20/04/2022
ARC. AHMED MUSA DANGIWA: JAKADAN AMANA DA KARE HAKKIN AL'UMMA
A tsawon shekaru 25 na Kafuwar Bankin FMBN, Bankin ya samun Nasarar biyan kudin Pension Refund (Maidawa maaikata da s**a Yi retire) yawan Kudin Naira Biliyan 10.8bn.
Kudin Pension Refund, kudade ne d a Maaikata suke tattarawa tsawon Lokacin aikinsu a Nigeria har zuwa retire, Wanda a cikin Lokacin aikin su, suke da damar amfani da kudin don karbar Lamunin gida, fili ko kudin Gina Gida daga Bankin Bada Lamunin Gidaje na Gwamnatin Tarayya (FMBN). Dokar aikin Gwamnati ta Bada badamar a rika cire wani Dan kaso daga cikin albashin Ma'aikacin Nigeria duk wata don tanadawa a Wani asusun Bada Lamunin Gidaje na Gwamnatin Tarayya. Hakan yasa kusan ko wane maaikaci yake da wani kudi ajiye a Bankin. Ya sani ko Bai sani ba.
Saboda rashin sanin Bankin da ayyukanshi a tsawon Lokaci, yasa dubban maaikata Basu ma San suna da Wannan kudi a ajiye ba. Don haka wannan kudi suna zama wasu abin zuqar wasu daga Marasa gaskia a Bankin tsawon Lokaci. Shi yasa Bankin a Tsawon shekaru 25 na kafuwar shi, Naira Biliyan 10.8 kacal ya biya kudin refund ga mutane 127,632.
Zuwan Arc. Ahmed Musa Dangiwa cikin shekaru 5 ya rosa wannan mummunan tarihin inda ya biya Naira Biliyan 35.8bn ha maaikata 232,637. Hakan na nufin 300% na abinda Bankin ya biya cikin shekaru 25, amma Arc. Dangiwa ya cimma wannan Nasara cikin shekaru 5 kacal..
Wannan na nuni da Amana, rikon gaskia da kyautata hakkin al'umma Wanda shine kashin bayan cin Nasarar ko wane Irin shugabanci.
Wannan Nasara na nufin daga Shekarar 2023 in Allah ya kaimu Arc. Dangiwa ya samu Nasarar zama Gwamnan Jihar Katsina, za a samu shugaba da yake da kiyayewa da taka tsantsan kan raayin Jama'a.
Jihar katsina za a samu nasarar magance Matsalar cin hanci, handama da babakere, da watanda da dukiyar Jama'a. Kenan za a samu tarin kudaden da za ayi ma alumma aikin cigaban kasa da raya kasa dasu.
Gudummuwar Dangiwa 2023 Frontiers