07/09/2026
A safiyar yau, tawagar REMASAB ta gudanar da aikin feshin maganin sauro a Gama E, Ƙaramar Hukumar Nasarawa, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Hukumar na kare lafiyar al’umma da inganta muhalli.
Wannan aiki na daga cikin shirye-shiryen da muke aiwatarwa bisa ƙwarin gwiwar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, His Excellency Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ke ci gaba da bai wa REMASAB cikakken goyon baya wajen sauke nauyin da aka ɗora mata.
A ƙarƙashin jagorancina, REMASAB za ta ci gaba da shiga lungu da saƙo na birnin Kano, tare da ƙara himma wajen ayyukan kula da muhalli, da rage yaduwar sauro da sauran ƙwari masu iya haifar da barazana ga lafiyar al’umma.
Dr. Muhammad S. Khaleel
Managing Director,
REMASAB