23/04/2026
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) reshen Jihar Katsina ta kammala babban taronta na Congress a ranar Alhamis, 23-04-2026, inda aka tattauna tare da tsara cikakken tsarin shugabancin jam’iyyar a matakin jihar.
A yayin wannan muhimmin taro, an gudanar da sahihin zaben shugabanci wanda ya haifar da nadin AMBASSADOR MUHAMMAD RIMI a matsayin Sabon Shugaban Jam’iyyar ADC na Jihar Katsina.
An zabi AMB. Rimi ne bisa la’akari da kwarewarsa, jajircewarsa da kuma gudunmawar da yake badawa wajen cigaban jam’iyyar a jihar.
Jam’iyyar ADC ta bayyana kwarin gwiwa cewa sabon shugabancin zai kara kawo hadin kai, tsari da kuma ci gaban jam’iyyar a dukkanin matakan Jihar Katsina.
An kammala taron cikin kwanciyar hankali da lumana.
Daga:
Jamilu Surajo (Met Jk-Malumfashi) Katsina ADC Media Department