Refuse Management and Sanitation Board, Kano State. Remasab

  • Home
  • Nigeria
  • Kano
  • Refuse Management and Sanitation Board, Kano State. Remasab

Refuse Management and Sanitation Board, Kano State. Remasab OFFICIAL ACCOUNT OF REMASAB
Committed to keeping Kano State clean, healthy, and sustainable through effective waste management �

PRESS RELEASE 08/06/2026.REMASAB TA KADDAMAR DA ASIBITIN ABBA KABIR YUSUF (A.K.Y) DOMIN KULA DA LAFIYAR MA’AIKATANTA.Huk...
08/06/2026

PRESS RELEASE
08/06/2026.

REMASAB TA KADDAMAR DA ASIBITIN ABBA KABIR YUSUF (A.K.Y) DOMIN KULA DA LAFIYAR MA’AIKATANTA.

Hukumar Tsaftar Muhalli da Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), ƙarƙashin jagorancin Manajan Darakta, Dakta Muhammad S. Khalil, ta kaddamar da Asibitin AKY domin kula da lafiyar ma’aikatan hukumar. Wannan muhimmin shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin hukumar na inganta jin daɗi da walwalar ma’aikatanta tare da samar musu da kulawar lafiya mai inganci.

Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya yaba wa Manajan Daraktan REMASAB bisa jajircewarsa wajen kula da walwalar ma’aikata da kuma gudanar da harkokin hukumar cikin kwarewa.

Ya ce, “Ya zama wajibi in yaba wa abokin aikina bisa yadda yake nuna ƙwarewa da jajircewa wajen tafiyar da wannan hukuma, tare da ba da fifiko ga jin daɗin ma’aikatanta.”
Haka kuma, ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su ci gaba da bai wa shugabancinsu cikakken goyon baya domin tabbatar da dorewar tsafta da kyakkyawan muhalli a faɗin Jihar Kano.

Shi ma da yake nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta Jihar Kano, Dakta Aliyu Isah Aliyu, ya jaddada aniyar ma’aikatarsa na ci gaba da haɗin gwiwa da REMASAB wajen tabbatar da tsafta a kasuwannin dabbobi, mayanka da sauran wuraren da s**a shafi harkokin dabbobi.

A nasa jawabin, Manajan Daraktan REMASAB, Dakta Muhammad S. Khalil, ya bayyana yadda asibitin zai gudanar da ayyukansa. Ya bayyana cewa an yi wa dukkan ma’aikatan hukumar rijista a Hukumar Kula da Lafiya ta Taimakon Juna ta Jihar Kano (KSCHMA) ƙarƙashin shirin Abba Care, domin sauƙaƙa musu samun ingantaccen kulawar lafiya.

Dr Khali ya Kara da cewa “An yi wa dukkan ma’aikatan wannan hukuma mai daraja rijista a KSCHMA. Asibiti zai riƙa gudanar da duba lafiyar ma’aikata da kula da ƙananan matsalolin lafiya. Duk wata cuta ko matsalar da ta zarce ƙarfin asibitin, za a tura mara lafiya zuwa manyan asibitocin gwamnati kamar Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da sauran makamantansu.”

A wani ci gaba kuma, hukumar ta samar da wutar lantarki ta hasken rana mai aiki na sa’o’i 24 a hukumar Remasab.

Wannan na daga cikin manufofin Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na inganta ababen more rayuwa da kuma kyautata ayyukan gwamnati.

Taron ƙaddamarwar ya samu halartar manyan daraktoci, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a bangare lafiya na jiha da abokan hulda na ketare (partners).

Sanya Hannu:

Abubakar Ahmad
Jami’in Hulɗa da Jama’a (P.R.O.)
REMASAB, Kano.

05/06/2026

Bayanin MD REMASAB Dr. Muhammad S Khalil yayin Bikini Ranar Mahalli ta Duniya

Press Release 4 ga Yuni, 2026.MA’AIKATAR ALBARKATUN RUWA, MUHALLI DA SAUYIN YANAYI TARE DA REMASAB SUN GUDANAR DA BIKIN ...
04/06/2026

Press Release
4 ga Yuni, 2026.

MA’AIKATAR ALBARKATUN RUWA, MUHALLI DA SAUYIN YANAYI TARE DA REMASAB SUN GUDANAR DA BIKIN RANAR MUHALLI TA DUNIYA A KANO.

Hukumar Tsaftar Muhalli da Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, sun gudanar da bikin Ranar Muhalli ta Duniya a yau Alhamis, 4 ga Yuni, 2026, a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, cikin Birnin Kano.

Bikin, wanda Mai Girma Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim ya jagoranta, tare da Manajan Daraktan REMASAB, Dakta Muhammad S. Khalil, ya kasance wata muhimmiyar dama ta wayar da kan jama'a game da muhimmancin kare muhalli da tabbatar da tsafta domin inganta rayuwar al’umma.

