31/08/2026
SAƘON TA’AZIYYA
إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
Allah Ya yi wa Mal. Muktar Usman Mai Du rasuwa, babban jami’in Hukumar Hisbah, wanda ya shafe sama da shekaru 25 yana hidima a cikin wannan tsari, har Allah Ya kai shi matsayin ACG, Mataimakin Babban Kwamanda.
Rasuwarsa babban rashi ne ga Hukumar Hisbah, iyalansa, abokan aikinsa da al’ummar da ya shafe tsawon shekaru yana yi wa hidima.
A madadin dukkan ‘yan Hisbah, muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyalan marigayin, ‘yan uwansa, abokan aikinsa da dukkan waɗanda wannan babban rashi ya shafa.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya yafe masa, Ya haskaka kabarinsa, Ya yalwata masa rahama, Ya sanya ayyukansa na alheri su zama sanadin samun rahamarSa, Ya kuma shigar da shi Aljannar Firdausi.
Ya Allah, Ka ba iyalansa da ‘yan uwansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Idan tamu ta zo, Ya Allah Ka sa mu cika da imani, Ka kyautata ƙarshen rayuwarmu, Ka karɓi rayukanmu cikin yardarka.
آمِين يَا رَبَّ الْعَالَمِينَ.
Allah Ya jiƙan Mal. Muktar Usman, Ya sa Aljanna ce makomarsa.
Copy
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa