Katsina State Water Board

Katsina State Water Board Katsina State Water Board is a Government agency responsible for the Supply of portable drinking water in the urban areas of Katsina State.

The Federal Program Coordinating Unit (FPCU) of the SURWASH and World Bank organized a workshop held at Bolton White Hot...
21/08/2026

The Federal Program Coordinating Unit (FPCU) of the SURWASH and World Bank organized a workshop held at Bolton White Hotel Abuja on 19th - 21st August, 2026. The workshop was attended by 14 states and the FCT.

The aim of the Workshop was organized to Validate the Revised SURWASH Program Operations Manual (POM) and also to ensure that all stakeholders have a common understanding of the restructured SURWASH Program, it's implementation arrangements, roles and responsibilies, verification requirements, and expectations going forward.

The Katsina State delegation under the leadership of Hon. Mannir Ayuba Sullubawa the Hon. Commissioner Ministry of Water Resources, also in attendance is the Permanent Secretary Ministry of Water Resources, PC SURWASH Program, the Executive Director of RUWASSA, STOWASSA & SEPA as well as other participants from the SURWASH implementatiing Agencies.

Katsina State is still the leading state among the 14 states based on the performance assessment carried out, this milestone achievement is due to the commitment of His Excellency the Governor of Katsina State Malam Dikko Umaru Radda PhD. in increasing access to WASH services to the people of Katsina State.

Copy From Malam Abdul Maje Yadda Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar ba-zata domin duba ayyuka...
21/08/2026

Copy From
Malam Abdul Maje

Yadda Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar ba-zata domin duba ayyukan da ake gudanarwa a sabbin hukumomin samar da ruwan sha (Water Board), RUWASSA da SURWASH da ke kan titin Dutsinma.

Ziyarar ta kasance wani bangare na ƙoƙarin Gwamnan na bibiyar yadda ayyukan ke gudana, tare da tantance ci gaban da aka samu wajen samar da ingantaccen ruwan sha ga al’ummar jihar.

An Maida Sunan Makarantar .Unguwar Dawo Primary School Dake Malumfashi da suna Marigayi. Injiniya Tukur Hassan Tinglin P...
19/08/2026

An Maida Sunan Makarantar .Unguwar Dawo Primary School Dake Malumfashi da suna Marigayi. Injiniya Tukur Hassan Tinglin PhD Domin Tunawa dashi

Da Irin gaggarumar gudummuwa da yaba Ilimina alokacin rayuwarahi a wannan yankin musanman Malumfashi/ Kafur Allah jikan Zannan da Rahama Yasa Aljanna ce Makomarshi Ameen.

Sarkin Daura Ya Yaba da Kokarin Gyara Matsalar Ruwan Sha a Karamar Hukumar DauraMai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Fa...
18/08/2026

Sarkin Daura Ya Yaba da Kokarin Gyara Matsalar Ruwan Sha a Karamar Hukumar Daura

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar CON, ya yabawa kokarin Gwamnatin Jihar Katsina na magance matsalar samar da ruwan sha a Karamar Hukumar Daura.

Mai Martaba Sarkin ya nemi Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Jihar Katsina da ta dauki matakan gaggawa domin ganin an dawo da ruwan sha ga al’ummar Daura.
Biyo bayan wannan kira,

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Mal Dikko Umar Radda PhD CON.ta bayar da umarni ga Ma’aikatar Albarkatun Ruw ta Jihar Katsina. , karkashin jagorancin Kwamishina Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, da a gyara matsalar tare da dawo da ingantaccen ruwan sha ga al’ummar yankin.

A halin yanzu, an kammala kusan kashi 75 cikin 100 na aikin gyaran, yayin da aka samu kayan aikin da ake bukata daga kasar China.

Ana sa ran wasu bangarorin Karamar Hukumar Daura za su fara samun ruwan sha a yau, ciki har da Tawalala, Rahamawa, Bayan Motel, Kururrubai, yankin gidan yari da sauran wurare, kamar yadda al’umma s**a saba samu.

An bayyana cewa da zarar an kammala sauran ayyukan gyaran da ake gudanarwa, za a ci gaba da samar da ruwan sha ga sauran sassan Karamar Hukumar Daura yadda ya kamata, Insha Allah.