A yayin bikin, an gudanar da ayyukan tsince shara, dashen bishiyoyi da kuma sanya Akwatin zubar da shara (Litter Bins) a muhimman wurare domin ƙarfafa tsafta da kare muhalli.

Haka kuma, an jaddada aniyar gwamnati na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a da sauran matakan da za su tabbatar da dorewar muhalli mai tsafta da lafiya.

Da yake jawabi a wajen taron, Manajan Daraktan REMASAB, Dakta Muhammad S. Khalil, ya bayyana irin gagarumar nasarorin da hukumar ta samu a ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf. Ya ce daga cikin nasarorin akwai biyan basuss**an da aka gada na ma’aikatan tsaftar muhalli, dawo da albashinsu zuwa kaso ɗari bisa ɗari (100%), tare da yi musu rijistar inshorar lafiya domin su samu damar samun kulawar lafiya da magunguna cikin sauƙi.

Dakta Khalil ya kuma bayyana ƙudirin hukumar na ci gaba da sauya REMASAB zuwa hukuma ta zamani ta hanyar ƙirƙiro sabbin manufofi da shirye-shiryen da za su amfanar da ma’aikata da al’umma baki ɗaya.

Ya ce daga cikin waɗannan tsare-tsare akwai shirin samar da cibiyar lafiya a cikin REMASAB domin bai wa ma’aikata damar samun kulawar likita da magunguna cikin gaggawa idan buƙata ta taso.

A nasa jawabin, Mai Girma Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya yabawa ƙoƙarin REMASAB wajen inganta tsaftar muhalli a jihar, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwar gwamnati da al’umma wajen kare muhalli daga gurɓacewa.

A ƙarshe, Dakta Muhammad S. Khalil ya miƙa godiyarsa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa kulawa, goyon baya da jajircewar da yake nunawa wajen inganta harkokin tsaftar muhalli da walwalar ma’aikatan REMASAB.

Hukumar REMASAB ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaftataccen muhalli, kare lafiyar jama'a da kuma gina Kano mai tsafta.

Sa hannu.

Abubakar Ahmad
Jami’in Hulɗa da Jama’a (P.R.O.)
REMASAB

PRESS RELEASE4 June 2026. MINISTRY OF WATER RESOURCES, ENVIRONMENT AND CLIMATE CHANGE AND REMASAB COMMEMORATE WORLD ENVI...
04/06/2026

PRESS RELEASE
4 June 2026.

MINISTRY OF WATER RESOURCES, ENVIRONMENT AND CLIMATE CHANGE AND REMASAB COMMEMORATE WORLD ENVIRONMENT DAY IN KANO.

The Refuse Management and Sanitation Board (REMASAB), in collaboration with the Kano State Ministry of Water Resources, Environment and Climate Change, today commemorated the 2026 World Environment Day at the Palace of His Royal Highness, the Emir of Kano, Kofar Kudu, Kano.

The event was officially flagged off by the Honourable Commissioner for Water Resources, Environment and Climate Change, Dr. Dahiru M. Hashim, and attended by the Managing Director of REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, alongside senior government officials, environmental stakeholders, traditional leaders, development partners and members of the public.

The celebration featured a range of environmental sustainability initiatives, including community sanitation exercises, tree-planting activities and the installation of litter bins along strategic locations within the metropolis. These efforts reflect the Kano State Government's commitment to environmental stewardship, effective waste management and the promotion of a cleaner, healthier and more sustainable environment for all citizens.

In his remarks, the Managing Director of REMASAB, Dr. Muhammad S. Khalil, highlighted the significant milestones achieved by the Board under the visionary leadership of the Executive Governor of Kano State, His Excellency Alhaji Abba Kabir Yusuf. He noted that the administration has successfully cleared inherited liabilities relating to sanitation workers, restored their salaries to full payment status and enrolled them in a comprehensive health insurance scheme, thereby ensuring access to quality healthcare services and medical support.

Dr. Khalil further reaffirmed his commitment to repositioning REMASAB as a modern, efficient and service-oriented environmental management institution through the implementation of innovative policies and sustainable reforms.

He disclosed plans to establish a healthcare facility within the Board to provide prompt medical attention and enhance the welfare of its workforce.

He also expressed profound appreciation to His Excellency, Governor Alhaji Abba Kabir Yusuf, for his unwavering support, strategic leadership and continued investment in environmental sanitation and the wellbeing of sanitation workers across Kano State.

The World Environment Day commemoration underscores Kano State's enduring commitment to environmental sustainability, climate resilience and community participation in building a cleaner, safer and more prosperous future for present and future generations.

