO TA AREWA,KANO TA KUDU DA KUMA KANO TA TSAKIYA) DAKE JIHAR KANO.
A cikin Shirye-shiryen kungiyar na ganin Alh Atiku Abubakar ya samu nasara, Shugaban kungiyar Atiku Alkhairiyya Alh. Bin Abdulrahman ya karbi bakuncin sababbin excos din kungiyar na mutum 25 daga yankunan Kudu, 25 daga yankunan Arewa da 25 daga yankunan tsakiyar jihar Kano a ofishin sa a jiya.
A yayin taron masu jawabai daga kowane shiyyoyi ukun sun jaddada goyon bayansu ga burin Alh. Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya.
Inda s**a shaida masa cewa gwamnatin APC a yanzu ta gaza matuka, wanda hakan ya sa ya zama dole Najeriya ta nemi shugaba mai hangen nesa, tunani da kuma tsare-tsare don kawo wa al’umma ababen more rayuwa da kuma bunkasa kasuwanci.
A nasa martanin, Alh Bin Abdurrahman yace Alh Atiku Abubakar tuni ya fito da tsare-tsare na ceto Najeriya daga kuncin rayuwa da rashin tsaro da ke kawo cikas ga martabar Najeriya.
Yayi Alkawarin yin aiki dasu domin tabbatar da nasarar Atiku Abubakar a kakar zabe ta 2023.
Ya kuma bukaci daukacin Excos da su mika sakon zuwa kananan hukumominsu, domin tunatar da al’umma bukatar su zabi Alh Atiku Abubakar domin cancantar shi a zaben 2023 mai zuwa.
Vote PDP
Vote Alh. Atiku Abubakar
Vote Progress
ATIKU ALKHAIRIYYA 2023 HEAD OFFICE KANO, KANO STATE.
7th August, 2022.