Al’ummar Daura sun bayyana godiyarsu ga Gwamnan Jihar Katsina da Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, bisa kokarin da suke yi wajen ganin an magance matsalar ruwan sha.

Sun kuma yi addu’ar Allah Ya kara wa Kwamishinan jagoranci da nasara, Ya kuma ba da damar kammala aikin cikin lafiya da nasara, albarkar Manzon Allah (S.A.W).

Hukumar Ruwa Ta Ci Gaba da Kai Ruwan Agaji ga Mazauna wasu unguwani Dake Fama da Matsalar Ruwa a garin KatsinaAyau asaba...
15/08/2026

Hukumar Ruwa Ta Ci Gaba da Kai Ruwan Agaji ga Mazauna wasu unguwani Dake Fama da Matsalar Ruwa a garin Katsina

Ayau asabar 15 ga Agusta, 2026: Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina, ƙarƙashin kulawar Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, ta ci gaba da kai ruwan agaji ga wasu unguwannin da ke fama da matsalar ƙarancin ruwa a cikin birnin Katsina.

A ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026, hukumar ta kai ruwan sha ga mazauna Unguwar Kofar Keke da Kofar Sauri, domin rage wa al'ummar unguwannin wahalar samun ruwa sakamakon ayyukan faɗaɗa tituna da ke gudana a wasu sassan birnin.

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da cewa mazauna yankunan da ayyukan gine-gine s**a shafa ba su rasa ruwan sha na yau da kullum ba.

Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina tana da alhakin samar da ruwan sha ga birane da manyan garuruwan jihar, kuma tana aiki domin tabbatar da samuwar isasshen ruwan sha mai inganci ga al'umma.

Mazauna unguwannin sun nuna godiya ga hukumar bisa wannan tallafi, musamman ganin yadda matsalar ta shafi samun ruwa a wasu lokuta.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan gaggawa domin rage wa al'ummar da abin ya shafa radadin ƙarancin ruwa yayin da ake ci gaba da ayyukan faɗaɗa tituna a cikin birnin Katsina.

Wanda gwamnatin Mal Dikko Umar Radda PhD CON Yakeyi domin Kara zamuntar da garin Katsina Yadda zaiyi gigayya da sauran biranen jihohin Nigeria

15/08/2026

Kwamishina Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina Hon Mannir Ayuba Sullubawan yayin wani taro inda dandazon Alumma ke bite dashi

An Dage Aikin Sabunta Manyan Bawulolin Ruwan Ajiwa Zuwa Birnin KatsinaHukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina, ƙarƙa...
12/08/2026

An Dage Aikin Sabunta Manyan Bawulolin Ruwan Ajiwa Zuwa Birnin Katsina

Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina, ƙarƙashin kulawar Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, na sanar da al’ummar mazauna garin Katsina cewa an dage aikin sabunta manyan bawulolin ruwan da s**a taso daga Matatar Ruwan Ajiwa zuwa cikin birnin Katsina da kewaye, wanda aka shirya fara gudanarwa ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026.

Hukumar ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne sakamakon wasu sabbin dalilai na aiki da s**a taso, wanda s**a sa aka ga ya dace a ɗan jinkirta fara aikin domin tabbatar da an shirya komai yadda ya kamata kafin a fara gudanar da aikin.

Saboda haka, ranar da za a fara aikin za a sanar da al’umma nan gaba, da zarar an kammala shirye-shiryen da ake buƙata.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, ya bayyana cewa aikin na daga cikin muhimman shirye-shiryen gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, na inganta tsarin samar da tsaftataccen ruwan sha da rage matsalar ƙarancin ruwa a jihar.

Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina ta gode wa al’ummar jihar bisa haƙuri, fahimta da goyon bayan da suke bai wa ƙoƙarin gwamnati na inganta samar da ruwan sha, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da ya shafi aikin.

Sanarwa _Sanarwa_Sanarwa !!Hukumar  Samar da Ruwa Sha  Za Ta Sake Sabbin Manyan Bawulolin Ruwan Ajiwa Zuwa Birnin Katsin...
12/08/2026

Sanarwa _Sanarwa_Sanarwa !!

Hukumar Samar da Ruwa Sha Za Ta Sake Sabbin Manyan Bawulolin Ruwan Ajiwa Zuwa Birnin Katsina.

Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina. kalkashin kulawar kwamishin Albarkatun ruwa na Jihar Katsina.Hon Mannir Ayuba Sullubawan.ta sanar da fara wani muhimmin aikin sake sabunta manyan bawulolin ruwan da s**a taso daga Matatar Ruwan Ajiwa zuwa cikin birnin Katsina da kewaye.

Hukumar ta ce za a fara aikin ne ranar Asabar 15 ga Watan Augusta 2026. idan Allah Ya yarda, domin inganta tsarin samar da ruwan sha tare da tabbatar da samun tsaftataccen ruwa ga al’ummar birnin Katsina.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, ne ya bayyana hakan yayin wani bayani da ya yi wa manema labarai a ofishinsa da ke Sakatariyar Gwamnatin Jihar Katsina.

Ya bayyana cewa aikin wani muhimmin ɓangare ne na shirin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, na ƙarfafa tsarin samar da ingantaccen ruwan sha da kuma rage matsalolin ƙarancin ruwa da al’ummar jihar ke fuskanta.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, manyan bawulolin da ake shirin sauyawa sun shafe sama da shekaru 50 tun lokacin da aka samar da Matatar Ruwan Ajiwa, kuma ba a taɓa yin cikakken aikin sabunta su ba tun wancan lokaci.

Saboda haka, ya ce aikin zai taimaka matuƙa wajen inganta zirga-zirgar ruwa daga matatar zuwa cikin birnin Katsina, tare da ƙara inganci da dorewar tsarin samar da ruwan sha.

Hukumar ta kuma buƙaci al’ummar Katsina da mazauna garuruwan da ke kewaye da birnin da su kasance cikin shiri, domin gudanar da aikin na iya haifar da ɗan tsaiko ko ƙarancin ruwan sha na ɗan lokaci a wasu wurare.

Kwamishinan ya nemi al’umma da su ƙara haƙuri da fahimta a yayin gudanar da aikin, yana mai cewa duk matakan da ake ɗauka na da nufin samun mafita mai ɗorewa ga matsalar ruwan sha.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su bai wa ma’aikatan da za su gudanar da aikin cikakken haɗin kai da goyon baya, domin a samu nasarar kammala aikin cikin sauƙi a Kan lokaci.

“Wannan aiki ba wai kawai gyaran bawuloli ba ne; wani mataki ne na ƙarfafa tsarin samar da ruwan sha da kuma tabbatar da cewa al’ummar Katsina sun samu ingantaccen ruwa mai tsafta.”

Hukumar ta ce tana sane da muhimmancin ruwan sha ga rayuwar yau da kullum, don haka za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gudanar da aikin cikin tsari, tare da rage wahalar da jama’a za su iya fuskanta.S

Albishirinku Mutanen Daura da Kewaye: An Ƙara Samun Ci Gaba Wajen Inganta Ruwan Fanfo a Daura.Bisa amincewar Maigirma Gw...
12/08/2026

Albishirinku Mutanen Daura da Kewaye: An Ƙara Samun Ci Gaba Wajen Inganta Ruwan Fanfo a Daura.

Bisa amincewar Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, na ganin inganta samar da tsaftataccen ruwan sha a faɗin Jihar Katsina, musamman a Ƙaramar Hukumar Daura da kewaye, ana ci gaba da ɗaukar matakai domin inganta ruwan sha a yankin.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, ya lashi takobin ganin an daidaita tare da inganta samar da ruwan sha a Ƙaramar Hukumar Daura.

A yau, na kai ziyara wajen Manajan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina (Water Board) domin samun ƙarin bayani kan shirin gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda na inganta samar da ruwan sha a wannan gari.

A yayin ziyarar, na samu bayanin cewa Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina ya riga ya samar tare da sanya bawuloli (valves) guda 11 a cibiyoyin samar da ruwan sha na Daura da kewaye, kamar haka:

Gidan Ruwan Dunu: An sanya bawul guda 3 mai inci 8, da kuma bawul guda 2 mai inci 2.
New Yard (Zonal Office): An sanya bawul guda 1 mai inci 6.
Gidan Ruwan Mother: An sanya bawul guda 1 mai inci 6.
Gidan Ruwa na Old Yard (Tashar Yamma): An sanya bawul guda 2 mai inci 4.

