26/11/2022
SOYAYYA GAMON JINI 2
HIKAYAR ALISHARU DA YARINYA ZUMURRAZI
Da shigarsa kasuwa sai ya hangi mutane sun yi dafifi, sun zagaye wani abu a tsakiyarsu suna kallo. Sai ya ce a cikin ransa, "Shin me waÉ—annan mutane ke kallo ne, bari in matsa in É—ebe kwarkwatar ido.
Ya kutsa cikin mutane har ya kai ga abin da ake kallo. Sai ya ga ashe wata kyakkyawar kuyanga ce ake talla. Tsawon wannan kuyanga zai kai kafa biyar, jikinta madaidaici, ita ba siririya ba kuma ba mai ƙiba ba. Tana da jajayen kumatu k**ar furen wardi. Ƙirjinta faffaɗa a cike, ya turo sama k**ar zai fasa rigar da ta sanya. Tana da shafaffen ciki da faffaɗan kuturi. Wannan kuyanga ta zarce dukkanin matan zamaninta da kyawo, da haiba da kwarjini. Sunanta Zumurrazi.
Yayin da Alisharu ya ga wannan kuyanga sai ya yi mamaki da irin kyawun da Allah ya h**e mata, ya ce, "Na rantse da Allah, ba zan bar wannan wuri ba sai na ji tamanin wannan kuyanga, kuma sai na ga wanda Allah zai ba sa'ar sayenta." Don haka sai ya yi tsaye a cikin attajirai, su kuma da s**a ga haka sai s**a yi zaton cewa shi ma ya zo ne domin sayen wannan kuyanga, saboda sun san mahaifinsa ya bar masa gadon dukiya mai yawa, ba su san cewa fanko ne ba. Ganin kitse suke yi wa rogo.
Daga nan sai dillalin kuyanga ya tsaya kusa gare ta, ya dubi attajirai ya ce, "Ya ku attajirai, ya ku manyan mutane. Wanene daga cikinku zai fara taya wannan kuyanga mai daraja, sarauniyar watanni, murjanin zamani, kwararrar masaƙiya, farin cikin wanda ya same ta, baƙin cikin wanda ya rasa ta, kuyanga Zumurrazi? Duk wanda zai fara taya ta ya sani, babu komawa baya bisa ga kuɗin da ya ambata."
Daga nan sai wani tajiri ya yi gaba ya ce, "Na saye ta dinari É—ari biyar."
Sai wani ya zaburo ya ce, "Zan biya dinari É—ari biyar da goma."
Yana rufe bakinsa sai wani tsoho mai shuÉ—in idanu da matsattsar fuska, k**ar an matse lemu, mai suna Rashiduddini ya ce, "Ni zan biya dinari É—ari shida."
Sai wani ya cafe, "Zan biya dinari É—ari shida da goma."
Rashiduddini ya ce, "Na saya d