Mahamuda Sani M/Gini dan siyasa ne da ya reke shugaban karamar hukumar Dala da ke daya daga cikin kananan hukumumomin dake kano ta tsakiya, a shekarar 2003 zuwa 2007. Mutanen karamar hukumar Dala sun ta neman ya sake fitowa takarar wannan kujera tasa don ya cigaba da yin manyan aiyukan more rayuwa da gina dan Adam da ya ke yi a wannan karamar hukumar. Mahamuda Sani ya amsawa mutanen karamar hukuma
rsa, ya fito takara. Burin mutanen karamar hukumar kuma ya cika cikin yarda Ubangiji inda ya dawo a matsayin zababen shugaban karamar hukumar a karo na biyu, a shekarar 2007 zuwa 2011. Mahamuda Sani (Buharin Dala) dan siyasa ne wanda a lokacin mulkin sa ko 'yan adawar jam'iyarsa ta ANPP na karamar hukumarsa suna ya bonsa sabi da irin yanda yake tafiyar da mulkinsa. A karshen zagayen mulkinsa na Biyu, Mahumada Sani ya yiwa wata togaciya wacce ba taiwa dayawa mutanen karamar hukumarsa dadi ba ba 'yan jam'iyarsa kurum ba. Duk da haka mutanen karamar hukumarsa basu daina kiraye-kiraye a gareshi ba na ya fito takarar Governor 2015. Buharin Dala, ya kuma amsa masu zai fito takarar Governor a wannan kakar zaben da muke fuskanta ta 2015 da izini Ubangiji