Gidan Ruwa na Total: An sanya bawul guda 2 mai inci 8, da kuma bawul guda 1 mai inci 6.
Muhimmancin Bawulolin
Waɗannan bawuloli suna da matuƙar muhimmanci wajen sarrafa kwararar ruwa da rufe hanyoyin ruwa a lokacin da ake tara ruwa a cikin tankuna domin rarrabawa ga al’umma.

Haka kuma, samar da bawulolin zai taimaka wajen rage asarar ruwan da ake samu a yayin ake da rarraba ruwa daga tankuna.

Bugu da ƙari, za su taimaka wajen tabbatar da samun isasshen ruwa a madatsun da ake amfani da su wajen tattara da rarraba ruwan sha a Daura.
A ƙarshe, muna miƙa godiya ga Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen inganta samar da tsaftataccen ruwan sha a faɗin Jihar Katsina.

Haka kuma, muna yaba wa Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, bisa ƙoƙarinsa na ganin al’ummar Daura da kewaye sun samu ingantaccen ruwan sha.

Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Katsina Ta Ci Gaba da Kai Ruwan Tallafi ga Al’ummomin da Ke Fama da Karancin RuwaAyau  Tal...
11/08/2026

Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Katsina Ta Ci Gaba da Kai Ruwan Tallafi ga Al’ummomin da Ke Fama da Karancin Ruwa

Ayau Talata 11 ga Agusta, 2026 – Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina ta ci gaba da kai ruwan tallafi ga al’ummomin da ke fama da karancin ruwan sha a wasu sassan birnin Katsina. Sakamakon Aikin fadada manyan tituna da gwmatin Mal Dikko Umar Radda PhD CON ta Keyi a cikin garin Katsina.

Shirin rarraba ruwan na gudana ne ƙarƙashin kulawar Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, da nufin rage wa al’ummomin da matsalar ta shafa na radadin karancin ruwan sha.

A yau Talata, tankar dakon ruwa ta Hukumar ta kai ruwan tallafi zuwa Unguwar Sharara Pipe, da ke cikin birnin Katsina, domin taimaka wa mazauna yankin samun ruwan sha.

Hukumar ta ce tana ci gaba da kai ruwan tallafi zuwa yankunan da matsalar karancin ruwa ta fi shafa, musamman a wannan lokaci da ake gudanar da wasu manyan ayyukan raya birnin Katsina.

Da yake magana kan wannan shiri, Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Hon. Mannir Ayuba Sullubawa, ya yaba wa al’ummomin da ke fama da karancin ruwa bisa haƙuri da haɗin kan da suke bai wa Hukumar wajen gudanar da ayyukanta.

Kwamishinan ya bayyana cewa matsalar karancin ruwa da ake samu a wasu sassan birnin Katsina na da alaƙa da ayyukan faɗaɗa da inganta manyan tituna da ake gudanarwa a birnin,
waɗanda ke buƙatar sauya ko gyara wasu layukan samar da ruwan sha.

Ya tabbatar da cewa Hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da samar da ruwan tallafi ga al’ummomin da matsalar ta shafa, har sai an samu daidaito a tsarin samar da ruwan sha.

Wasu mazauna yankunan da s**a amfana da ruwan tallafin sun bayyana jin daɗinsu tare da gode wa Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Katsina da Kwamishinan Albarkatun Ruwa bisa wannan tallafi.

Sun ce kai musu ruwan ya rage musu wahalar da suke fuskanta sakamakon karancin ruwan sha.
Hukumar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da ba ta haɗin kai, tare da yin amfani da ruwan da ake samar musu cikin tsafta da kulawa, domin kare lafiyar al’umma.

Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan gaggawa domin rage tasirin karancin ruwa ga mazauna birnin Katsina, tare da ƙoƙarin tabbatar da samun ingantaccen ruwan sha ga al’umma.

Address

No. 8 Olusegun Obasanjo Drive G. R. A Katsina
Katsina

Opening Hours

Monday 08:00 - 16:00
Tuesday 08:00 - 16:00
Wednesday 08:00 - 16:00
Thursday 08:00 - 16:00
Friday 08:00 - 12:30

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina State Water Board posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Katsina State Water Board:

Shortcuts

Share