Signed:

Abubakar Ahmad
Public Relations Officer (P.R.O.)
Refuse Management and Sanitation Board (REMASAB)
Kano State

03/06/2026

Da yake yiwa Premier radio karin bayani, Shugaban hukumar ta Remasab Muhammad S Khalil ya ce, tattakin na daga cikin shirye-shiryen bikin ranar Muhallin ta duniya wanda ake gudanarwa a ranar 5 ga watan Yunin kowace shekara.

Muhammad S Khalil ya ce tattakin za'a faro shi ne daga Kofar kudu dake fadar mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da misalin karfe 9 na safiya a gobe Alhamis.



Press Release 2/6/2026.REMASAB TA KARYATA ZARGIN RASHIN BIYAN ALBASHIN MA’AIKATA.Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli da Kwas...
02/06/2026

Press Release
2/6/2026.

REMASAB TA KARYATA ZARGIN RASHIN BIYAN ALBASHIN MA’AIKATA.

Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli da Kwashe Shara ta Jihar Kano. (REMASAB) ta lura da wani rahoto da Gidan Radiyon Dala fm ya wallafa a Shafin na Facebook (flyer), inda ake ikirarin cewa ba a biya ma’aikatan. REMASAB albashin su ba, tare da cewa ma’aikatan suna karɓar albashin Naira Dubu Goma (₦10,000) kacal a kowane wata.

REMASAB ta bayyana karara cewa waɗannan ikirari ƙarya ne, kuma ba su da alaƙa da ainihin halin da ake ciki a hukumar Remasab. A sanin hukumar Remasab babu wani maaikacin ta da ake bawa albashin dubu goma 10,000.00 idan Kuma akwai to ya gabatar da shedar biyan albashi ga hukumar ko Kuma duk kafar yada labaran da ta bayyana hakane.

Hukumar ta nuna damuwarta kan yadda aka yaɗa irin waɗannan zarge-zarge ba tare da neman ƙarin bayani ko tabbatar da sahihancin su daga REMASAB ba, lamarin da ya saɓa wa ƙa’idojin aikin jarida na Gaskiya, Adalci da ƙwarewa.

Saboda haka, REMASAB na kira ga waɗanda s**a wallafa wannan rahoto da su gabatar da hujjojin da s**a dogara da su wajen yaɗa waɗannan zarge-zarge. Haka kuma, hukumar na buƙatar gidan rediyon Dala FM da ya janye rahoton tare da gyara bayanan na Gaskiya.

REMASAB ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da biyan albashin maaikatanta duk Wata, ba tare da bata lokaci ba, kazalika ta biya duk bashin da ta gada a baya, zuwa yanzu babu wani maaikacin ta da yake bin bashi.

Hukumar ta ja hankalin kafafan yada labarai da su zama masu yada labarin Gaskiya a Koda yaushe.

An Sa Hannu:

Abubakar Ahmad
Jami’in Hulɗa da Jama’a (P.R.O.)

31/05/2026
31/05/2026

PRESS RELEASE
31 ga Mayu, 2026.

MD, REMASAB, Dr. Muhammad S Khalil ya kai zyarar gani da Ido Unguwar Gwammaja domin duba matsalar hanyoyin magudanan Ruwa.

A madadin Mai Girma Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dr. Dahir M. Hashim, Manajan Daraktan Hukumar Kula da Tsaftar Muhalli da Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Dr. Muhammad S. Khalil, ya kai ziyarar gani da ido zuwa unguwar Gwammaja domin tantance matsalar toshewar hanyoyin magudanan ruwa da mazauna yankin ke fuskanta.

Ziyarar ta biyo bayan koke-koke da korafe-korafen al’ummar yankin dangane da matsalolin da ke haddasa ambaliyar ruwa, musamman a lokacin damina, lamarin da ke janyo shigar ruwa cikin gidaje tare da haddasa asarar dukiyoyi da kuma barazana ga lafiyar jama'a.

A yayin ziyarar, Dr. Muhammad S. Khalil ya gana da wakilan al’ummar unguwar, inda s**a bayyana masa irin kalubalen da suke fuskanta da kuma bukatar daukar matakan gaggawa domin magance matsalar.

Bayan tattaunawar, an zagaya wuraren da matsalar ta shafa domin duba halin da ake ciki tare da tantance hanyoyin da za a bi wajen magance ta.

Dr. Khalil ya bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma, musamman ta hanyar daukar matakan kariya daga ambaliyar ruwa da sauran matsalolin muhalli.

Ya kara da cewa tuni aka fara daukar matakan gaggawa bisa umarnin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano domin magance matsalar da kuma samar da mafita mai dorewa ga mazauna yankin.

Ya kuma tabbatar wa da al’ummar Gwammaja cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da sanya idanu da kuma aiwatar da ayyukan da s**a dace domin tabbatar da ingantaccen muhalli da walwalar jama'a.

Sa hannu

Abubakar Ahmad
P.R.O Remasab

Address

No. 15 Club Road
Kano
700213

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Refuse Management and Sanitation Board, Kano State. Remasab posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share