04/09/2026
KANO, WANNAN DAMAR CE TA SAMUN CANJI NA GASKIYA! 🗣️
Idan da gaske muna son canji na gari, to dole ne mu zaɓi mutanen kirki da nagari. Ba za mu ci gaba da tsammanin sakamako daban ba alhali muna maimaita zaɓin da ya jefa mu cikin matsalolin da muke fuskanta.
Kano na buƙatar shugaba mai amincin zuciya, nagarta, ƙwarewa, tausayi da kishin al’umma, wanda yake da niyyar yi wa jama’a hidima da gaskiya. Wannan shi ne Malam Ibrahim Khalil.
Duk da ƙoƙarin da wasu s**a yi na hana shi kasancewa a cikin waɗanda za su fafata, saboda tsoron samun shugaba mai gaskiya da riƙon amana, jama’a ce ke da magana ta ƙarshe.
Ya ku mutanen kirki na Kano, kada ku bari wannan dama ta kuɓuce muku! Idan muna son Kano mai tsaro, ingantaccen ilimi, ci gaban tattalin arziki, ayyukan yi da kyakkyawar rayuwa, to lokaci ya yi da za mu yi amfani da ƙuri’armu wajen zaɓen shugabanci nagari.
Kano ta cancanci shugaba nagari. Kano ta cancanci shugabanci mai kishin jama’a. Kada mu rasa wannan dama.
Malam Ibrahim Khalil — dama ce ta canji. ✊🏽🇳🇬